Kogi
Jihar Kogi Sunan barkwancin jiha: Jihar koguna biyu. | ||
Wuri | ||
---|---|---|
![]() | ||
Ƙidaya | ||
Harshe | Igala, Ebira, Turanci, Hausa | |
Gwamna | Yahaya Bello (APC) | |
An ƙirkiro ta | 1991 | |
Baban birnin jiha | Lokoja | |
Iyaka | 29,833km² | |
Mutunci 1995 (ƙidayar yawan jama'a) |
3,314,043 | |
ISO 3166-2 | NG-KO |
Jihar Kogi jiha ce dake a shiyar tsakiya a ƙasar Najeriya. Tana da yawan fili kimanin kilomita araba’in 29,833 da yawan jama’a milyan uku da dubu dari uku da sha huɗu arba'in da uku (ƙidayar yawan jama'a shekara 2006). Babban birnin jihar ita ce Lokoja. Yahaya Bello shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2015 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Simon Achuba. Dattijan jihar su hada: Isaac Alfa, Ahmed Ogembe da Dino Melaye.
Jihar Kogi tana da iyaka da misalin jihhohi sha ɗaya, su ne: Abuja, Nijar, Kwara, Ekiti, Ondo, Edo, Anambra, Enugu, Benue, Nasarawa da Kaduna.
.
Kogi na daga cikin jahohin dake a tsakiyar kasar Nigeriya ana kiranta da mahadar ruwa saboda gamuwar ruwan (kogin Nijar da kogin Benue) a babban birninta Lokoja a wannan zamani a Nijeriya. Noma da kamun kifi sune manyan aikin mutanen wannan jihar da kuma sayar da gawayi.
Kananan hukumomi[gyara sashe | Gyara masomin]
Jihar Kogi nada adadin Kananan hukumomi ashirin da daya (21). Wadanda sune:
- Adavi
- Ajaokuta
- Ankpa
- Bassa
- Dekina
- Ibaji
- Idah
- Igalamela-Odolu
- Ijumu
- Kabba/Bunu
- Koton Karfe
- Lokoja
- Mopa-Muro
- Ofu
- Ogori/Magongo
- Okehi
- Okene
- Olamaboro
- Omala
- Yagba ta Gabas
- Yagba ta Yamma
Jihohin Najeriya |
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |