Ruwan sama

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Wikidata.svgRuwan sama
liquid water (en) Fassara
Rain 2.gif
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na precipitation (en) Fassara, yanayi da energy source (en) Fassara
Yana haddasa ambaliya
Rukunin da yake danganta rukuni:Waƙoƙi game da ruwan sama
ruwan sama na faɗowa akan titi

ruwan sama ruwa ne dake sauka daga sama wanda daga Allah (S W T) shine yake saukar dasu a ko wane lokaci dare ko rana, wani lokaci yayi yawa wani lokaci kuma kadan, amma mayyawa yafi zuwa da hadari,wanda a hausaw suke mashi lakabi da (ruwa kaman da bakin kwarya). Sai kuma yayyafi, shi yayyafi mafi akasari yana zuwa ne a hadarin da bai saukar da ruwa ba, sai kuma misali lokacin malka-malka shi kuma a wannan lokacin zaka ga ruwa ba dare ba rana. a wani lokaci ruwan yayi karfi wani lokacin kuma baya yin karfi to wanda baiyi karfin ba shine ake kira da yayyafi.[1][2]

yara suna wasa a ruwan sama

Hadari[gyara sashe | Gyara masomin]

Shidai hadari shine kusan ace ginshikin ruwan sama wanda mafi yawan ruwan saman da ake yi sai hadari ya hadu ya taso yayi iska sannan sai ruwa yazo wani lokaci a hade da iska wani lokacin kuma zalla ruwa ne. Menene Hadari? Hadari dai shine haduwar gira-gizai waje daya musamman bakaken gira-gizai sai su dunkule waje daya su tado da iska daga nan bayan iska sai ruwa ya biyo baya, sai dai akwai akwai abunda ke kawowa hadari cikas shine bakan gizo wanda zaka gashi wani ja-ja da yalo-yalo kala dai kusan uku, to idan ya kewaye hadari zaka ga sai dai hadarin nan yayi yayyafi, to wannan yayyafin hausawa nace dashi aman bakan gizo

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. https://www.dw.com/ha/ambaliyar-ruwan-sama-ta-kashe-mutane-12-a-najeriya/a-50263746
  2. "Hukumar kula da yanayi tayi hasashe". BBC Hausa. Retrieved 20 March 2021.