Muhammad

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Muhammad
Dark vignette Al-Masjid AL-Nabawi Door800x600x300.jpg
Rayuwa
Cikakken suna مُحَمَّدٌ
Haihuwa Makkah, ga Afirilu, 26, 570
Mazaunin Makkah
Madinah
ƙungiyar ƙabila Larabawa
Harshen uwa Larabci
Mutuwa Madinah, ga Yuni, 8, 632
Makwanci Sacred Prophetic Chamber (en) Fassara
Green Dome (en) Fassara
Yan'uwa
Mahaifi Abdullahi dan Abdul-Muttalib
Mahaifiya Amina yar Wahb
Yara
Siblings
Ƙabila Banu Hashim (en) Fassara
Karatu
Harsuna Classical Arabic (en) Fassara
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a herder (en) Fassara, consignor (en) Fassara, merchant (en) Fassara, Annabawa a Musulunci, preacher (en) Fassara, ɗan siyasa da military leader (en) Fassara
Muhimman ayyuka Al Kur'ani
Aikin soja
Ya faɗaci Badar
Yaƙin Uhudu
Yaƙin gwalalo
Battle of Khaybar (en) Fassara
Battle of Hunayn (en) Fassara
Battle of Tabouk (en) Fassara
Imani
Addini Hanif (en) Fassara
Musulunci

Muhammadu da Hausa, da (larabci مُحَمَّد‎) furuci [muħammad]; haihuwa c. 570 CE – 8 Juni 632 CE) Annabi ne kuma Manzo, wato ma'aikin Allah Madaukakin Sarki. Allah Ya aiko shi domin ya tabbatar da addinin da Annabawan da suka gabace shi suka koyar, Kamar Annabi Ibrahim da Annabi Musa da Annabi Annabi Isah da dukkannin sauran Annabawan Allah, (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare su), Annabi Muhammad (s.a.w) shine cikamakon Annabawa, wato Annabin karshe wanda daga kansa babu wani, shine kuma ya hada kan dukkan larabawa suka dunkule waje daya, tare da daidaita yan adam ta hanyar koyar da su Al Kur'anin da hadisi.

Suna da ambato[gyara sashe | Gyara masomin]

Da harshen hausa akan ce Mahammadu, Mamman, ko Mahammada, dukkannin waɗannan sunayen da hausa ne malan bahaushe yake kiran Muhammad (S.A.W) , kalman Muhammad (محمد)‎, asali kalman larabci ce, tana nufin wanda ake godemawa, akan juya jinsin kalman a larabci ace, Ahmad ko Mahmud, wanda dukkannin sunan yana da alaƘa ne da godiya, sunan shi yazo sau hudu a Al Kur'ani[1] sannan a Al Kur'ani an kirashi da sunan annabi, manzo, bawan Allah, bashir (mai bushara)[Quran 2:119], da kuma shahid (mai shaidawa)[Quran 33:45] dakuma da kuma mubashshir (mai bushara) da kuma nathir(mai jan kunne)[Quran 11:2] da kuma mudhakkir(mai kira zuwa ga Allah)(dā'ī),[Quran 12:108] da kuma noor (mai haske)[Quran 05:15] da kuma sirajan munira(fitila mai haske).

Nasabar sa[gyara sashe | Gyara masomin]

Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muɗɗalibi ɗan Hashimi ɗan Abdu-Manafi ɗan Ƙusayyi ɗan Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam, (Harshen Larabci: Abūl-Qāsim Muḥammad ibn ʿAbd Allāh ibn ʿAbd al-Muṭṭalib ibn Hāshim ibn ˁAbd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) nasabarsa maɗaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam. Manzon Allah ne. Khataman-Nabiyyin da addinin Musulunci.

Dangin sa[gyara sashe | Gyara masomin]

Asalin sa bakurayshe ne, daya daga cikin kabilun larabawa, ya samo asali ne tin daga zurriyyan Annabi Ibrahim.

Matan sa[gyara sashe | Gyara masomin]

Annabin Musulunci Muhammad Ya auri mata goma sha uku, ga Jerin sunayen su.

 1. Khadija bint Khuwaylid, shekaran aure 595–619
 2. Sawda bint Zamʿa, shekaran aure 619–632
 3. Aisha bint Abi Bakrc, shekaran aure 623–632
 4. Hafsa bint Umar, shekaran aure 624–632
 5. Zaynab bint Khuzayma, shekaran aure 625–627
 6. Hind bint Abi Umayya, shekaran aure 625–632
 7. Zaynab bint Jahsh, shekaran aure 627–632
 8. Juwayriyya bint al-Harith, shekaran aure 628–632
 9. Ramla bint Abi Sufyan, shekaran aure 628–632
 10. Rayhana bint Zayd, shekaran aure 629–631
 11. Safiyya bint Huyayy, shekaran aure 629–632
 12. Maymunah bint al-Harith, shekaran aure 630–632
 13. Maria al-Qibtiyya, shekaran aure 630–632

Madogaran hujjoji dangane da tarihin sa[gyara sashe | Gyara masomin]

Qur'an Asalin shafin na nan, duba Al Kur'ani[gyara sashe | Gyara masomin]

Akan tattara tarihin sa daga qur'ani domin nan ne inda Allah ya bayar da labarin sa kai tsaye ga duniya ta tahanyar wahayi.

