Musulunci

Daga Wikipedia
A tsallaka zuwa: Shawagi, nema
Al'Quran mai tsarki
Dakin ka'aba me girma dake birnin Makkah
Wannan wurin launin kore sune kasashin Musulunci

Musulunci shi ne addinin da mafiya yawan Hausawa suke bi. Kimanin kaso 90 ne na Hausawa suke bin addinin musulunci. Ma'anar Musulunci shine "Mika wuya ga kadaituwan Allah (SWT) cikin abubuwan da ya kebantu dasu, da mika wuya ga umarnin Allah Ubangijin talikai, tare da tsarkaka daga kafirci (sanya kishiya wa Allah) da kafirai." Allah (SWT) shi ya aiko Annabi Muhammadu (Yabo da Amincin Allah su Tabbata a gare shi) da Al Kur'ani Mai Girma. Yanzu haka, akwai fiye da Musulmai Biliyan Daya da Miliyan dubu dari biyar a fadin duniya.

Tarihin Addinin Musulunci[gyarawa | Gyara masomin]

Asalin addini a duniya shi ne musulunci. Mutum na farko da Allah ya halitta, Annabi Adam (alaihis salam), ya rayu ne bisa tafarkin musulunci. Dukkanin manzanni tun daga Annabi Nuhu (alaihis salam), zuwa Annabi Ibrahim, da Annabi Musa, da Annabi Isa, alaihimus salam, musulmai ne ma su kadaita Allah. Sai dai gaba dayansu Allah ya aikosu ne zuwa ga al'ummominsu kadai. Annabi na karshe kuma cikamakin tsarin annabawa shi ne Annabi Muhammadu (yabo da amincin Allah su tabbata a gareshi). Allah ya aiko Annabi Muhammadu (SAW) da sako zuwa ga daukacin al'ummar duniya, mutane da aljannu. An haifeshi a birnin Makkah da a yanzu ke kasar Saudi Arabia. Annabi Muhammadu (SAW), bakureishe ne, dan Abdullahi da Amina daga tsatson Annabi Isma'ila (AS) dan Annabi Ibrahim (AS).

Shika Shikan Musulunci[gyarawa | Gyara masomin]

Shika shikan Musulunci guda biyar (5) ne kamar haka :

  • TAUHIDI
  • SALLAH
  • AZUMI
  • ZAKKA
  • HAJJI (ga wanda ke da iko)

Kalmar Shahada[gyarawa | Gyara masomin]

Ma'anarsa shine shaidawa babu abun bauta bisa cancanta sai ALLAH (SWT), sa'annan Annabi Muhammad (SAW) Manzon Allah ne.

Sallah[gyarawa | Gyara masomin]

Sallah yana daga cikin shika shikan Musulunci mai mahimmanci matuka bayan Tauhidi, ana bukatar kowanne musulmi yayi Sallah sau biyar a rana, yana mai fuskantar Ka'aba dake kasar Saudiya. A kasashen Musulmai, za'a ke jin Kiran Sallah daga Masallaci mafi kusa a yayin da lokacin Sallah yayi. Sallah ana yinta ne cikin Natsuwa, domin a samu kyakkyawan lada.

Musulmai suna Sallah a wani Masallacias

Azumi[gyarawa | Gyara masomin]

Azumi: Wannan rukuni ne wanda ake nufin barin ci, da sha, da yin jima'i daga fitowan alfijir har zuwa faduwan rana. Dukkan musulmi tilas ne da ya/ta azimci watan Ramalana (watau wata na tara a kalandar musulunci).

Zakka[gyarawa | Gyara masomin]

Shine cire wani kayyadadden kaso, daga cikin wasu kayyadaddun dukiyoyi, a cikin wani kayyadadden lokaci ga wasu kayyadaddun mutane, domin Allah (SWT).

Masallacim Kudus shine guri na uku mafi tsarki a wajen musulmai a duniya

Hajji[gyarawa | Gyara masomin]

Shine zuwa ziyartan dakin Allah Mai Alfarma ga wanda keda iko da nufin Ibada.

Imani[gyarawa | Gyara masomin]

Ma'anan Imani shine : abun da zuciya ta kudurta, harche yayi furuci da shi, sa'annan gabban jiki suka yi aiki da shi. Imani yana da shika-shikai guda shida (6) kamar haka : Imani da Allah, da Mala'ikunsa, da littafansa, da Manzanninsa, da Ranar karshe, da Imani da kaddara mai dadi ko marar dadi.