Misra
![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
جُمهورِيّةُ مِصرَ العَرَبيّةِ (ar) | |||||
|
|||||
| |||||
Take |
Bilady, Bilady, Bilady (en) ![]() | ||||
| |||||
Suna saboda |
Ptah (en) ![]() ![]() | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Babban birni | Kairo | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 94,798,827 (2017) | ||||
• Yawan mutane | 93.82 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Larabci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Bangare na | Arewacin Afirka, Gabas ta tsakiya da Yammacin Asiya | ||||
Yawan fili | 1,010,407.87 km² | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Bahar Rum da Nil | ||||
Wuri mafi tsayi |
Mount Catherine (en) ![]() | ||||
Wuri mafi ƙasa |
Qattara Depression (en) ![]() | ||||
Sun raba iyaka da |
| ||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi |
Kingdom of Egypt (en) ![]() ![]() | ||||
Ƙirƙira |
28 ga Faburairu, 1922: Kingdom of Egypt (en) ![]() 3150 "BCE" | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Tsarin gwamnati | jamhuriya | ||||
Gangar majalisa |
House of Representatives (en) ![]() | ||||
• President of Egypt (en) ![]() | Abdul Fatah el-Sisi (8 ga Yuni, 2014) | ||||
• Prime Minister of Egypt (en) ![]() |
Moustafa Madbouly (en) ![]() | ||||
Ikonomi | |||||
Kuɗi | Fam na Masar | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Suna ta yanar gizo |
.eg (en) ![]() ![]() | ||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | +20 | ||||
Lambar taimakon gaggawa |
122 (en) ![]() ![]() ![]() | ||||
Lambar ƙasa | EG | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | egypt.travel |
Kasar Misra,ko Masar tana kudu maso gabashin Afrika, kuma tana kudu maso yammacin Asiya [1]ɗaya daga cikin muhimman siffofin da take taƙama da su shi ne na kasancewa ta a kan mararraba ta kusa da nahiyar Turai. Sannan kuma tana matsayin ƙasar da ta kasance mashiga tsakanin Afirka da nahiyar Asiya. Har ila yau kuma, ita ce kuma ta haɗa hanyar safara ta cikin ruwa, tsakanin tekun Mediterrenean da tekun Indiya ta hanyar Bahar Maliya.
Dalar Giza da ke birnin Al-ƙahirar Kasar. Misra ko ƙasar Masar dai ta kasance ƙasa mafi yawan al'umma a cikin dukkanin ƙasashen Larabawa, kuma babban birninta wato birnin Al'ƙahira shi ne birni mafi girma a nahiyar Afirka tun ƙarnoni da dama da suka gabata. Sannan kuma har ila yau, ga ta a ƙarshen kogin nilu, wanda shi ne kogi mafi girma a duniya. Saboda haka, idan aka yi la'akari da waɗannan dalilai na tarihi, to za a iya fahimtar dalilin da ya sa matsayin ƙasar Misra yake da ƴar rikitarwa.
Su ma kansu Misirawan a tsakanin su, sukan kasance cikin ruɗani a game da batun nahiyar da ya kamata su yi tutiya da ita a matsayin nahiyarsu. Ga su dai a cikin kwazazzabon nilu, da mediterenean, da Sahara, har ila yau kuma ga su cikin duniyar Musulmai, dukkan waɗannan siffofi, siffofi ne da kuma ba kasafai ya kamata a ce wata ƙasa guda ɗaya ta haɗa su ba. To, sai dai duk da haka za a iya cewa, mafi yawan faɗin ƙasar yana ɓangaren nahiyar Afirka ne. To, amma fa duk da haka ana kallon garuruwan da suke lardin Sinai na ƙasar Misiran a matsayin ɓangaren nahiyar Asiya, kasancewar su, suna yankin gabashin ƙasar ne.
Kogin Nilu wanda shi ne kogi mafi girma a duniya. A zamanin da can, dangantakar Misra da ƙasashen da ke Afirka na da matukar ƙarfi. To amma tun lokacin da Siriyawa da ke ƙarƙashin daular Rumawa suka mamaye Misira, a ƙarni na bakwai kafin zuwan Annabi Isa Alaihissalam, sai Misira ta fuskanta zuwa ga Yankin Gabas ta Tsakiya, ta fuskar harkokin al'adunta, da na addininta da na siyasarta da kuma na tattalin arzikinta. Kuma mafiya yawan Misirawa suna danganta kansu ne da Larabawa kuma ƴan Yankin Gabas ta Tsakiya. Har ila yau, kuma wasu da yawa daga cikinsu, kusan ace waɗanda suke su ne 'yan asalin ƙasar ta Misira, waɗanda kuma aka fi sani da Nubiyawa, suna danganta kansu ne da Afirka. Hasali ma suna iƙirarin su jinin Afirka ne.
Babu shakka dai idan aka bi salsala ta tarihi, shekaru kimanin 200 da suka gabata, Misra tana da alaƙa mai ƙarfi da ƙasashe irin su Sudan da Habasha da Libya da ma wasu ƙasashe da dama na nahiyar ta Afirka. Kuma ba tare da wani kokwanto ba, Misra za ta cigaba da cin tudu biyu, a matsayinta na ruwa-biyu, wato ga ta dai 'yar Afirka, kuma 'yar yankin Gabas ta Tsakiya, yana daga cikin tarihin Misira kasancewarta
gari na farko a tarihi da sheɗan da kansa ya bayyana ga azzalumin sarki Fir' auna a lokacin da Fir'auna ya ce shi Ubangiji ne.
Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]
Kasar na da matukar tarihin gaske a yankin Afirka da duniya gabaki daya
Al'adu[gyara sashe | gyara masomin]
Abinci[gyara sashe | gyara masomin]
Tufafi[gyara sashe | gyara masomin]
Yarika[gyara sashe | gyara masomin]
Mulki[gyara sashe | gyara masomin]
Kasan misra tana da karfin mulki.
Arziki[gyara sashe | gyara masomin]
Noma[gyara sashe | gyara masomin]
Kasar Misra na da dabino da furanni daban-daban.
Kiwon lafiya[gyara sashe | gyara masomin]
Akwai asibitoci da'ake kula da marasa lafiya
Wasanni[gyara sashe | gyara masomin]
Addini[gyara sashe | gyara masomin]
Musulunci[gyara sashe | gyara masomin]
Kiristanci[gyara sashe | gyara masomin]
Tsaro[gyara sashe | gyara masomin]
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
Ƙasashen Afirka |
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe |