Neja

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Globe icon.svgNeja
Gurarafalls.jpg

Suna saboda Nijar
Wuri
NigeriaNiger.png
 10°N 6°E / 10°N 6°E / 10; 6
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Minna
Yawan mutane
Faɗi 5,556,247 (2016)
• Yawan mutane 72.76 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 76,363 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi North-Western State (en) Fassara
Ƙirƙira 3 ga Faburairu, 1976
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa executive council of Niger State (en) Fassara
Gangar majalisa Niger State House of Assembly (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-NI
Wasu abun

Yanar gizo nigerstate.gov.ng
Dutsen Zuma kenan na jikin Naira dubu dake a niger
Lambar mota kenan ta niger

Jihar Neja Jiha ce dake kudu maso, yammacin, Najeriya. Tana da yawan fili kimanin na kilomita murabba’in 76,363 da yawan jama’a miliyan uku da dubu dari tara da hamsin da huɗu da ɗari bakwai da saba'in da biyuƙidayarar yawan jama'a na shekara ta 2006).Babban birnin tarayyar jahar ita ce Minna. Abubakar Sani Bello shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2015 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Ahmed Muhammad getso. Jahar ta Neja tanada manyan mutane da dama waɗanda suka rike manyan mukamai a kasar Najeriya sannan jaha ce wacce ta ke da tsofaffin shugabanni ƙasa na Najeriya har guda biyu a lokacin mulkin soja, wato Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) mai ritaya da kuma Abdusalami Abubakar mai ritaya dukkaninsu mutanan Jahar ta Naija ne.[1][2]

Manyan kananan hukumomin Jahar sune, Chanchaga, Bosso da kuma kananan hukumomin Bidda, Suleja da kuma Kontagora.

Manyan yarukan jahar sune Nufanchi, Hausa, Gbagi da kuma turanci inda yankunan Bidda da Agaie da kuma Lapai, Mokwa sukafi yawan masu amfani da yaren Nufanci, Yankin Kontagora, Kagara, Mariga, Mashegu Rijau, Suleja sukeda mafi rinjayen masu amfani da yarukan Hausa. Paikoro, Chanchaga, Bosso, Edati dadai sauransu suna amfani da saura yarokan a matsayin masu rinjaye.

al'adar daka doya a jihar niger

Akwai wuraren tarihi sosai a jahar ta Neja musamman a garin Zungeru inda anan nan ne turawan Yamma suka sanya hannun domin hadewan Najeriya kasa daya daga sauran yankuna sannan a wannan garin ne gwamnan farko na Najeriya ya yada zango a matsayin hedikwata gareshi.

Alhaji Umar Farouk Bahago shine sarkin Minna

Jihar neja tana da iyaka da misalin jahohi shida, sune: Babban birnin tarayya, Kwara, Kogi, Kaduna, Kebbi kuma da Zamfara. [3]

Kananan Hukumomi[gyara sashe | Gyara masomin]

Jihar Neja nada Kananan Hukumomi guda ashirin da biyar (25). Sune:

Ilimi[gyara sashe | Gyara masomin]

Jihar Neja na da manyan jami'oi na ilimi wanda suka hada da:

  • Federal Polytechnic, Bida[4]
  • Federal University of Technology Minna
  • Niger State Polytechnic, Zungueru.[5].

Yaruka[gyara sashe | Gyara masomin]

An jero yaruka jihar Neja dangane da kananan hukumomin da ake amfani da su;[6]

LGA Languages
Agaie Nupe, Dibo; Kakanda;
Agwara Cishingini
Bida Nupe, BassaNge, Gbari
Borgu Busa, Bisã; Boko; Cishingini; Laru; Reshe
Chanchaga Basa-Gumna; Basa-Gurmana; Gbagyi; Gbari; Nupe; Kamuku; Tanjijili
Edati Nupe, BassaNge
Gbako Nupe
Gurara Gwandara, Gbagyi
Katcha Nupe, Dibo; Kupa
Kontagora Acipa, Eastern; Asu; Tsishingini; Tsuvadi
Lapai Nupe, Dibo; Gbari; Gupa-Abawa; Kakanda; Kami;
Magama Lopa; Tsikimba; Tsishingini; Tsuvadi
Mariga Baangi; Bassa-Kontagora; Cicipu; Kamuku; Nupe; Rogo; Shama-Sambuga; Tsikimba; Tsishingini; Tsuvadi
Mashegu Asu; Tsikimba; Tsishingini; Nupe-Tako
Minna Nupe; Gbari; Gbagyi
Mokwa Nupe, Yoruba; Gbari
Munya Adara
Paikoro Gbari; Kadara
Rafi Basa-Gurmana; Bauchi; Cahungwarya; Fungwa; Gbagyi; Gbari; Kamuku; Pangu; Rogo; Shama-Sambuga
Rijau Fulani; C'Lela; Tsishingini; Tsuvadi; ut-Hun
Shiroro Gbagyi; Gurmana
Suleja Gbagyi; Gbari; Gwandara; Nupe; Tanjijili
Wushishi Hausa; Nupe; Gbari


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. "Kainji Lake National Park". United Nations Environment Programme: World Conservation Monitoring Centre. Archived from the original on 30 September 2007. Retrieved 21 October 2010.
  2. "Boko Haram ta mamaye garuruwa da dama a jihar Neja". 4 October 2021. Retrieved 10 October 2021. Unknown parameter |= ignored (help)
  3. https://www.britannica.com/place/Niger-state-Nigeria
  4. Keetu (19 August 2017). "List Of Accredited Courses,Offered In Federal Polytechnic Bida (Fed Poly Bida)". Retrieved 26 August 2021.
  5. "Updated List of Courses Offered In FUTMINNA forJAMB 2021,Registration". O3schools. 5 March 2021. Retrieved 26 August 2021.
  6. "Nigeria". Ethnologue (22 ed.). Retrieved 26 August 2021.