Madara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Nono da kankara a Cikin shi din ya sashi sanyi
Mahaifiya ta na shayar da jariri nono
Fakiti da gwangwanayen madara
Madara akofi
yarinya ta dakko nono a gora
ana tatsan nonon akuya
Hasashshen nono

Madara ko Nono dukkanin kalmomin biyu suna nufin abu daya ne sai dai akan banbanta halittar mama ta dan'Adam akirata da Kalmar Nono kawai ba'a kiranta da madara. Idan akace Nono to ana nufin ruwan dake fita daga nonuwan halitta walau ta Dan'adam ko ta Dabba misali mace tana fitar da nono asanda ta haihu Dan shayar da jaririnta, haka kuma dabbobi kamar saniya, tunkiya, akuya, suma suna fitar da nono dan shayarwa, sa'annan idan kuma akace Madara to anan ana nufin nono ne wadda aka samosa ba daga jikin halitta ba amma dai ansamesa ne daga wasu nau'ukan bishiyoyi, tsirrai, ko kayan abinci, kamar kwa-kwa, waken-suya, gyada, dadai sauransu. Madara ko Nono dai wani farin ruwa ne dake dauke da sinadarai masu amfani a jikin dan'Adam, madara dai yakasance shi kadai ne ake amfani dashi domin samarwa jarirai abinci na dan'Adam ko dabba kafinsu iya fara cin abinci, nono na dauke da wasu kwayoyin halittu dake fita daga jikin uwa zuwa jikin jariri dan su kareshi daga cututtukan da zasu iya samun jaririn, wannan yasa uwa ta shayar da jaririnta abune mafi mahimmanci a rayuwar jariri.