Hadisi Asalin shafin na nan, duba Hadisi[gyara sashe | Gyara masomin]

Ana dogara da bayar da tarihin sa idan ya tabbata a cikin hadisi ingantacce.

Tarihin bayan wahayi[gyara sashe | Gyara masomin]

Akan yi dogoro da bayar da tarihin sa kafin zuwan qur'ani da hadisi, duba da kuma la'akari da wanda ya bayar da larabin, kaman Halimatus sa'adiya, ta bayar da labarin sa tin kafin a aiko shi, a lokacin tana shayar da shi, da kuma waɗanda sukayi rayuwa da shi kafin a aik shi da manzanci.

Larabawa a lokacin jahiliyya[gyara sashe | Gyara masomin]

Annabi Muhammad (s.a.w) ya kasan ce gabanin musulunci baya bauta ma gumaka, kuma baya shirka, kuma mutum ne wanda baya karya ko cin amana, har ya sa ma mutanan Makkah suke masa laƙabi da amintacce.

Rayuwar sa[gyara sashe | Gyara masomin]

Yarinta[gyara sashe | Gyara masomin]

Farkon wahayi[gyara sashe | Gyara masomin]

ƙin yarda da shi[gyara sashe | Gyara masomin]

Isra'i da mi'itaji[gyara sashe | Gyara masomin]

Rayuwar shi kafin hijira[gyara sashe | Gyara masomin]

Hijira[gyara sashe | Gyara masomin]

Hijira zuwa Madina[gyara sashe | Gyara masomin]

Bayan Tsanani da takurawar Kafuran Makkah akan Annabi Muhammad (s.a.w) da wadanda sukayi inami da shi yayi yawa, sai Allah Yayi ma Manzon Sa da sauran Wadan da sukayi imani da shi izinin akan suyi kaura daga garinsu na haihuwa wato birnin Makka zuwa wani garin daban na wati Madina. Mutanen birnin Madina kuwa sunyi matukar murna da zuwan sa garin su kuma sun bashi kyakkyawan masauki. Sanna kuma sukayi imani dashi suka shiga AddiMusulunci. A farkon Hijira dai Shi Annabi da kansa dakuma babban aminin sa kuma na farko wajen imani dashi wato Sayyadina Abubakar Sukayi tasu hijirar tare. Sannan sauran musulmai sukayi ta bin bayansu daya bayan daya. Kaurar Annabi (s.a.w) daga Makka zuwa Madina shine ake kira Hijira kuma shine farkon kalandar Musulunci.

Kafa daulan musulunci a Madina[gyara sashe | Gyara masomin]

YaƘi[gyara sashe | Gyara masomin]

Ƴakin Badar[gyara sashe | Gyara masomin]

Shine yaki na farko a tarihin musulunci, domin karbo ma musulmai haƘƘoƘin su da'aka kwace a lokacin yin hijira zuwa Madina[2]

Ƴakin Uhudu[gyara sashe | Gyara masomin]

Yaƙi na biyu a musulunci, a dalilin rashin yardan mutanan Makka akan yaƘin Badr[3]

Ƴaƙin gwalalo[gyara sashe | Gyara masomin]

Abu sufyan ya tattaro kimanin mutane dubu goma daga yankin larabawa domin daukan fansan mutanen da'aka kashe musu da kuma dukiyan sukayi asara a yakin Badar da kuma Uhudu, a inda musulmai suka kai kimanin mutane 3,000[4]

Sulhun hudaibiyya[gyara sashe | Gyara masomin]

Cin garin Makkah[gyara sashe | Gyara masomin]

Ƴakan kasar larabawa[gyara sashe | Gyara masomin]

Hajjin ƙarshe[gyara sashe | Gyara masomin]

Wafati da kabari[gyara sashe | Gyara masomin]

Iyayen Sa[gyara sashe | Gyara masomin]

Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (Āminah) 'yar Wahbi ɗan Abdu-Manaf ɗan Zuhrata ɗan Kilabi (Radhi Allahu anha). Alkunyarsa: Abu-Qasim, Abu Ibrahim.

