Zakka

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zakka
religious behaviour (en) Fassara
Bayanai
Bangare na Rukunnan Musulunci

Zakkah ɗaya ce daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar wadda ta ke zama wajibi a kan dukkan wani musulmi namiji da mace, yaro da babba. Ana fitar da ita ne daga cikin dukiyar da mutum ya mallaka Wanda ya hada da tsabar kudi, kadara, da kuma ma'adanai wanda yakai tsawon wani adadi na musamman sannan kuma ta kai wani lokaci kebantacce zuwa ga wadansu kebantattun mutane.[1][2] Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa a cikin Alqur'ani mai girma a cikin suratul Baƙarah, وَأَقِيمُواْ الصَّلاَةَ وَآتُواْ الزَّكَاةَ وَارْكَعُواْ مَعَ الرَّاكِعِينَ Aya-43.

wanda za abama zakka[gyara sashe | gyara masomin]

Masu cin Zakkah mutane takwas ne (8) kamar yadda Ayar Alqur'ani tayi bayani akansu.

  1. Talakawa (Faqirai)
  2. A kan Tafarkin Allah (Fi sabilillihi)
  3. Bayi
  4. Waɗanda ake jansu zuwa musulunci
  5. Miskinai
  6. Matafiyi wanda bada saɓon Allah ba
  7. Waɗanda ake bi bashi
  8. Masu aiki a kan dukiyan zakka

wadanda bai kamata aba zakka ba sune;

  1. Masu arziki
  2. Wanda sukayi ridda watau suka bar Addinin Musulunci
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Nura Bala, Ibrahim (22 September 2018). "Hukumar raba zakka na jihar Sokoto ta bada tallafin N 7.4m ga gajiyayyu a jihar". legit.hausa.ng. Retrieved 22 November 2021.
  2. "Zakkah". Retrieved 22 November 2021.