Nahiya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Afirka da Antarctica da Asiya da Austaraliya da Turai da kudancin Amirka da kuma Amirka ta Arewa


Nahiya na nufin sashe-sashe ko kuma manya-manyan shigifun da'irar shimfiɗaɗɗiyar ƙasa da ake da su a wannan duniya tamu. Babu dai wata ƙididdiga da ta tabbatar da adadin nahiyoyin da ake da su a duniya bakiɗaya, sai dai kawai ana ganin ko dai guda shida ne ko kuma guda bakwai.

Amma dai abin da aka fi haƙƙaƙewa akai shi ne, waɗannan nahiyoyi guda Bakwai ne. Kuma sun haɗar da Afirka da Antarctica da Asiya da Austaraliya da Turai da kudancin Amirka da kuma Arewacin Amirka. Wannan a yadda aka karantar da ɗalibai kenan a yankin nahiyar Amirka bakiɗaya.

Amma kuma a yankin nahiyar Turai da kuma sauran sassan duniya, mafi yawan ɗaliban yankunan ana karantar da su cewar, nahiyoyi Shida rak ake da su a duniyar nan. Ma'ana a waɗannan yankuna ana duban Kudancin Amirka da kuma Arewacin Amirka a matsayin nahiya guda ɗaya ta Amirka. Anan lissafin nahiyoyi shidan kenan ya haɗar da Afirka da Amirka da Antarctica da Asiya da Australiya da kuma Turai.

To sai dai a halin da ake ciki kuma, mafiya yawan masana ta fuskar kimiyya na duban waɗannan nahiyoyi Shida da cewar nahiyar Turai da ta Asiya a dunƙule suke wuri ɗaya a matsayin nahiya guda, don haka ne ma suke kiran nahiyar da suna Eurasiya, sai kuma Afirka da Antarctica da Austaraliya da Kudancin Amirka da kuma Arewacin Amirka.

Masana ilimin taswirar duniya, su kuma a halin yanzu sun kasafta duniyar nan zuwa yankuna takwas domin samun sauƙin fahimta. Yanki na farko dai shi ne na Asiya, wanda ya ƙunshi Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka. Sai kuma Turai da Arewacin Amirka. Akwai kuma Tsakiyar Amirka da yankin Carribbean. Kana ga Kudancin Amirka da Afirka da Austaraliya da kuma Yankin Teku, wato Oceania kenan.

Wannan dai shi ne taƙaitaccen bayani game da ma'anar nahiya ta fuskoki daban-daban

Nahiya is a village in betul district of madhya pradesh in India.

it has a population of 25000

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

Wannan ƙasida guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.