Addini

Daga Wikipedia
A tsallaka zuwa: Shawagi, nema

Addini (Ad-Deen, Ad-Diin ko Deen! (Arabic or Relgion.)) an samo kalmar daga harshen Larabci, tana nufin hanyar bauta, rayuwa ko kuma hanya kawai.

Addini shi ne hanyar rayuwa bisa bautar wani abun bautawa, bisa amfani da tsare-tsaren da wannan abin bautar ko kuma makusantansa suka tanadar domin tafi da rayuwar yau da kullum bisa wasu tanaje-tanaje ko tsare-tsare. Addini ya rabu gida daban-daban, kamar yadda masana addini su ka yi bincike kuma su ka tabbatar. A bisa wannan za a iya kasafta addini gida biyu, wato Addinan Kaɗaitaka (Monothiestic Religions) da kuma Addinan Tarayya (Polythiestic Religions).

Rabe-Raben Addinai:

1. Addinan Kaɗaitaka (Monothiestic Religions): Wadannan sune addinan da suka yarda da wanzuwar abin bauta guda ɗaya tilo, kuma suka tafi akan tabbatuwar wannan abin Bauta a matsayin wanda ya halicci rayuwa da duk abin da rayuwar ta tattara, Mutane, Aljannu, Dabbobi, Tsirrai, Sararin Sammai, Sararin Kassai, Ruwa, Iska da makamantansu.

Addinan da suke a cikin wannan kason sun hadar da:

Addinin Musulunci (Islam) Addinin Kiristanci (Christianity) Addinin Yahudanci (Judaism) Addinin Zarusta (Zoroastorianism)

Littatafai:

Wadannan addinai su na da littatafai da suke ƙunshe da hukunce-hukuncen tafiyar da rayuwar jama'a bisa tsari da tsafta da kuma jagoranci. Ubangiji shi ya saukarwa bayinSa littatafan, ta hanyar Mala'ikunSa zuwa ga ManzanninSa domin suyi gargadi da kuma jagoranci bisa hanyarSa.

Addinai da Littatafansu:

-Addinin Yahudanci (Judaism) an saukar masa da littafi Zabura (Zaboor (Old Testament)) ta hannun Annabi Musa (Moses).

-Addinin Kiristanci (Christianity) an saukar masa da littafin Injila (Injeel (New Testament)) ta hannun Isa Ɗan Maryama (Jesus Christ).

-Addinin Musulunci (Islam) an saukar masa da Ƙur'ani Mai Girma (Noble Qur'an (Koran)) ta hannun Annabi Muhammad "Sallallaahu Alaihi Wasallam" (Mohamed, Mohammed).

2. Addinan Tarayya (Polythiestic Religiona): Wannan nau'in addinai sune addinan da basu yadda da bautar Allah ba, mafi yawancinsu su na bautar gumaka ne ko kuma halittu daban-daban kamar Saniya, Macijiya, Birai, Tumaki da sauransu. Wasu kuma su na bautar halittu ne kamar su Rana, Iska, Ruwa, Duwatsu da sauran su.

Ire-iren waɗannan addinai sun yarda da gabatar da hadaya ga ababan bautarsu, kuma basu da wasu tsayayyun dokokin rayuwa ko littatafai da ke dauke da hukunce-hukunce da tsare-tsaren tafiyar da rayuwar yau da kullum, saɓanin addinan kaɗaitaka.

Addinan da suke cikin wannan kason sune:

Addinin Buddah (Buddhism) Addinin Hindu (Hinduism) Addinin Aztec (Aztec) Addinin Majusanci. Da Sauransu.

Wallafar Abdullahi Faisal Kano, @IsmaAbdulF

Wikimedia Commons on Addini