Larabci
Larabci | |
---|---|
اللُّغَة العَرَبِيّة | |
'Yan asalin magana |
harshen asali: 295,000,000 (2010) sum (en) : 315,421,300 (2019) 422,000,000 (2012) |
| |
Arabic script (en) | |
Lamban rijistar harshe | |
ISO 639-1 |
ar |
ISO 639-2 |
ara |
ISO 639-3 |
ara |
Glottolog |
arab1395 [1] |
Harshen Larabci, shine harshen da mutane Larabawa ke magana da shi. Da Arabic ko
kuma muce larabci a harshen Hausa,yare ne wanda ya fito daga iyalin yarurruka na AfroAsiya Kuma yare ne wanda ake amfani da shi a yankin gabas ta tsakiya da kuma wasu sassa na kudancin da gabashin nahiyar Afrika dama wasu ɓangarori na nahiyar Turai.
Yawan mutanen da suke amfani da harshen larabci ya kai Miliyan Dari Biyu Da Chasa'in (290m).
Harshen Larabci
[gyara sashe | gyara masomin]Muhimmancin Larabci a wurin Musulmai
[gyara sashe | gyara masomin]Akasarin musulmai masu wani harshe daban suna amfani da harshen larabci sabo da shi ne harshen da ya zama na addinin musulunci. Da harshen larabci ne aka saukar da Alkur'ani, sannan kuma da harshen larabci ne aka rubuta manya-manyan litattafai na Addinin musulunci.
Bayan Litattafan Addinin musulunci kuma, akwai ɗimbin litattafai da aka rubuta su a cikin harshen na larabci.
Ƙasashen da ake amfani da harshen larabci a matsayin harshen ƙasa
- Masar
- Aljeriya
- Sudan
- Iraki
- Maroko
- Saudiyya
- Yemen
- Siriya
- Tunisiya
- Somaliya
- Jodan
- Hadaddiyar Daular Larabawa
- Libya
- Falasdinu
- Lebanon
- Oman
- Kuwait
- Muritaniya
- Qatar
- Baharain
- Jibuti
- Komoros
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Larabci". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.