Madinah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
 masallacin Annabi
Masallacin Annabi (s.a.w) dake birnin madinah

Madinah Wani babban birni ne mai girman gaske dake yammacin Saudi Arabia a nahiyar Asiya cikin tsakiyar daular Larabawa shi dai wannan birni ya kafu ne tun dubban shekaru a baya tun a zamanin Annabawa. Hakika birnin Madinah birni ne na-gani-na-fada, Birni ne na Musulunci shine birnin manzon Allah Annabi Muhammad (s.a.w). Kafin zuwan Musulunci ana kiran birnin da suna Yathrib amma daga baya sai Annabi ya canjawa garin suna zuwa Madinah ko kuma Madinat Al-munawwarah a cikin birinin akwai wani babban masallaci wanda shine farkon Masallacin da Annabi ya gina a Madinah, wannan masallaci shine masallacin Quba


Fadin kasa

Birinin Madinah yana da fadin kasa kamar haka:

  • Fadin gari

589 km2 (227 sq mi)

  • Fadin babban birni

293 km2 (112 sq mi)

  • Maki mafi daukaka

608 m (1,995 ft)

  • kididdigar yawan mutane a shekarar (2010)

1,180,770

  • Density

2,000/km2 (5,200/sq mi)

 Taswirar birnin Madinah
Wannan taswirar Birnin Madinah kenan.

Hakika birnin Madinah yana matukar tasiri a Musulunci, shine garin Annabi (s.a.w) bayan hijararsa daga birnin Makkah acikin garin yayi rayuwa har Ajalinsa, sannan kuma acikin birinin aka rufe shi. Shi yasa duk Alhazan da suka je Madinah to sai sun kai ziyara kabarinsa (s.a.w) da manyan sahabbansa.