Daular Abbasiyyah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Globe icon.svgDaular Abbasiyyah
الدولة العباسية (ar)
Black flag.svg

Suna saboda Abbasids (en) Fassara
Wuri
Abbasid Provinces ca 788.png

Babban birni Samarra (en) Fassara, Kufa, Bagdaza, Bagdaza da Kairo
Yawan mutane
Harshen gwamnati Larabci
Addini Musulunci
Labarin ƙasa
Yawan fili 6,800,000 km²
Bayanan tarihi
Mabiyi Umayyad Caliphate (en) Fassara
Wanda ya samar As-Saffah (en) Fassara
Ƙirƙira 7
Rushewa 1258 (Gregorian)
Followed by (en) Fassara Mamluk Sultanate (en) Fassara da Daular Usmaniyya
Tsarin Siyasa
Tsarin gwamnati theocracy (en) Fassara
• caliph (en) Fassara As-Saffah (en) Fassara (750)
Ikonomi
Kuɗi dinar (en) Fassara

Daular Abbasiyya, da turanci Abbasid Caliphate (IPAc-en|ə|ˈ|bæ|sɪd| or IPAc-en|ˈ|æ|bə|sɪd| Larabci ٱلْخِلافَةُ ٱلْعَبَّاسِيَّة, transl|ar|al-Khilāfatu al-ʿAbbāsiyyah) itace na uku daga cikin masarautar Kalifancin Musulunci dasuka gaji Manzo Muhammad tsira da amincin Allah sun tabbata agare shi. An samar da daular ce tun daga kawun manzon Allah, Abbas ɗan Abdul-Muttalib (566–653 CE), wanda daga sunansa ne daular ta samo suna Abbasiyya. Daular tayi mulkin Khalifanci ne a mafi yawan tsawon shekarun da tayi a matsayin Daular, Wanda ta kafa babban birninta a Bagadaza waddake kasar Iraq ayanzu, bayan samun nasara akan daular, sai Daular Umaydiyya a lokacin juyin juyahalin Abbasiyya a 750 CE

Daular Abbasiyya dafari ta sanya harkokin gwamnatin ta a Kufa, ayanzu kasar Iraq, amma a 762 sai Khalifa Al-Mansur yakafa garin Baghdad, kusa da tsohuwar garin Sasaniyan babban birnin kasan Ctesiphon. Lokacin zamanin Abbasiyyah ta dogara ne a Fasha ahalin Barmakid domin kula da harkokin biranen ta, da kuma sanya wasu daga musulmai wanda ba Larabawa ba a al'ummah (national community). wanda masu kudin lokacin suka dauka, daga suka fara taimakon Malamai da artists.[1] Baghdad tazama cibiyar kimiyya, al'adu, Falsafa da Kirkire kirkire inda yazamanto abinda akasani da Kyawawan shekarun Musulunci.

Dukda hadin kan da akasamu da farko, sai yan'Abbasiyyah na karshen Karni na 8, sunyi kawance da dukkanin Larabawa mawali[2] da kuma Iraniyawa.[3] An tilasta su bayar da mulki ga Al-Andalus da kuma Yammacin Afrika ga masarautar Umayya a 756, Morocco zuwa Idrisiyya a 788, Ifriqiya zuwa Aghlabiyya a 800 da Misra zuwa ga Yan Shi'ar Isma'iliyya khalifancin Fatimiyya a 969.

Karfin Siyasa na Kalifofinsu (Abbasiyya) ya karene da tasowa da samun karfin Iraniyawan Buyidiyya da kuma Daular Seljuq ta Turkiyya, wanda duk suka kwace Baghdad a 945 da 1055. Dukda mulkin Abbasiyya a mafi yawan Daulolin Musulunci yafara raguwa kadan kadan zuwa sai kawai lokacin yin addini kawai ake aiwatarwa, the dynasty tacigaba da rike kula da Mesopotamian domain. Zamanin Abbasiyya yakare ne a 1258 da kwace Bagadaza a hannun Mongoliyawa karkashin Hulagu Khan. The Abbasid line of rulers, da al'adar Musulunci gabar daya, duk sun sake shiga cikin Mamluk Babban birnin Alkahira a 1261. Dukda ta rasa karfin siyasa, amma dynasty ta cigaba da nuna karfin gudanar da addini har sai bayan Cin galaban Ottomaniyya akan Misra a shekarar 1517.

Anazarci[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. cite book|last1=Canfield|first1=Robert L.|title=Turko-Persia in Historical Perspective|date=2002|publisher=Cambridge University Press|isbn=9780521522915|page=5
  2. cite web|title = ABŪ MOSLEM ḴORĀSĀNĪ – Encyclopaedia Iranica|url = http://www.iranicaonline.org/articles/abu-moslem-abd-al-rahman-b%7Cwebsite = www.iranicaonline.org|accessdate = 2015-11-20|archive-url = https://web.archive.org/web/20151122132055/http://www.iranicaonline.org/articles/abu-moslem-abd-al-rahman-b#%7Carchive-date = 22 November 2015|dead-url = no|df = dmy-all
  3. cite book|title = The History of Government from the Earliest Times: Volume II: The Intermediate Ages p.720|url = https://books.google.com/books?id=AhEab85xHAMC%7Cpublisher = OUP Oxford|date = 1999-01-01|isbn = 9780198207900|first = S. E.|last = Finer