Noma

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Tomb of Nakht (2).jpg
Chapeltoun Mains Farm, East Ayrshire, Scotland. View from Bankend Farm.jpg

Hausawa Suka ce "Noma na duke tsohon ciniki, kowa yazo duniya kai ya taras"

  • Menene Noma?
yadda ake huda kenan a lokacin noma
Nuoman shinkafa

Noma yana da ma'anoni da dama kasancewar irin amfanin sa a fannoni daban-daban. To amma dai a fassara mafi sauki, zamu ce, Noma wata hanyar sana'a ce domin samun abinci da kudin shiga. Haka zalika, noma wata babbar hanya ce ta samun karuwar tattalin arziki da al'ummai suka raja'a a kan ta. A kasar Hausa ko kuwa, noma shi ne babbar hanya ta samun haɓakar tattalin arziki. Da noma ne hausawa suka fi samun kudin shiga da abinci dama kayayyakin da ake sarrafawa a masana'anta kamar tufafi da sauran su. A wajen hausawa musamman mazauna karkara noma ya zama kamar wajibi (dole) a wajen kowanne bahaushe musamman magidanci. Kusan mu ce ma ko wanne bahaushe ya iya noma ya san yarda ake yin shi. Noma da Kiwo duk tana nufin abu daya ne.

YARDA AKE NOMA[gyara sashe | Gyara masomin]

Kafin bayani game da yarda ake noma zamu dan tattauna ne a game da rabe-raben noma. Noma ya rabu zuwa gida biyu, kuma kowanne da irin yarda ake yin shi.

  • noman rani
  • noman damina

NOMAN RANI[gyara sashe | Gyara masomin]

Norman rani a lokacin da ruwan sama ya kare

Noman rani, noma ne da ake yin shi a lokacin rani ba da damina ba.

  • ga yarda ake noman rani

Shi noman rani ana yin sa ne a wuraren da ruwa yake wadatacce kamar rafi , korama , da madatsun ruwa wato (dam). Da zarar ruwan sama ya dauke wato kaka ta yi, manoman rani za su fara ne da share gonakinsu, daga nan kuma sai su yi kaftu su ja kwamame sai su shuka abin da zasu shuka a cikin kwamamen Suna yin amfani da injinan banruwa wajen bawa shukokin su ruwa har su girma su isa girbi.

Akasarin abubuwan da ake nomawa a noman rani ana shuka su ne sabo da sayarwa domin samun kudin shiga.

Ga irin abubuwan da ake nomawa da rani.

dadai sauran su. To amma kuma ya danganta da yanayi na yadda kasa zata iya daukar abin da aka shuka a kan ta. Misali idan aka shuka wani abun a wani yankin ba lallai ya yi ba kamar yadda zai yi a wani yankin.

NOMAN DAMINA[gyara sashe | Gyara masomin]

Sabanin noman rani, shi noman damina ana yin sa ne a lokacin damina.

  • ga yadda ake yin noman damina.

Da zarar an samu ruwan sama wato (damina ta fadi), manoma zasu bazama gonakinsu domin yin huda da shuka. Akasari an fi shuka kayan abinci a wajen noman damina, to amma akan shuka kayan sayarwa jefi-jefi.

ABUBUWAN DA AKE NOMAWA DA DAMINA[gyara sashe | Gyara masomin]

Na abinci akwai.

da sauran su.

Na sayarwa

da sauran su.