Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Globe icon.svgJamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango
République démocratique du Congo (fr)
Flag of the Democratic Republic of the Congo (en) Arms of the Democratic Republic of the Congo (en)
Flag of the Democratic Republic of the Congo (en) Fassara Arms of the Democratic Republic of the Congo (en) Fassara

Take Debout Congolais (en) Fassara

Kirari «Justice – Paix – Travail»
«Justice – Peace – Work»
«Справедливост - мир - труд»
«Cyfiawnder - Heddwch - Gwaith»
Official symbol (en) Fassara Okapia johnstoni (en) Fassara
Suna saboda Kogin Congo
Wuri
COD orthographic.svg Map
 2°54′S 23°42′E / 2.9°S 23.7°E / -2.9; 23.7

Babban birni Kinshasa
Yawan mutane
Faɗi 86,790,567 (2019)
• Yawan mutane 37.01 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Faransanci
Labarin ƙasa
Bangare na Afrika ta Tsakiya
Yawan fili 2,344,858 km²
• Ruwa 3.3 %
Wuri a ina ko kusa da wace teku Tekun Atalanta
Wuri mafi tsayi Mount Stanley (en) Fassara (5,109 m)
Wuri mafi ƙasa Tekun Atalanta (0 m)
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Zaire (en) Fassara
Ƙirƙira 30 ga Yuni, 1960Republic of the Congo (Léopoldville) (en) Fassara
Tsarin Siyasa
Tsarin gwamnati jamhuriya
Majalisar zartarwa Government of the Democratic Republic of the Congo (en) Fassara
Gangar majalisa Parliament of the Democratic Republic of the Congo (en) Fassara
• President of the Democratic Republic of the Congo (en) Fassara Félix Tshisekedi (en) Fassara (24 ga Janairu, 2019)
• Prime Minister of the Democratic Republic of the Congo (en) Fassara Sylvestre Ilunga (en) Fassara (7 Satumba 2019)
Ikonomi
Kuɗi Congo Franc
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Suna ta yanar gizo .cd (en) Fassara
Tsarin lamba ta kiran tarho +243
Lambar taimakon gaggawa 113 (en) Fassara, 114 (en) Fassara da 118 (en) Fassara
Lambar ƙasa CD
Tutar Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango
taswirar Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango

ƙasar Kwangosunan ta jamhuriyar Kwango, tun kafin zamanin mulkin mallaka, to amma bayan da Turawan mulkin mallaka, suka mamaye ƙasar sai suka sa mata suna, Jamhuriyar dimokuraɗiyyar Kwango, a ranar 1, ga watan Agustan, shekara ta 1964, kuma an yi haka ne da nufin banbance ta da maƙwafciyarta wadda ita ma sunanta jamhuriyar Kwango.

Jamhuriyar domokaradiyar kwango

Mobutu Sese Seko shine tsohon shugabar kasar na kwango.daga bisani kuma Zayar ta karfi Mulkin,Yadda aka yi ta samu tsohon sunanta na Zayar kuwa ya faru ne a ranar 27 ga watan Oktoban shekara ta 1971, a zamanin mulkin tsohon shugaba Mabutu Sese Seko. Kuma sunan ya samo asali ne daga yadda al'ummar ƙasar Potigal suke kiran kogin kwango da suna nzere ko nzadi, wato ma'ana "Kogi mai haɗiye sauran koguna." To amma bayan da aka gudanar da yaƙin Kwango na farko, wanda yai sanadiyyar hamɓarar da gwamnatin Mobutu a shekara ta 1997, an sake mayar wa da ƙasar sunanta na zamanin Turawan mulki, wato jamhuriyar dimokuradiyyar Kwango.

Ita dai jamhuriyar dimokuraɗiyyar Kwango, ƙasar Faransa ce tai mata mulkin mallaka, kuma ta kansance ne a yankin tsakiyar Afirka.

Shugaba Denis Sassou Nguesso, na jamahuriyar Kwango Babbar hanyar da ake iya rarrabe ƙasashen kwangon guda biyu ita ce, ita wannan kwangon da muke batu akai a kodayaushe ana ambatonta ne da jamhuriyar ɗimokuraɗiyyar Kwango, ko a ce DR Kwango, ko DRC, ko RDC, ko kuma a kira ta da Kwango-Kinshasa, wato a jingina mata sunan babban birninta na Kinshasa. Saɓanin ɗaya Kwango ɗin da ake mata laƙabi da Kwango-Brazzaville.

Shi dai wannan suna "Kwango" Suna ne na "Kogin Kwango", har ilayauk kuma, akan kira shi da Kogin Zayar (Kuma sunan ya samo asali ne daga sunan wata ƙabila da ake kira Bakongo). Jamhuriyar dimokuraɗiyyar Kwango dai, ƙasa ce da ta sha amsa sunaye da dama a tarihi, inda akan ce mata 'yantacciyar ƙasar Kwango, ko Kwangon Beljiyom, ko Kwango-Kinshasa, ko kuma Zayar.

Duk da cewa ƙasar ta jamhuriyar dimokuraɗiyyar ta kasance ne a yankin tsakiyar Afirka, to amma fa ta fuskar harkokin tattalin arziki da kuma ɓangaranci, ta alaƙanta kanta ne da ƙasashen Kudancin Afirka kasancewar ita memba ce a ƙungiyar bunƙasa ƙasashen Kudancin Afirka wato (SADC).

Iyaka da mutane[gyara sashe | gyara masomin]

Jamhuriyar domokaradiyar kwango ta kasance kasa mai karamcin tattalin arziki a wani lokaci

kasar Kango Ita ce ƙasa ta uku a girman taswira a nahiyar Afirka. Sannan kuma kamar yadda ƙiyasin Majalisar Ɗinkin Duniya ya nunar, ƙasar na da yawan al'umma kimanin miliyan 66,020,000 wanda hakan ya ba ta iko zama ƙasa ta 19 a jerin ƙasashe mafiya yawan al'umma a duniya, kuma ta huɗu a yawan al'umma a Afirka, amma kuma a rukunin ƙasashen da suke magana da harshen faransanci a duniya ita ce ƙasa ta farko a yawan al'umma. Ƙasar ta yi iyaka da ƙasashe tara su ne kamar haka:-

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]



Ƙasashen Afirka
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe