Falasdinu
| Wuri | |||||
|---|---|---|---|---|---|
| |||||
| Labarin ƙasa | |||||
| Bangare na | Southern Levant (en) | ||||
| Bayanan Tuntuɓa | |||||
| Kasancewa a yanki na lokaci | |||||



Falasdinu (Turanci Palestine), (Larabci فلسطين) دولةفلسطين Daular Falastin ƙasa ce da ake rigima a kanta a nahiyar Asiya. Ƙasar na ikirarin mallakar yankin gabar tekun yammacin ta kwato (iyaka da ƙasar Isra'ila da Jordan) sai kuma yankin Gaza (iyaka da Israila da Masar) da kuma gabashin birnin Jerusalem wanda shi ne ƙasar take dauka a matsayin babban birnin ta, duk da yake kuma a birnin Ramallah ne ake tafiyar da mafi yawan aiyukan gwamnati. Mafi yawancin yankunan ƙasar Falasɗinu na karkashin Yahudawan Israila 'yan kama guri zauna da suka kwace tun daga shekarar 1967. Yawan mutanen asar ya kai 4,560,368 ƙidayar shekarar 2014, ita ce ƙasa ta 123 a yawan jama'a a duniya.
Bayan kammala yakin duniya na biyu a 1947, Majalisar dinkin duniya ta yi kokarin kafa ƙasar ta Falasɗinu wadda ta kumshi Larabawa Musulmai, da kuma Yahudawa da ƙasar su ta Israila a shekara ta 1948. Bayan kafa ƙasar ta Falasɗinu ne sai larabawa Musulmai suka dauki makamai domin nuna adawa da yin hakan tare da yakar Yahudawa.
Tun daga nan yankin ya yi ta cigaba tare da canza salo kala-kala har zuwa ranar 15 Nuwamba, a shekarar 1988, inda shugaban Falsdinawa Yaseer Arafat, ya ayyana kafa ƙasar ta Falasdinu a birnin [[Aljas]] na ƙasar AljeriyaShekara daya kuma bayan sa hannun kan yarjejeniyar Osla Accords a shekara ta 1993 gwamnati ta kafu a ƙasar Falsɗinu.
Ƙasashe guda 136 daga cikin mambobi a majalisar ɗinkin duniya ne suka amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa. Ƙasar har yanzu ba mamba ba ce ba a Majalisar dinkin Duniya, amma kuma mamba ce a ƙungiyar ƙasashen larabawa wato G77, da kuma Hukumar wasanni ta Olympic da sauran manyan ƙungiyoyin duniya.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]| Asiya | |||
|
Kazakystan • Kyrgystan • Tajikistan • Turkmenistan • Uzbekistan |
Sin • Japan • Mangolia • Koriya ta Arewa • Koriya ta Kudu • Jamhuriyar Sin | ||
| Armeniya • Azerbaijan • Baharain • Georgia • Irak • Isra'ila • Jordan • Kuwait • Lebanon • Oman • Qatar • Saudiyya • Siriya • Turkiya • Taraiyar larabawa • Falasdinu • Yemen | Brunei • Kambodiya • Indonesiya • Laos • Maleshiya • Myanmar • Filipin • Singafora • Thailand • Timor-Leste • Vietnam | ||
| Afghanistan • Bangladash • Bhutan • Indiya • Iran • Maldives • Nepal • Pakistan • Sri Lanka | |||
