Harshen Hausa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Hausa
Kasashen da ake anfani da yaren Hausa: Nijeriya, Nijar, Kamaru, Cadi, Benin, Burkina Faso, Ghana, Togo, Sudan, Côte d'Ivoire.
Adadin Hausawan asali: 70.000.000
Yawan mutanen da suke magana da Hausa: 150.000.000[1]
Matsayin Hausa: 11[2]
ƙungiyar yare
Afro-Aziatisch
Officiële status
Wurin da yake na farko: Nigeria (arewacin ) da Nijar
lambar yare
ISO 639-1: ha
ISO 639-2(B): hau
Hausa language niger.png
Afro asiatic peoples nigeria.png


Tarihin Yaren Hausa هَوُسَا[gyara sashe | Gyara masomin]

Ƙabilar Hausa dai, ƙabila ce dake zaune a arewa maso yammacin tarayyar Nijeriya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. Kabilace mai ɗimbin al'umma, amma kuma a al'adance mai mutuƙar haɗaka, akalla akwai sama da mutane miliyan tamanin da harshen yake asali gare su. A tarihance ƙabilar Hausawa na tattare a salasalar birane. Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300's, sa'adda suka sami nasarori da dauloli kamar su daular Mali, Songhai, Borno da kuma [fulani]. A wasu lokutan Hausawa sun sami gagarumin ikon, mulki da haɗaka ta kau da baki 'yan neman ruwa da tsaki, da kuma neman angizo a cikinta da kuma harkallar bayi. A farko-farkon shekaru na 1900's, a sa'adda kabilar Hausa ke yunkurin kawar da mulkin angizo na fulani, sai turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka mamaye arewancin Nijeriya, da kuma kafa manufofin mulkin bayan gida,a bisa ƙarƙashin mulkin birtaniya,'yan mulkin mallaka sai suka marawa [[fulani

baya na ci gaba da manufofin angizon siyasarsu, har yanzu dai mulkin gamin gambiza tsakanin Hausawa da [[fulani]] shi ne ya yi kane-kane a arewacin Nijeriya. Wannan haɗakar gamin gambiza, an faro ta ne tun asali a matsayin [[fulaniFulani]] su dare madafun ikon a tsararren tsarin siyasar arewa. Akasarin masu mulki na [[fulaniFulani]] sun kasance yanzu, a al'adance Hausawa gwamitse.

Ko da yake, Hausawa na farko-farko maharba ne, amma zuwan addinin Islama da kuma karɓansa da hannu bibbiyu ya sanya labari ya sha bambam. Ginshikokin al'adun Hausawa na da mutukar jarumta, kwarewa da sanaiya fiye da sauran al'ummar dake kewayenta. Sha'anin noma ita ce babbar sana'ar Hausawa inda Hausawa ke ma sana'ar noma kirari da cewa, na doke tsohon ciniki kowa yazo duniya kai ya tarar, akwai kuma wasu sana'o'in kamar su sha'anin jima watau harkar fatu, rini, saka da kira, fannonin dake mutukar samun cigaba a harkokin sana'o'in hausawa. Hausawa dai sun jima da shahara wajen harkar fatauci kana kuma masu arziki na taka rawa a sha'anin yau da kullum, tare da masu mulki da masana. Harshen Hausa shi ne mafi girma da kuma mafi sanannen harshe a nahiyar Afirka. Harshen Hausa ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman larabci kana kuma harshen na tafiya tare da yanayin mu na zamani bisa al'adar cudeni-na cudeka. Harshen Hausa dai ya zama harshen yau da kullum ga miliyoyin jama'a da ba Hausawa ba ne a nahiyar Afirka. Bugu da ƙari, akwai cincirindon al'ummar Hausawa a manyan biranen yammacin Afirka da arewacinta da kuma yankunan cinikayyar al'ummar Hausawa da kuma yankunan da Hausawa suka jima suna bi a hanyar ta zuwa aikin hajji. Akwai kuma rubutattun adabi masu zurfi da kasidodi da kuma rubuce-rubuce a rubutun ajami da aka buga tun kafin zuwan turawa 'yan mulkin mallaka na birtaniyya. Har ila yau, kuma wani tsarin rubutu a ajami da aka ƙirƙiro tun kafin zuwan turawa, da ba kasafai ake amfani da shi ba yanzu.

Ire Iren Yaren Hausa[gyara sashe | Gyara masomin]

Yaren Hausa yana da ire-ire da yawa. Gabarcin Hausa su ne:-

 • gabarcin Hausa
  • 1 -Kanawa
  • 2 - Katagumawa
  • 3 - Hadejawa
 • yammacin Hausa :-
  • 1- Sakkwatawa
  • 2- Katsinawa
  • 3- Kurfayawa
  • 4- Gobirawa
  • 5- Adarawa
  • 6- kabawa
  • 7- Zanfarawa
 • Arewacin Hausa :-
  • 1- Arewa
  • 2- Arawa

Hausa ajami wanda suka fita daga ƙasashin Hausa suka shiga kasashin larabawa shekaru aru-aru :- 1- Sudan 2- Saudiyya 3- Libya 4- Aljeriya

Muhimmancin Yaren Hausa[gyara sashe | Gyara masomin]

Yaren hausa yare ne mai muhimmanci sosai a kimanin kasashe ashirin wurin aikin kasuwanci musamman ma a manyan biranen ƙasashen Afrika ta Yamma (Najeriya, Benin, Burkina Faso, Ghana, Nijer, [[To

_________________________________________________________

Saifullah Bashir Harun :

HAUSA A FAGEN YADA LABARAI

GIDAGEN REDIYOYIN DA SUKE YADA SHIRYE-SHIRYE DA HARSHEN HAUSA DAGA KASASHEN WAJE :

NAHIYAR TURAI :

1- BBC Hausa. (Ingila)

2- RFI Hausa. (Faransa)

3- DW Hausa. (Jamus)

4- TRT Hausa. (Turkiyya). (www.trt.net.tr/hausa)

LATIN AMERIKA :

5- VOA Hausa. (Amerika)

NAHIYAR YURASIYA :

6- Sashen Hausa Radio Moscow. (Rasha)

NAHIYAR ASIYA :

7- CRI Hausa. (China)

8- IRIB Hausa, ko kuma : Hausa Radio Tehran. (Iran)

NAHIYAR AFRIKA :

9- Muryar Afirka Birnin Alkahira. (Misira)

10- Sashen Hausa Radiyon kasar (Libiya).

Idan ka san wasu gidajen rediyon, ka taimaka mana da sunayen su, da sunayen kasashen da suke.

 1. https://www.herald.ng/full-list-hausa-is-worlds-11th-most-spoken-language/
 2. https://www.herald.ng/full-list-hausa-is-worlds-11th-most-spoken-language/