Jump to content

Yammacin Asiya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yammacin Asiya
yankin taswira da subcontinent (en) Fassara
Bayanai
Bangare naAsiya
NahiyaAsiya
Territory overlaps (en) FassaraGabas ta tsakiya
Sun raba iyaka daTsakiyar Asiya da South Asia (en) Fassara
Wuri
Map
 29°10′00″N 47°36′00″E / 29.166667°N 47.6°E / 29.166667; 47.6
TASBIRAN Yammacin Asiya
Yammacin Asiya

Yammacin Asiya, Asiya ta Yamma,Kudu maso Yamma da Asiya shi ne yankin yammaci na nahiyar Asiya. Ana takaitawa ace yammacin Asiya, ammah ana iya faɗaɗawa wajen fadin Gabas ta Tsakiya, anan kuma akan haɗa ne harda dukkannin yankunan ƙasar Misira da kuma yankin Turkiyya Turai.

Adadin yawan mutane a yankin yammacin Asiya an kiyasta zai kai miliyan 300 a ƙiyasin da akayi na shekarar 2015.[1]

Taswiras yammacin Asiya

A farkon ƙarni na 19 ana amfani da Kalmar yammacin asiya ne wajen bambancewa tsakanin yanayin muhallai na nahiyar Asiya da kuma bambance tsakanin iyakoki na ƙasashen da suka shafi yankin. Ammah dai dukda haka ana daukar yankin a matsayin wani bamgare na nahiyar Asiya.[2].

Tattalin Arziƙi

[gyara sashe | gyara masomin]

Yanayin hanyoyin samun tattalin arziƙi a yammacin Asiya ya bambanta,ammah ana samun saurin habakar tattalin arziƙi kwarai a yankin.ƙasar Turkiyya ce kan gaba wajen ƙarfin tattalin arziki a yammacin Asiya sai kasar Saudiyya ke biye da ita a matsayin ta biyu da kuma kasar Iran.Man fetur shine babban tattalin arziki a yankin, India Samar da rabin man fetur da duniya me da shi yake a yankin, sannan kuma kashi 40% na iskar gas ta duniya ma na a yankin.[3].

Kasashen yammacin Asiya sune;

Sannan kuma akan kara da Misira.

Dajin Cedar a Lebanon.
Taswira mai nuna yanayin muhalli a yankin Yammacin Asiya

Ƙidayar jumullar mutane a yankin yammacin Asiya ya kai miliyan 272 a shekarar 2008, akwai hasahen adadin ka iya kaiwa miliyan 370 zuwa shekarar 2030 a wani kiyasi na Maddison (kididdigar ta hada da yankin Caucus da kuma kasar Cyprus. Wannan ya ƙunshi karin hauhawar haihuwar mutane Akan kaso 1.4% a shekara shekara.

Mutane a yammacin Asiya sunkai kaso 4% na mutanen Duniya, sun fara ne daga miliyan 39 a farkon ƙarin na 20, ko a kalla kaso 2% na mutanen duniya.[4]

Kasa mafi yawan jama'a a yankin yammacin Asiya itace kasar Turkiyya sai kuma Iran, wadanda dukkansu mutanen su sun kai miliyan 79, masu biye masu ta fuskar yawan jama'a kuma sune kasashen Saudi Arebiya da Iraƙi masu adadin mutane sama da miliyan 33.

Larabawa dai aka fi sani a yankin yammacin Asiya, sai kuma Farisawa, Turkawa, sannan harsunan yankin sune Larabci, Farisa, Turkanci, wadanda kowanne nada masu amfani da su Sama da mutane miliyan 70, akwai wasu kananan ƙabilu wadanda suka hada da Kurdawa, Azabaijawa, Yahudawa. Sauran kabilu marasa rinjaye sun hada da Assiriyawa, Chaldiyawa, Druze, Mandawa, Maronitawa, Shabakawa, Lur da Yazidawa.