Ruwa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Ruwa ne wannan a matsayin kankara, da kuma wanda ya kwanta, da kuma wadda ke cikin iska

Ruwa wani tataccen sinadari ne wanda yake da matukar muhimmanci a wurin halittun Duniya baki daya kama daga kwari, tsuntsaye, halittun ruwa dana doron kasa. A turance ana kiransa water, Hakika Ruwa ya kasance shine kinshikin rayuwar halittun duniya baki daya, ruwa shine tubalin ginin kwayar duk wata halitta a doron duniya.

Ruwa ya kasance yana tabbatuwa ko saukowa zuwa doron duniya a bisa kudirar Allah mahalicci. Da farko dai asalin samuwar ruwa daga cikin giza-gizai yake taruwa, sannu a hankali har giza-gizai sun cika da tekun ruwa wadda daga nan iska zata rika tura girgijen zuwa inda ruwan zai faru, shi yasa duk lokacinda hadari ya taso zakaji iska tana kadawa da karfi cikin kankanin lokaci sai kaji an goce da ruwa.

Bayan ruwa ya sauka nan take kasa zata tsosa daga nan kuma sai ta kumbura, saboda haka duk wata kwayar tsiro itama sai ta kumbura sakamakon ruwanda ta tsotsa cikin ikon Allah sai kaga an wayi gari tsirai iri-iri sun cika ko'ina a sararin duniya abin gwanin ban sha'awa. Hakika ruwa shine ginshikin duk wata halitta mai rai a doron kasa kowacce halitta tana bukatar ruwa, musamman dan Adam yana amfanuwa da ruwa ta haanyoyi da dama wanda bazai yiwu a iya kididdige amfanin da ruwa keyiwa da Adam ba, tsarki ya tabbata ga Allah mahaliccin ruwa domin amfanin bayinsa.