Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango
République Démocratique du Congo
Flag of the Democratic Republic of the Congo.svg Coat of arms of the Democratic Republic of the Congo.svg
Administration
Government jamhuriya
Head of state Félix Tshisekedi (en) Fassara
Capital Kinshasa
Official languages Faransanci
Geography
COD orthographic.svg da LocationDRCongo.svg
Area 2344858 km²
Borders with Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Sudan ta Kudu, Uganda, Ruwanda, Burundi, Tanzaniya, Zambiya, Angola, Jamhuriyar Kwango, Sudan, Kameru da Ruwanda
Demography
Population 86,790,567 imezdaɣ. (2019)
Density 37.01 inhabitants/km²
Other information
Time Zone UTC+01:00 (en) Fassara da UTC+02:00 (en) Fassara
Internet TLD .cd (en) Fassara
Calling code +243
Currency Congolese franc (en) Fassara
Tutar Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango
taswirar Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango

ƙasar Kwango sunanta jamhuriyar Kwango, tun kafin zamanin mulkin mallaka, to amma bayan da Turawan mulkin mallaka suka mamaye ƙasar sai suka sa mata suna Jamhuriyar dimokuraɗiyyar Kwango a ranar 1, ga watan Agustan, 1964, kuma an yi haka ne da nufin banbance ta da maƙociyarta wadda ita ma sunanta jamhuriyar Kwango.

Jamhuriyar domokaradiyar kwango

Mobutu Sese Seko, tsohon shugaban Kwango, a lokacin tana amsa sunan Zayar Yadda aka yi ta samu tsohon sunanta na Zayar kuwa ya faru ne a ranar 27 ga watan Oktoban 1971, a zamanin mulkin tsohon shugaba Mabutu Sese Seko. Kuma sunan ya samo asali ne daga yadda al'ummar ƙasar Potigal suke kiran kogin kwango da suna nzere ko nzadi, wato ma'ana "Kogi mai haɗiye sauran koguna." To amma bayan da aka gudanar da yaƙin Kwango na farko, wanda yai sanadiyyar hamɓarar da gwamnatin Mobutu a shekarar 1997, an sake mayar wa da ƙasar sunanta na zamanin Turawan mulki, wato jamhuriyar dimokuraɗiyyar Kwango.

Ita dai jamhuriyar dimokuraɗiyyar Kwango, ƙasar Faransa ce tai mata mulkin mallaka, kuma ta kansance ne a yankin tsakiyar Afirka.

Shugaba Denis Sassou Nguesso, na jamahuriyar Kwango Babbar hanyar da ake iya rarrabe ƙasashen kwangon guda biyu ita ce, ita wannan kwangon da muke batu akai a kodayaushe ana ambatonta ne da jamhuriyar ɗimokuraɗiyyar Kwango, ko a ce DR Kwango, ko DRC, ko RDC, ko kuma a kira ta da Kwango-Kinshasa, wato a jingina mata sunan babban birninta na Kinshasa. Saɓanin ɗaya Kwango ɗin da ake mata laƙabi da Kwango-Brazzaville.

Shi dai wannan suna "Kwango" Suna ne na "Kogin Kwango", har ila yau kuma akan kira shi da Kogin Zayar (Kuma sunan ya samo asali ne daga sunan wata ƙabila da ake kira Bakongo). jamhuriyar dimokuraɗiyyar Kwango dai, ƙasa ce da ta sha amsa sunaye da dama a tarihi, inda akan ce mata 'yantacciyar ƙasar Kwango, ko Kwangon Beljiyom, ko Kwango-Kinshasa, ko kuma Zayar.

Duk da cewa ƙasar ta jamhuriyar dimokuraɗiyyar ta kasance ne a yankin tsakiyar Afirka, to amma fa ta fuskar harkokin tattalin arziki da kuma ɓangaranci, ta alaƙanta kanta ne da ƙasashen kudancin Afirka kasancewar ita mamba ce a ƙungiyar bunƙasa ƙasashen kudancin Afirka wato (SADC).

iyaka da mutunci[gyara sashe | Gyara masomin]

Jamhuriyar domokaradiyar kwango ta kasance kasa mai karamcin tattalin arziki a wani lokaci

kasar Kango Ita ce ƙasa ta uku a girman taswira a nahiyar Afirka. Sannan kuma kamar yadda ƙiyasin Majalisar Ɗinkin Duniya ya nunar, ƙasar na da yawan al'umma kimanin miliyan 66,020,000 wanda hakan ya ba ta iko zama ƙasa ta 19 a jerin ƙasashe mafiya yawan al'umma a duniya, kuma ta huɗu a yawan al'umma a Afirka, amma kuma a rukunin ƙasashen da suke magana da harshen faransanci a duniya ita ce ƙasa ta farko a yawan al'umma. Ƙasar ta yi iyaka da kasashe tara sune wa'yannen:-


Ƙasashen Afirka
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe