Abdulsalami Abubakar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Abdulsalami Abubakar a shekara ta 1998.

Abdulsalami Abubakar tsohon janar din Soja ne kuma ɗan siyasa. An haife shi a shekara ta 1942 a Minna, Arewacin Najeriya (a yau jihar Neja). Abdulsalami Abubakar shugaban kasar Nijeriya ne daga Yuni 1998 zuwa Mayu 1999 (bayan Sani Abacha - kafin Olusegun Obasanjo).