Shehu Shagari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Shehu Shagari
Shagaricropped.jpg
2. shugaban ƙasar Najeriya

1 Oktoba 1979 - 31 Disamba 1983
Olusegun Obasanjo - Muhammadu Buhari
Ministan Albarkatun kasa

1971 - 1975
Obafemi Awolowo - Asumoh Ete Ekukinam (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Shagari (Nijeriya), 25 ga Faburairu, 1925
ƙasa Najeriya
Mutuwa Abuja, 28 Disamba 2018
Yan'uwa
Yara
Yan'uwa
Karatu
Makaranta Kwalejin Barewa
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Mabiya Sunnah
Jam'iyar siyasa National Party of Nigeria (en) Fassara

Shehu Shagari ɗan siyasan Nijeriya ne. (An haife shi a ranar 25 ga watan Fabrairu shekara ta alif 1925) a garin Shagari, Arewacin Najeriya (a yau jihar Sokoto)[1], Ya rasu ne a ranar 28 ga watan Disamban shekara ta 2018 bayan jinya da gajeruwar rashin lafiya da yayi a wani asibiti a Abuja, ya rasu yana da shekara 93 Dahaihuwa. Shehu Shagari ya zama shugaban kasar Nijeriya a watan Oktoban shekarar ta alif 1979, yayi mulki har zuwa Disamban shekara ta alif 1983, wanda sojoji suka kwace mulki a hunnunsa, a jagorancin Muhammadu Buhari. Shagari shine shugaban Nijeriya da ya hau mulki ta sanadiyar zabe na farko. Olusegun Obasanjo ne ya bayar da mulkin zuwa ga farar hula, a dalilin haka da matsi da mulkin sojoji ke fuskanta, ga rashin yin katabus, ganin hakan ne dai yasa Obasanjon ya bayar da mulkin amma ba'a kai ko’ina ba sai sojojin suka sake dawowa suka kwace mulki daga hannun farar hula, inda suka zargi mulkinsa da cin hanci da rashawa, hakane ne dai ya kai ga Muhammadu Buhari ga zama shugaban Ƙasa a wanchan lokacin.[2][3]

Tsohon shugaban kasa Shehu Shagari
Taron shugabannin kasashen a shekara 1981

Tarihi[gyara sashe | Gyara masomin]

Tarihi ya nuna cewa shehu shagari ya samo asali ne daga Muhammadu wanda ɗan uwan kakan-kakan shehu shagari ne, Makiyayi ne kuma yana yawo da iyalansa baki ɗaya. Kuma an nuna cewa sun zauna a sifawa a shekarar ta 1810, kuma ya zama daga cikin dakarun Shehu Usman Ɗan Fodiyo[1]. Hakazalika tarihi ya nuna cewa shagari wani wuri ne wanda ya samo asali lokacin shehu Ɗan Fodio sun tsaya tare da mutanen Muhammadu a wani wuri domin hutawa, sai Ɗan Fodiyo yace, "Ku Sha Gari” (fura da Nono). Daga nan aka sanya ma wurin Shagari, shi kuma shugaban Muhammadu Shagari. Muhammadu shagari ya rasu kuma an binne shi a Shifawa, inda aka binne Shehu Ɗan Fodiyo. Muhammadu Shagari ya rasu ya bar ƴaƴa biyu Usman Da Iggi wanda Iggi ne babba kuma an naɗa iggi a matsayin magajin shagari watau shugaban garin Shagari (Nijeriya). Bayan naɗin sarautan Magajin Shagari, igge tare da kawunsa Shehu Ɗan Fodiyo suka ƙaro dakarun tsaro kuma aka zagaye garin shagari da ganuwa[4]. Daga nan garin shagari ya fara bunƙasa a harkokin kasuwanci har ya mamaye ƙauyukan Sokoto ta kudu[1].Ƴan kasuwa da matafiya kan yada zango a garin shagari a duk lokacin da dare ya musu. Saboda mutanen garin suna da kara da kyawawan halaye. Garin shagari ya zama amintaccen gari mai zaman lafiya duk da yaƙe-yaƙe da akai tayi a ƙarni na 19th  a ƙarƙashin magajin Shagari. Sarautar sokoto ƙarƙashin shari’ar musulunci[1].

Bayan Turawa sun kama sokoto, sababbin ƙauyuka sun samu an sanya garin shagari ƙarƙashin mulkin Yabo[1]. Muhammadu Basharu ɗan magaji Rufa’i ya sake zama magajin shagari duk da sun rasa mulki da zuwan Turawa. A lokacin da aka haɗa kudanci da Arewacin Najeriya, a shekarar ta 1914 aka naɗa Aliyu baban Shehu shagari wanda ya gaji Galadima Bayan rasuwarsa da karban mulki daga hannun Muhammadu Basharu[1]. Bayan ƙirƙirar Jihohi, da ƙanan hukumomi a 1996, shagari ta zama sabon cibiyar ƙaramar hukumar- da yawan mutane 83,540 a ƙauyuka 10 dake ƙarƙashinta. Garin Shagari ta rasa mutane dalilin sabbin hanyoyin kasuwanci na zamani[1]. Duk da garin Shagari ba wata muhimmiyar alƙarya bace, amma tarihi ya nuna cewa garin ya wanzu cikin zaman lafiya da riƙon amana kusan mutanen garin na kula da harkokin gabansu ba tare da katsalandan ba[5].

