Gyada

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Gyada a tushen ta

Gyada wani abinci ne, asalinsa tsiro ne da ake shuka shi, yana fitar da ya'ya a cikin kasa karkashin jijiyoyinsa kuma ana sarrafa shi dan amfani dashi amatsayin abinci da sauransu ta hanyoyi daban-daban kamar wurin yin mai (mangyada), Madara , kuli kuli da sauransu. Gyada nada sinadari na furotin dake amfani sosai a miki, musamman kara girman jiki da baiwa jiki kariya, shiyasa yake da kyau arika amfani dashi a cikin abinci.Kuma Shi gyada ya kasu Kashi daban daban, akwai, Kampala, Dan dakkar, Mai bargo da sauransu.

Hanyoyin Sarrafa Gyada[gyara sashe | Gyara masomin]

Ana Sarrafa gyada ta hanyoyi daban-daban kuma ana amfani da ita a duk fadin duniya, sai dai anan zamu dubu kadan ne daga irin hanyoyin da ake sarrafa gyada amatsayin abinci.

  • Madaran Gyada, za'a iya yin madara da gyada, idan aka sami danyen gyada sai a bare su, a wanke sannan abari ya jiku a Ruwa, sai a niketa, idan aka nika sai a tace, bayan an tace sai a dafa, idan ya dahu sai a barshi ya huce, shikenan an sama madarar gyada, za a iya bai wa yara wadanda basu samun cikakken abinci domin Karin lafiya.
  • Mangyada, za'a iya hada mai da gyada idan aka samu gyada aka bare ta, aka barta ta bushe, ko kuma aka samu wanda aka riga aka busar, sai a soya ta bada wuta sosai ba ko kuma za'a iya kin soyawa, soyawa ba dole bane, idan an soya, sai a nika ta, to tazama tunkuza bayan an nika, daga nan sai a matse tunkuzar ta hanyar juyawa, za'a ga mai din na kadan kadan daga jikin tunkuzar.
  • ana sarrafa gyada a samar da man kuli kuli
    Kulikuli, idan anason yinsa za'a bi yanayin da aka bi dan yin mangyda ne, amma a dai dai lokacin da aka gama fitar da mai din gyadar daga jikin tunkuzar, to tunkuzar da aka riga aka fidda mai acikinsa, shine za'a hada da sinadirai kamar magi, gishiri, barkono, citta da sauransu sai a rika iba ana soyawa da mai din da aka fitar, idan aka soya yasoyu, to ansama kulikuli.