Gyaɗa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Gyaɗa
oil seed (en) Fassara, nut (en) Fassara da dan-ice
Cacahuate.png
Tarihi
Mai tsarawa Gyaɗa
Gyada a tushen ta
tugaggiyar gyaɗa bayan an ginota kafin a tsigeta daga tushen ta
ƙuli-ƙuli na gyaɗa da kantu
dafaffiyar gyada

Gyaɗa wani abinci ne, asalin ta tsiro ne da ake shuka shi,yana fitar da ya'ya a cikin kasa karkashin jijiyoyinsa kuma ana sarrafa shi dan amfani dashi a matsayin abinci da sauransu ta hanyoyi daban-daban kamar wurin yin mai.[1][2] (mangyada), Madara,kuli kuli da sauransu. Gyada nada sinadari na protein dake amfani sosai a jiki, musamman kara girman jiki da baiwa jiki kariya, shiyasa yake da kyau a rika amfani dashi a cikin abinci. Kuma ita gyada ta kasu Kashi daban daban, akwai, Kampala, yar dakkar, Mai bargo da sauransu.[2].

In da ake nomawa[gyara sashe | Gyara masomin]

yawancin inda suke nomata. Zamfara da Nasarawa da Kaduna da kuma Kwara. Duk dadai yanzu akwai sabon irin gyada da yake yalwa a jihohin yankin gabashin kasar nan, musamman ma jihohin Enugu da Anambra.[3]

Hanyoyin Sarrafa Gyada[gyara sashe | Gyara masomin]

Ana Sarrafa gyada ta hanyoyi daban-daban kuma ana amfani da ita a duk fadin duniya, sai dai anan zamu dubu kadan ne daga irin hanyoyin da ake sarrafa gyada amatsayin abinci.

  • Madaran Gyada, za'a iya yin madara da gyada, idan aka sami danyen gyada sai a bare su, a wanke sannan abari ya jiku a Ruwa, sai a niketa, idan aka nika sai a tace, bayan an tace sai a dafa, idan ya dahu sai a barshi ya huce, shikenan an sama madarar gyada, za a iya bai wa yara wadanda basu samun cikakken abinci domin Karin lafiya.
  • Mangyada, za'a iya hada mai da gyada idan aka samu gyada aka bare ta, aka barta ta bushe, ko kuma aka samu wanda aka riga aka busar, sai a soya ta bada wuta sosai ba ko kuma za'a iya kin soyawa, soyawa ba dole bane, idan an soya, sai a nika ta, to tazama tunkuza bayan an nika, daga nan sai a matse tunkuzar ta hanyar juyawa, za'a ga mai din na kadan kadan daga jikin tunkuzar.
  • ana sarrafa gyada a samar da man kuli kuli
    Kulikuli, idan anason yinsa za'a bi yanayin da aka bi dan yin mangyda ne, amma a dai-dai lokacin da aka gama fitar da mai din gyadar daga jikin tunkuzar, to tunkuzar da aka riga aka fidda mai acikinta, shine za'a hada da sinadirai kamar magi, gishiri, barkono, citta da kuma sikari da sauransu sai a rinka diba ana curawa ana soyawa da mai din da aka fitar, idan aka soya yasoyu, to ansama kulikuli.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. https://www.voahausa.com/a/cin-kwayaoyi-dangin-su-gyada-bashi-da-matsala-ga-mata--ga-mata-masu-ciki/1831526.html
  2. 2.0 2.1 https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-kasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html
  3. https://aminiya.dailytrust.com/sarrafa-albarkatun-gona-gyada-3/