Jump to content

Armeniya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Armeniya
Հայաստան (hy)
Հայաստանի Հանրապետություն (hy)
Flag of Armenia (en) Coat of arms of Armenia (en)
Flag of Armenia (en) Fassara Coat of arms of Armenia (en) Fassara


Take Mer Hayrenik (en) Fassara

Wuri
Map
 40°23′00″N 44°57′00″E / 40.38333°N 44.95°E / 40.38333; 44.95

Babban birni Yerevan
Yawan mutane
Faɗi 2,930,450 (2017)
• Yawan mutane 98.52 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Armenian (en) Fassara
Addini Kiristanci
Labarin ƙasa
Bangare na Yammacin Asiya da Gabashin Turai
Yawan fili 29,743.423459 km²
Wuri mafi tsayi Mount Aragats (en) Fassara (4,090 m)
Wuri mafi ƙasa Debed (en) Fassara (400 m)
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Kungiyar Sobiyet
Ƙirƙira 23 Satumba 1991
Tsarin Siyasa
Tsarin gwamnati jamhuriya, unitary state (en) Fassara da parliamentary system (en) Fassara
Majalisar zartarwa Government of Armenia (en) Fassara
Gangar majalisa National Assembly of Armenia (en) Fassara
• President of Armenia (en) Fassara Vahagn Khachatryan (en) Fassara (13 ga Maris, 2022)
• Prime Minister of Armenia (en) Fassara Nikol Pashinyan (en) Fassara (8 Mayu 2018)
Ikonomi
Nominal GDP (en) Fassara 13,861,409,969 $ (2021)
Kuɗi Armenian dram (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
UTC+04:00 (en) Fassara
Suna ta yanar gizo .am (en) Fassara da .հայ (en) Fassara
Tsarin lamba ta kiran tarho +374
Lambar taimakon gaggawa *#06#, 101 (en) Fassara, 102 (en) Fassara da 103 (en) Fassara
Lambar ƙasa AM
Wasu abun

Yanar gizo gov.am…
Twitter: armenia Edit the value on Wikidata
Wani Gini Mai tarihi a Armaniay a yamacin turai
murnar samun 'yanci a (1920) Armeniya

Armeniya Armeniya, a hukumance jamhuriyar Armeniya, ƙasa ce a yammacin nahiyar Asiya da Turai. Tana iyaka da Turkiyya daga yamma, Georgia daga arewa, da kuma Lachin corridor (karkashin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Rasha) tare da Azarbaijan daga gabas, sai Iran da Azarbaijan da ke yankin Nakhchivan daga kudu. Yerevan shine babban birnin kasar kuma birni mafi yawan jama'a.[1]

Armeniya ƙasa ce da ta ginu a tsarin mulki na bai ɗaya, tana da jam'iyyu da yawa, ana kuma gudanar mulkin demokraɗiyya a cikinta, tana da daɗaɗɗun al'adun gargajiya. An kafa ƙasar Armeniya ta farko Urartu a shekara ta 860 BC, kuma a ƙarni na 6 BC ta maye gurbinta da Satrapy na Armeniya. Masarautar Armeniya ta yi ƙarfi ne a ƙarƙashin Tigranes the Great a karni na 1 BC kuma a shekara ta 301 ta zama kasa ta farko a duniya da ta ɗauki addinin Kiristanci a matsayin addininta na hukuma farkon karni na 5.[2]


Fasalin ƙasa[gyara sashe | gyara masomin]

Armeniya tana da yanki mai faɗin kilomita 29,743 (sq mi 11,484). Ƙasar galibi tana da tsaunuka, tare da koguna masu guduna, da dazuzzuka kaɗan. Ƙasar ta haura zuwa mita 4,090 (ƙafa 13,419) sama da matakin teku a Mount Aragats, kuma babu wani wuri da yake ƙasa da mita 390 (1,280 ft) sama da matakin teku. Matsakaicin girman yankin ƙasar shine na goma mafi girma a duniya kuma tana da yanki masu tsaunuka akalla kaso 85.9%, fiye da Switzerland ko Nepal. Mount Ararat, wanda a tarihi ya kasance a cikin yankin kasar Armeniya, shine tsauni mafi tsayi a yankin mai tsayin mita 5,137 (ƙafa 16,854). A yanzu kuwa yana cikin yankin ƙasar Turkiyya ne, amma kuma bayyane yake a na ganinsa sosai daga Armeniya, Armeniyawa suna ɗaukarsa a matsayin alamar ƙasarsu dalilin kenan da yasa suka saka hoton tsaunin a cikin alamar ƙasar Armeniya har zuwa yau.

Mulki da Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Armeniya jamhuriya ce ta demokraɗiyya mai majalisa. Kundin tsarin mulkin Armeniya ya zamo tsarin tafi da mulkin shugabancin jamhuriyar kan gaba har zuwa watan Afrilun 2018.

Bisa kundin tsarin mulkin Armeniya na yanzu, shugaban kasa shi ne wanda ke rike da manyan ayyuka na wakilci, yayin da firaministan kuma shi ne shugaban gwamnati kuma yake gudanar da harkokin zartaswa. Ƙarfin doka yana hannun Azgayin Zhoghov ko Majalisar Dokoki ta ƙasa, wadda ita ce majalisa marar rinjaye.

Larduna[gyara sashe | gyara masomin]

An raba Armeniya zuwa larduna goma, su ne;


Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Human Development Report" (PDF). United Nations Development Programme (UNDP). 2019. Archived (PDF) from the original on 16 July 2020. Retrieved 27 July 2020.
  2. "Armenian cave yields what may be world's oldest leather shoe". CNN. 9 June 2010. Archived from the original on 28 January 2018. Retrieved 28 January 2018.
Asiya    

Kasashen tsakiyar Asiya l

KazakystanKyrgystanTajikistanTurkmenistanUzbekistan

Gabashin Asiya

SinJapanMangoliaKoriya ta ArewaKoriya ta KuduJamhuriyar Sin

Yammacin Asiya

ArmeniyaAzerbaijanBaharainGeorgiaIrakIsra'ilaJordanKuwaitLebanonOmanQatarSaudiyyaSiriyaTurkiyaTaraiyar larabawaFalasdinuYemen

Kudu maso gabashin Asiya

BruneiKambodiyaIndonesiyaLaosMaleshiyaMyanmarFilipinSingaforaThailandTimor-LesteVietnam

Tsakiya da kudancin Asiya

AfghanistanBangladashBhutanIndiyaIranMaldivesNepalPakistanSri Lanka

Arewacin Asiya

Rasha

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.