Jump to content

Juma'a

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Juma'a
day of the week (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na non-holiday (en) Fassara, rana da ranar hutu
Bangare na mako
Gajeren suna dv., Fr da Fri
Suna saboda Frigg (en) Fassara, Venus (goddess) (mul) Fassara, biyar, shida da Metal (en) Fassara
Mabiyi Alhamis
Ta biyo baya Asabar
Hashtag (mul) Fassara FridayFeeling da FridayMotivation
Code (en) Fassara C
Series ordinal (en) Fassara 5 da 6
NCI Thesaurus ID (en) Fassara C64966
sallah juma'a a Delhi a shekarar 1910

Juma'a (ko Jumma'a): rana ce daga cikin ranakun mako guda bakwai. Daga ita sai ranar Asabar gabaninta kuma akwai ranar alhamis. Ranar Juma'a dai musamman a ƙasashen musulunci ana kiranta da babbar rana ko karamar idi inda wasu ke kiranta da ranar idi, wannan yasa ake yin kwalliya, ziyara, yin abinci na musamman da shagulgula duk saboda mahimmancin wannan ranar saboda babban rana ce.

Ranar ne aka hallita Dan Adam.

Kuma ranan ce za ayi tashin alkiyama

Ranar Juma'a ta kasance wata babbar rana mai gwaɓi ga al'ummar Musulmi a duniya, wadda malamai da dama ke ayyana ta da tamkar Idi. Malamai na yawan kwaɗaitar da jama'a su zage dantse wajen yawaita ibada da addu'o'i a darenta da ranarta. To sai dai abin da ke shigar wa jama'a da dama duhu shi ne wace irin Ibadar ce ta fi kowacce a wannan rana domin samun babban lada. Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, shugaban hukumar Hizba a Kano kuma malamin addinin, a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce ibadar da ta fi kowacce a wannan rana ita ce salatin annabi. "A ranar Juma'a ya zama mafi yawan ibadar da za ka yi ita ce Salati ga manzon Allah. Haka ma a daren Juma'a ka ajiye duk wani abu kamar karatun Ƙur'ani da tasbihi da tahmidi da tahlili ka yi ta salatin annabi. Haka ma kuma a ranar Juma'a," in ji Sheikh Daurawa. Duk da dai Sheikh Daurawa bai faɗi adadin yawan salatin da ya kamata mutum ya yi ba amma ya nanata buƙatar yawaitar salatin a wannan rana mai albarka.[1]

  1. bbc