Wahayi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Hildegard von Bingen.jpg

A addinai da Ilimin Tauhidi (Theology), Wahayi shi ne bayyana da saukar da wasu labaran gaskiya ko Ilimi ta hanyar magana da Ubangiji ta hanyar dan sakonsa kamar mala'ika.

A addinin Musulinci, wahayi ya karkarsu daban-daban ta fuskar yanayin da aka karbeshi. Wani wahayin yana zuwa ta hanyar dan sako, kamar mala'ika, ko ta hanyar ruhi (wahyul ilhamiy) ko kuma ta hanyar wata alama. A Alkur'ani, Allah ya bayar da labarin cewa har wadanda ba Annabawa ba ana iya yi musu wahayi. Cikin wadanda suka samu wannan wahayin sun hada da tururuwa da kudan-zuma.