Jump to content

Muhammad Al-Bukhari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Muhammad Al-Bukhari
Fayil:محمد بن إسماعيل البخاري.png
Rayuwa
Haihuwa Bukhara (en) Fassara, 20 ga Yuli, 810
ƙasa Daular Abbasiyyah
Mutuwa Samarkand (en) Fassara, 1 Satumba 870
Makwanci Al Bukhari Memorial (en) Fassara
Ƴan uwa
Mahaifi Ismail ibn Ibrahim
Karatu
Harsuna Larabci
Malamai Ahmad Ibn Hanbal
Ali ibn al-Madini (en) Fassara
Yahya ibn Ma'in (en) Fassara
Ishaq Ibn Rahwayh (en) Fassara
Al-Darimi (en) Fassara
Q12183100 Fassara
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a muhaddith (en) Fassara, maiwaƙe, Ulama'u, Islamic jurist (en) Fassara da Masanin tarihi
Muhimman ayyuka Sahi al-Bukhari
al-Adab al-mufrad (en) Fassara
al-Tārīkh al-kabīr (en) Fassara
Q19492250 Fassara
Q19455078 Fassara
Imani
Addini Musulunci
Mabiya Sunnah
Fayil:محمد بن إسماعيل البخاري.png
Anyana sunan Muhammad Al-Bukhari
Imam Bukhari

Imamul Bukhari Asalin sunansa shine Muhammad bin Isma’il bin Ibrahim bin Mugira, Abu Abdullah, Al-Ju’ufi, Ana masa kirari da Malamin Malamai na duniya face Malamin sa (Imam Malikk), kuma jagora wajen sanin fiqihun hadisi, yayi karatu a wurin malaminsa wato Babban Malamin nan Imam Malik Ibn Anas.

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Imamul Bukhari ranar Juma’a sha uku ga watan Shawwal shekara ta (194 A.H), a garin Bukhara ƙasar Uzbekistan, mahaifinsa ya rasu tun yana yaro, don haka ya taso a karkashin kulawar mahaifiyarsa.[1] Imamul Bukhari ya kasance a lokacin da yake yaro ya samu matsala a ganinsa sai ya zamanto ba ya gani, Wata rana mahaifiyarsa sai ta yi mafarki da Annabi Ibrahim (AS), sai ya ce mata: Allah ya dawowa da danki ganinsa, da gari ya waye sai taga idon danta ya bude. [2]Allah ya yiwa imamul Bukhari baiwa ta haddar hadisai, harma ana hikaito cewa ya haddace hadisai (70,000) tun yana dan shekara (16), shi yasa wani daga cikin malamai yake cewa: duk hadisin da Imamu Bukhari bai san shi ba, to ba hadisi ba ne, har wasu Malamai ma suna gabatar da shi a wajen sanin hadisi da fiqihun hadisi a kan imam Ahmad da Ishaq. Imam Muslim ya yi karatu a wajensa.[3].

Neman Iliminsa

[gyara sashe | gyara masomin]

Imam Bukhari ya fara karatun Hadisi tun yana karami. Ya kammala karatun sa na farko, musamman na Hadisi a Bukhara (garin haihuwar sa). Yana shekara 16 ya haddace littafai da dama na mashahuran malamai ciki har da littafin 'Al-waki' na Abdullahi Ibn Al-Mubarak. Bayan haddar Hadisi da littafan Malaman farko, ya kuma fara karanta tarihin dukkan masu ruwaito Hadisi (Rawi) waɗanda suka yi ruwa da tsaki wajen watsa Hadisai, da kuma haddar Ranar haihuwarsu da rasuwarsu, wurin haihuwarsu da sauransu.

