Farauta
![]() | |
Iri | aiki |
---|---|
Bangare na |
primitive tribal community (en) ![]() |
Kwanan watan kalanda | 1,800,000 years BCE – |
Aircraft type (en) ![]() |
hunting weapon (en) ![]() trapping (en) ![]() |
Farauta Sana'a ce ta tuntuni wadda aka gada tun iyaye da kakanni, musamman a ƙasar Hausa. Kuma kusan ace farauta ita ce sana'a ta farko a ƙasar Hausa kafin zuwan wasu sana'o'in kamar su kiwo, noma, Su, da dai sauran sana'o'i. Kuma wasu suna ganin cewa ita farauta kai tsaye tana nufin (Nema) haka zakaji wasu suna cewa idan zasu fita gida don zuwa kasuwa ko wani wurin neman abinci, sai kaji sunce "mun fita (farauta) wato nema" haka kuma mata a cikin gida idan mazajen su zasu fita sai kaji suna cewa a farauto da yawa. A takaice dai farauta na nufin Nema. Amma a zahiri farauta na nufin fita daga gida zuwa daji don neman namun daji da kuma tsuntsaye da sauransu, Mafi yawanci maza ne aka fi sani da sana'ar farauta. suna shiga daji don farauto dabbobin daji, ko da yake ana samun kaɗan daga cikin mata masu kamar maza suna fita farauta. Akan fita farauta wuni ɗaya, kwana ɗaya har zuwa watanni.[1][2]ana Amfani da karnuka da bindigu, kwari da baka, abin kai bugu domin gudanar da farautar.
Kayan da ake farauta dasu[gyara sashe | gyara masomin]
Da dai sauransu akan farauto irin su Zomo, barewa, gada da sauran su. Mafi yawancin mafarauta sunada magunguna sosai (tambaya) saboda ƙwanƙwaman namun jeji. Mafarauci shine tilon mai sana'ar farauta mafarauta kuma jam'in masu yin farauta.[3]
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ "Mafarauta na fuskantar kalubale a kudancin Najeriya". BBC Hausa.Com. 25 May 2016. Retrieved 20 September 2021.
- ↑ Khalid, Aisha (10 August 2021). "Mafarauta: 'Manyan dabbobi' irin 'yan bindiga da masu satar mutane zamu saka gaba". legit.hausa.ng. Retrieved 20 September 2021.
- ↑ https://www.rumbunilimi.com.ng/KasarHausaFarauta.html#gsc.tab=0