Mahaifinsa: Shi ne Abdullahi dan Abdullahi dan Abdulmutallabi dan Hashimu dan Abdumunaf dan Qusay dan Kilab (Allah ya kara yarda a gareshi)

Laƙabinsa: Al-Musɗafa (zababben Allah) yana da sunaye da suka zo a cikin Ƙur'ani Mai Girma kamar, Khataman-Nabiyyin, da Al-Ummi da Al-Muzzammil da Al-Muddassir da An-Nazir da Al-Mubin da Al-Karim da An-Nur da An-Niˁima da Ar-Rahma da Al-ˁAbdu da Ar-Ra'uf da Ar-Rahim da Ash-Shahid da Al-Mubasshir da An-Nazir da Ad-Da'i da sauransu.

Haihuwar Sa[gyara sashe | Gyara masomin]

An haifi Annabi Muhammad (s.a.w) a wajen shekara ta 570M. Mahaifinsa shine Abdullahi ya rasu kafin haihuwar Sa. Mahaifiyar sa Amina itama ta rasu lokacin da yake dan shekara shida a [[duniya]. Haka yasa kakan sa Abdul-Mudallib ya rike shi har zuwa lokacin daya rasu, lokacin Annabi Muhammad (s.a.w) yana dan shekara takwas a duniya. Daga nan sai kawun sa Abu-Talib yaci gaba da rikon sa. Abu-Talib ya taimaka ma Manzon Allah (s.a.w) sosai a rayuwar sa.

Aiko Shi[gyara sashe | Gyara masomin]

Kogon Hira, wajen da aka fara wa Annabi Wahayi

Aikoshi: An aiko shi ga mutane baki daya, amman ya fara da'awan musulunci a cikin garin Makkah a shekara 2 kafin hijira, a cikin watan Rajab 27, yana ɗan shekara arba'in.

Da'awa[gyara sashe | Gyara masomin]

Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makkah a ɓoye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma, ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da 'yan-uwantaka da rangwame na gaba ɗaya ga wanda ya shiga musulunci, sa'annan ya kafa shari'a maɗaukakiya da dokoki na adalci da ya karɓo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karɓa daga gare shi.

Mu'ujizozinsa[gyara sashe | Gyara masomin]

Mu'ujizarsa madauwamiya ita ce Ƙur'ani amma waɗanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.

Amsa kira[gyara sashe | Gyara masomin]

Yawancin masu amsa kiran sa talakawa ne da kuma bayi da miskinai.

Karyata shi[gyara sashe | Gyara masomin]

Abu lahab shine mutum na farko da ya fara karya ta shi bayan ya kira dukkannin dangin sa makusanta.

Iyalan gidansa[gyara sashe | Gyara masomin]

Ammomin sa[gyara sashe | Gyara masomin]

Ammominsa: Tara ne, su 'ya'yan ˁAbdul-Muɗɗalib ne: Al-Haris da Zubair da Abu Ɗalib da Hamza da Al-Ghaidaq da Dirar Al-Muqawwam da Abu Lahab da ˁAbbass.

Ammominsa mata: Su shida ne daga iyaye mata daban-daban su ne: Aminah da Ummu Hakima da Barra da Atiqa da Safiyya da Arwa. Wasiyyansa goma sha biyu ne, su ne: Amirul-Mu'minina Ali ɗan Abi Ɗalib (a.s) da Hasan ɗan ˁAli da Hussain ɗan ˁAli da ˁAliyyu ɗan Husaini da Muhammad ɗan ˁAli da Jaˁfar ɗan Muhammad da Musa ɗan Jaˁfar da ˁAli ɗan Musa da Muhammad ɗan ˁAli da ˁAli ɗan Muhammad da Alhassan ɗan ˁAli da Muhammad ɗan Hassan Mahadi (a.s).

Ya'yayen sa[gyara sashe | Gyara masomin]

 • Qasim ibn Muhammad, (598 – 600 ko 601 M)
 • Zainab bint Muhammad, (599 – 630 M)
 • Ruqayyah bint Muhammad, (601 – 624 M)
 • Umm Kulthum bint Muhammad, (603 – 630 M)
 • Abd-Allah ibn Muhammad, (d. 615 M)
 • Fatimah bint Muhammad, (c. 615 – 632 M)
 • Ibrahim ibn Muhammad, (630 – 631 M)

Sahabban sa[gyara sashe | Gyara masomin]

Mai tsaron ƙofarsa: Anas ɗan Malik.

Mawaƙinsa: Hassan ɗan Sabit, da ˁAbdullahi ɗan Rawahata, da Ka'abu ɗan Malik.

Mai kiran sallarsa: Bilal Al-Habashi da ˁAbdullahi ɗan Ummu Maktum da Saˁad Al-Kirdi.

Tambarin zobensa: Muhammadur Rasulullah!

Tsawon rayuwarsa: shekaru 63.

Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23.

Tarihin wafatinsa: 28 Safar 11 H.

Wajan da ya yi wafati: Madinah.

