Turai, Ko kuma Yurof (da Turanci, Europe). Yurof nahiya ce, kuma an santa da wani bangare na Yureshiya, daukacinta tana arewacin Hemisfira kuma kusan duka a cikin Gabashin Hemisfira.Ta kunshi mafiyammacin feninsulolin Yureshiya [1] tana raba Landmass na nahiya ta Afro-Yureshiya da duka Asiya da Afirka.Ta yi iyaka da Tekun Aktic daga arewa, da tekun Atalantika daga yamma, da Tekun Meditaraniya daga kudu da kuma Asiya daga gabas. Yawanci ana daukar Yurofa a matsaya cirarra daga Asiya ta dalilin watershed na tsaunukan Ural, da Rafin Ural, da Tekun Kasfiyan, da Greater Caucasus, da Bakin Teku da kuma hanyoyin ruwan Turkish Straits.[2] ko da yake mafi yawancin iyakar kan kasa ta ke, Kusan ko da yaushe dai ita Yurofa ana ganinta a matsayin Nahiya mai zaman kanta saboda girmanta da kuma nauyin tarihinta da tsiburinta.
↑National Geographic Atlas of the World (7th ed.). Washington, DC: National Geographic. 1999. ISBN978-0-7922-7528-2. "Europe" (pp. 68–69); "Asia" (pp. 90–91): "A commonly accepted division between Asia and Europe ... is formed by the Ural Mountains, Ural River, Caspian Sea, Caucasus Mountains, and the Black Sea with its outlets, the Bosporus and Dardanelles."