Imam Bukhari yana ɗan shekara sha takwas ya ziyarci Makka tare da rakiyar Mahaifiyarsa da ɗan uwansa, sun dawo Bukhara bayan kammala aikin Hajjin su amma Imam Bukhari ya zauna a can don neman ilimi. Ya yi shekara biyu a Makkah, ya kuma koyi Hadisi da sauran karatun addini a wajen Malaman Musulunci na Makkah. Bayan haka ya tafi Madina ya kara ilimi a fannin Hadisi da Fiqhu na tsawon shekaru huɗu. Bayan ya yi shekara shida a Makkah da Madina, ya tafi Basrah, Kufa da Baghdad, ya ziyarci kasar Masar da Sham (Syria). Shi da kansa ya ce:

"Domin neman ilimi na yi tafiya Masar da Sham sau biyu, Basrah sau hudu, na yi shekaru shida a Hijaz (Makkah da Madina) na tafi Kufa da Baghdad a lokuta da dama tare da Muhaddithin (Masu tattara Hadisi ko masana Hadisi)".

An bada labari da yawa game da gwagwarmayar Imam Bukhari wajen tattara Hadisai. Ya zagaya wurare daban-daban don kawai ya tattaro maganganu masu daraja da suka fito daga bakin Manzon Allah (SAW).

A tafiye-tafiyen da ya yi a kasashe daban-daban, Imam Bukhari ya gana da manyan malamai wadanda za'a iya amincewa da su. Shi da kansa ya ce ya rubuta Hadisai daga malamai 1,080 kuma dukkansu kwararrun Malaman Hadisi ne.[4]

Daga cikin malamansa akwai:

~ Ali bin Al-Madini

~ Imam Ahmad bin Hanbal

~ Yahya ibn Ma'een

~ Muhammad bin Yusuf Al-Firyabi

~ Muhammad bin Yusuf Al-Baykandi

~ Ishaq Ibn Rahwayh

Da sauran su.

Ba a san adadin mutanen da suka ruwaito Hadisi daga Imam Bukhari ba. Sai dai kamar yadda wasu bayanai suka nuna, kusan mutane 90,000 ne suka ji Hadisai kai tsaye daga Imam Bukhari.

Daga cikin daliban Imamul Bukhari akwai:

~ Muslim bin Hajjaj (wanda aka fi sani da Imam Muslim)

~ Abu Isa Muhammad Al-Tirmidhi (wanda aka fi sani da Imam Al-Tirmidhi)

~ Abu Abd-ur-Rahman Ahmad ibn Shuaib Al-Nasai (wanda aka fi sani da Imam Al-Nasai)

~ Abdullah bin Abd-ur-Rahman Al-Darimi

~ Muhammad bin Nashr Al-Marwazi

~ Abu Hatim Ar-Razi

~ Abu Bakar bin Ishaq bin Khuzaimah

Da sauran su.

Rubuce-rubucensa/Littattafansa

[gyara sashe | gyara masomin]

Imam Bukhari ya rubuta littafai da dama a rayuwarsa. Aikinsa ba a fagen ilimin Hadisi kadai yake ba, har ma da sauran ilimomi kamar Tafsiri, fiqhu da kuma Tarihi (Tarikh).

Mafi shahararran littafin Imam Bukhari shine 'Al-Jami As-Sahih' wanda aka fi sani da Sahih Al-Bukhari.

Korar Imam Bukhari da gwamnan Bukhara yayi daga kasarsa ya haifar masa da radadi a cikinsa. Ya yi sauran kwanakinsa a Khartang, [[Samarkand. A ranar 1 ga watan Shawwal shekara ta 256 bayan hijira (870 miladiyya), Imamul Bukhari ya rasu yana da shekaru 62 a duniya a Khartang, Samarkand. Kabarin Imam Bukhari yana nan a birnin Khartang na Samarkand.

  1. "Encyclopædia Britannica". Archived from the original on 8 March 2021.
  2. Melchert, Christopher. "al-Bukhārī". Encyclopaedia of Islam. Brill Online.[permanent dead link]
  3. Bourgoin, Suzanne Michele; Byers, Paula Kay, eds. (1998). "Bukhari". Encyclopedia of World Biography (2nd ed.). Gale. p. 112. ISBN 9780787625436. Archived from the original on 20 May 2016. Retrieved 19 October 2015.
  4. https://www.islamicfinder.org/knowledge/biography/story-of-imam-bukhari/