Inda aka binne shi: Madinah a Masallaci Maɗaukaki Mai Alfarma. Ka sani cewa Muhammad (S.A.W) shi ne ƙarshen annabawa kuma addininsa shi ne musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari'arsa zata wanzu har zuwa qiyama kuma ita kaɗai ce shari'ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa ƙarshen rayuwar duniya da lahira. Kamar yadda shi kaɗai ne mutum abin koyi ga dukkan duniya baki ɗaya, dukkan mutanen duniya idan suna son alheri ga kawukansu to dole ne su bi tarfarkinsa su yi koyi da kyawawan halyensa (S.A.W) da kuma sanin sashen tarihinsa da ba makawa mu kawo wasu daga siffofinsa (S.A.W): Shi ne Muhammad ɗan ˁAbdullah (S.A.W) kuma babarsa ita ce Aminatu 'yar Wahab. An haife shi a Makkah ranar juma'a goma sha bakwai ga watan Rabi'ul awwal bayan ɓollolwar alfijir a shekarar giwa, a zamanin sarki mai adalci Kisra . (wato idan an kwatanta shi da ire-irensa).

Aiko Annabi Mai Daraja (S.A.W)

An aiko Annabi Muhammad (S.A.W) da saqo a 27 ga Rajab bayan yana ɗan shekara 40 yayin da Jibrilu (A.S) ya sauka gareshi daga wurin Allah (S.W.T) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makkah ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Alaƙi . Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makkah a lokcin akwai jama'a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da saƙon Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi yana cewa da su: "Ku ce babu abin bauta sai Allah kwa rabauta" .

A lokacin tunda mutanen Makkah mushrikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka riƙa yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk sa'adda ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutar da shi har ya ce: "Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni" . Ba wanda suka yi imani da shi sai mutane ƙalilan, na farkonsu Imam ˁAli sannan sai matarsa Khadijah (A.S) sannan sai wasu mutane. Farkon wanda ya yi imani da shi daga maza Imam Ali sannan daga mata sai Hadiza (A.S).

Yayin da takurawar mushrikai ta yi yawa sai ya yi hijira zuwa Madinah wannan kuwa ita ce hijirar farko a tarihin Musulmi, yayin da suka yi yawa sai qarfinsu ya daɗu kuma suka samu koyarwa daga Manzon Allah da shari'arsa Mai Sauƙi Mai Hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da mutumtaka da wayewa da cigaba a Madinah har suka fi dukkan duniya da addini na sama da waɗanda ba na sama ba. Kuma an samu yaƙoƙi masu yawa a Madinah kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga maƙiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zaɓar ɓangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin waɗanda ake kashewa daga ɓangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yaƙoƙinsa tamanin da wani abu, wato; waɗanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu ɗaya da ɗari huɗu ba.

Mutuwa Mai Zafin Gaske Tun lokacin da aka aiko Annabi da saƙo har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu (A.S) shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji (S.W.T) a hankali a hankali har littafin Ƙur'ani ya ciki a cikin shekaru ishirin da uku, sai Manzo (S.A.W) ya yi umarni da a haɗa shi kamar yadda yake a yau ɗin nan. Manzo (S.A.W) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu'amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu.

Kulafa'u[gyara sashe | Gyara masomin]

Dabi'u[gyara sashe | Gyara masomin]

Siffofi[gyara sashe | Gyara masomin]

Daraja[gyara sashe | Gyara masomin]

Kamanni[gyara sashe | Gyara masomin]

Siyasa[gyara sashe | Gyara masomin]

Annabi Muhammad yayi zamanta kewa da yahudawa a madina da kuma mushrikai a Makkah, ya kulla yarje jeniya da yahudawa akan cewa basu hada kai da kowa ba domin a yake shi ba, shima ya amince bazai bari wasu su yake su, sai daga baya suka karya alkawari, sannan Annabi yasa aka yake su a Yakin Banu kuraiza.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

 1. https://en.wikipedia.org/wiki/Encyclopedia_of_the_Quran
 2. https://en.wikipedia.org/w/index.php?title=Muhammad&action=edit&section=2#cite_note-EoI-Muhammad-19
 3. https://en.wikipedia.org/w/index.php?title=Muhammad&action=edit&section=2#cite_note-135
 4. https://en.wikipedia.org/w/index.php?title=Muhammad&action=edit&section=2#cite_note-149

Bibiliyo[gyara sashe | Gyara masomin]

 • Peters, F. E. (Francis E.) (2003). Islam, a guide for Jews and Christians. Princeton, NJ: Princeton University Press. ISBN 0-691-11553-2. OCLC 50960849.
 • Aʻẓamī, Muḥammad Muṣṭafá. (2003). The history of the Qur'ānic text : from revelation to compilation : a comparative study with the Old and New Testaments. Leicester: UK Islamic Academy. ISBN 1-872531-65-2. OCLC 53124427