Poland

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Flag of Poland.svg
Herb Polski.svg

A zamanin da kabilai iri-iri sun yi yawa a cikin ƙasar Poland, kamar su Pomorzanie, da Polanie, da Wiślanie, da Goplanie, da Mazowszanie da sauransu. Duk mutanen nan suna jin harshe ɗaya, kuma al’adunsu da sana’o’insu sun yi kama da juna, amma su a rarrabe suke, sai suna yaƙi da juna. Su arna ne, sabo da haka wata kabila ta yamma kullum faɗa take yi da ƙasar Jamus, inda duk mutane Kiristoci ne. Ana nan sai wani sarki mai suna Mieszko ya yanke shawara a haɗa duk kabilai. Da farko ya mallaki kabilan Polanie, sabo da haka sunan ƙasarmu Poland ne. Bayan ya haɗa kabilai, ya zama shugaban ƙasa, kuma ya zama asalin iyalin sarakuna na ƙasar Poland mai suna PIASTOWIE.

Mieszko I (960-992) yana so ya zama lafiya da sarkin Jamus – Otto I, sabo da haka ya karɓi addinin Kirista a shekara ta 966. Daga wannan lokaci Poland ta zama ƙasar Kirista ne. Lokacin da ya yi yaƙi da ƙasar Czech, ya auri ’yar ƙasar Czech – Dobrawa, wadda ta haifa masa ɗa namiji. Sunansa Bolesław Chrobry (992-1025) wanda ya hau gadon sarautar ƙasar Poland. Ana cewa ya fi ubansa ƙarfi, ya sha yaƙi don ƙara ƙasa. A shekara 1018 ya ci nasara da Jamus, wadda ita ce ƙasar mafi girma a Turai a zamanin nan. Bolesław Krzywousty (1102-1138): Ana cewa wai wannan sarki mayaki shahararren ne, amma ba shi da hankali. Yana da yaya da yawa. Ba ya son su yi yaki da juna bayan mutuwarsa, sabo da haka ya rarraba kasar don kowane da ya sami yankinsa. Kasar Poland ta rasa karfi. Bayan an yi shekaru dari da hamsin wani sarki mai suna Kazimierz Wielki ya sake hada kasa. Kazimierz III Wielki (1333-1370), wato „Kazimierz Mai Girma”, ya yi matukar kokari don gyara kasarsa. Akwai wani kirari na sarkin nan wanda ake cewa „an haife shi a kasar mai gine-gina na itace, sai ya mutu a kasar mai gine-gine na dutse”. Ya sa an gina gine-gine na zamani. A zamaninsa ilmi da hikima suka karu, har ya kafa jami’ar Cracow, wadda ita ce daya daga cikin jami’o’i na farko a Turai. An kuma gina coci da yawa, aka gina ganuwar gari. Ya sa kasa ta zama mai karfi, mai muhimmanci. Kazimierz Wielki yana da mata hudu, amma bai sami da namiji, sai ’yan mata.

Iyali mai suna PIASTOWIE ya yi mulki wajen shekaru ɗari huɗu, har zuwa shekara ta 1370 bayan haihuwar Annaba Isa. Can an yi sarakuna mai girma, waɗanda suka ƙara faɗin ƙasa, kuma sun kula da addinin Kirista. Garuruwa da suka fi muhimmanci a wancan zamani, su ne Gniezno, wato gari mafi muhimmanci game da addinin Kirista, da Cracow, wato babban garin ƙasar. Bayan haka wani sabon iyali mai suna JAGIELLONOWIE ya sami mulki. A lokacin mulkinsu Poland ta zama ƙaton ƙasa mai ƙarfi, sabo da ta haɗa da ƙasar Lithuania. Amma sarakuna daga cikin wannan iyali ba su yi yawa ba, sai guda bakwai. Zygmunt II August, sarki na ƙarshe daga cikinsu ba shi da ɗa ko ɗaya, sabo da haka bayan mutuwarsa a shekara ta 1573, mutane masu kuɗi suka sami sarakuna daga wasu ƙasashe dabam na Turai. Daga wajen shekara 1600 kasar Poland ta yi yaki da makwabtanta – kasar Turkiya, Rasha da Ukraine. Yakin da ya fi muhimmanci shi ne yaki da kasar Sweden. Kasar Poland ta ci nasara amma duk yakin nan sun dami mutane, sun bata kasar an kashe kudin baitulmal. Daga wannan lokaci, ƙarfin sarki ya fara ragewa, kuma wahaloli iri-iri na siyasa suka ɓullo.

Sarki na karshe shi ne Stanisław August Poniatowski (1764-1795). A zamaninsa ilmi ya karu. A shekara 1793 an gina sannaniyar fada cikin garin Warsaw, wadda ake kira Łazienki Królewskie. Mutane daga kasahen daban-daban suna zuwa Warszawa don kallon Łazienki Królewskie. Sarkin nan ya lura da mawaka da ‘yan kade kade da masu fasaha. An kafa ma’aikata mai kula da makarantu. A wannan lokaci makwabtan kasar Poland kamar Rasha, Jamus da Austria sun kara karfi. Nufinsu ma shi ne a kwace kasar Poland, kowace daga cikinsu tana son daukar bangarenta. A shekara 1795 sun ci kasar Poland, kasar Poland ta rasa mulki, an zama yin mulkin mallaka a ƙasar. Mutanen kasar Poland sun sha wuya, sabo da wadannan kasashen ba sa yi masu alheri. An hana yin magana a harshen Poland, kuma an hana koyar da tarihin kasar Poland. Mutanen kasar Poland sun yi kokari su sami yanci. Sun yi yakoki da dama, inda mutane da yawa suka mutu. Bayan wahalce-wahalcen da suka dade daidai shekara dari daya da ashirin da uku, kasar Poland ta sake samun yanci. Shugaban da ya shawara da karfi kuma da wayo sunansa Józef Pilsudski. Shi da alkawaransa sun sami yanci ranar 11 Nuwamba 1918, sabo da haka wanann rana ta zama bikin samun ’yanci.