Tarihi ya nuna cewa na haifi Shehu Shagari ne a ranar laraba 8 ga watan Sha’aban (watan musulunci) a Shekarar 1925[6].(p14)Mahaifyar Shehu Shagari na kiransa da inkiya Balarabe, saboda an haifeshi a Sha’aban[7].  Asalin sunan Shehu Shagari “Usman” wanda ya samo asali daga Uthman Ibn Affan sannan kuma sunan kakansa ne ƙanin Muhammadu shagari (wanda ya ƙirƙiro garin shagari) hakazalika sunan Shehu Usman Ɗan Fodiyo[8]. Hausawa kan kira Usman Shehu. Shehu shagari ɗa na uku ne a wajen mahifiyarsa[9].

Rayuwa da Ilimi[gyara sashe | Gyara masomin]

Shehu shagari ya fara ganin mota a rayuwarsa lokacin yana dan shekara biyar a shekarar 1930, lokacin da sultan muhammadu Tambari (1925-1931) yazo garin shagari ya kwana a gidan shehu shagari. (p16Tarihi ya nuna tun kafin a tura shehu shagari makarantar boko ya riga ya koya ilimin addinin musulunci a wurin iyayensa da kuma manyan malamai[10]. (p17

Shehu shagari yayi zurfin karatu a ilimin addini kuma a duk lokacin da ya sami hutu yakan tsaya ya koyar da ilimi a ƙauyensa[11]. (p20) saboda fahimatarsa, ilimi wani abu ne da ya jiɓinci rayuwa gaba ɗaya, tun daga farko har ƙarshe. Shehu ya shafe tsawon shekara 34 yana koyarwa Shehu ya bar garin shagari a karo na farko a shekarar 1931, ya tafi neman ilimin zamani watau boko a garin yabo. Mahaifinsa ya rasu lokacin yana da shekara biyar[12].

Siyasa[gyara sashe | Gyara masomin]

 A shekarar ta 1962 sultan sir saddiq Abubakar III ya naɗa shehu Turakin sokoto a matsayin minista wanda sir Ahmadu Bello ya naɗa a kawu a watan Aprilu a garin kaduna[13].

A zaɓen watan oktoba,shekarar ta 1960, wacce zata kawo ƴanci a ƙasar nan, jam’iyyan NPC (wanda sir Ahmadu Bello da Abubakar Tafawa Balewa  a matsayin mataimakinsa) yaci. An naɗa shehu shagari da Alhaji Muhammadu Ribaɗu, Alhaji Inuwa Wada, Zanna Bukar Dipchorime, Waziri Ibrahim, Usman Sarki, Musa yar,adu a matsayin ministocin ƙasa bayan samun ƴanci[14].

An naɗa shehu shagari a matsayin ministan ayyuka da ɗuba a watan May 1965[15]. Aikin shehu na farko a matsayinsa na minista shine canza sakatarorin gwamnati na turawa da ƴan najeriya[16].

A ranar 23 ga watan oktoba,shekarar ta 1978, shehu shagari ya yanke shawara fitowa takaran shugan ƙasa akan cewa zai janye idan har bai cinye yawan kuri’u ba[17]. A zaɓen da akayi a ranar asabar 9 ga watan December-1978, shehu shagari ya cinye ƙuri’u 975, Maitama Sule 504, Adam Girome 293, Dr. Saraki 214, Traka 104, Prof Abubakar 92. (primary election held at casino cenema)[18].

Jam’iyyar NPN na shehu shagari ta lashe kujeru 36 (37.89%) na sanatoci da 168 (37.41%) na kujerun ƴan majalissu.A ranar Alhamis da ƙarfe 12:40pm aka sanar shehu shagari yaci zaɓen shugaban ƙasa da ƙuri’u 5, 688857[19]. An rantsar da shugaba na farko da aka  zaɓa a Najeriya a ranar litinin a Tafawa Ɓalewa Square dake Legas.

Ayyukan Cigaba[gyara sashe | Gyara masomin]

Daga cikin kamfanonin da shehu shagari ya samar sun haɗa:

 • Ministry of steel of develpment
 • Aledja steel plant a 1982
 • Steel rolling mills katsina
 • Steel rolling mills oshogbo
 • Steel rolling mills jos.
 • Anambra motor company 1980
 • National truck manufacturing company kano 1981
 • Stey motors bauchi
 • Leyland Ibadan
 • Private assembley company Illorin, Onitsha, Gusau, Benin & Porthercourt[20].

Bibliyo[gyara sashe | Gyara masomin]

 • Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). ISBN 978-129-932-0. OCLC 50042754.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

 1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 1.6 Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 13. ISBN 978-129-932-0.
 2. https://www.theguardian.com/world/2019/jan/09/shehu-shagari-obituary
 3. https://www.pmnewsnigeria.com/2018/12/28/life-and-time-of-alhaji-shehu-shagari/
 4. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 5. ISBN 978-129-932-0.
 5. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 13. ISBN 978-129-932-0.
 6. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 14. ISBN 978-129-932-0.
 7. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p.14. ISBN 978-129-932-0.
 8. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). pp. 14-15 ISBN 978-129-932-0.
 9. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 8. ISBN 978-129-932-0.
 10. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 17. ISBN 978-129-932-0.
 11. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 20. ISBN 978-129-932-0.
 12. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 31 ISBN 978-129-932-0.
 13. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria).pp. 57-58. ISBN 978-129-932-0.
 14. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). pp. 70-80. ISBN 978-129-932-0.
 15. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 103. ISBN 978-129-932-0.
 16. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p.90. ISBN 978-129-932-0.
 17. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p.200. ISBN 978-129-932-0.
 18. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). pp. 213-214. ISBN 978-129-932-0.
 19. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 227. ISBN 978-129-932-0.
 20. Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria).p. 310. ISBN 978-129-932-0.