Misra
Misra | |||||
---|---|---|---|---|---|
جُمهورِيّةُ مِصرَ العَرَبيّةِ (ar) مصر (ar) Arab Republic of Egypt (en) Egypt (en) Republik Arab Mesir (ms) Mesir (ms) | |||||
|
|||||
| |||||
Take | Bilady, Bilady, Bilady (en) | ||||
| |||||
| |||||
Kirari | «مصر أمّ الدنيا» | ||||
Suna saboda | Ptah (en) da Mizraim (en) | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Babban birni | Kairo | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 94,798,827 (2017) | ||||
• Yawan mutane | 93.82 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Larabci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Bangare na | Arewacin Afirka, Gabas ta tsakiya da Yammacin Asiya | ||||
Yawan fili | 1,010,407.87 km² | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Bahar Rum, Nil da Red Sea | ||||
Wuri mafi tsayi | Mount Catherine (en) (2,629 m) | ||||
Wuri mafi ƙasa | Qattara Depression (en) (−133 m) | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Kingdom of Egypt (en) da All-Palestine Government (en) | ||||
Ƙirƙira | 28 ga Faburairu, 1922: Kingdom of Egypt (en) | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Tsarin gwamnati | jamhuriya | ||||
Majalisar zartarwa | Cabinet of Egypt (en) | ||||
Gangar majalisa | Parliament of Egypt (en) | ||||
• Shugaban kasar Egypt | Abdul Fatah el-Sisi (8 ga Yuni, 2014) | ||||
• Prime Minister of Egypt (en) | Mostafa Madbouly (en) (14 ga Yuni, 2018) | ||||
Majalisar shariar ƙoli | Supreme Constitutional Court of Egypt (en) | ||||
Ikonomi | |||||
Nominal GDP (en) | 424,671,765,456 $ (2021) | ||||
Kuɗi | Fam na Masar | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Suna ta yanar gizo | .eg (mul) da .مصر (mul) | ||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | +20 | ||||
Lambar taimakon gaggawa | 122 (en) , 123 (en) da 180 (en) | ||||
Lambar ƙasa | EG |
Kasar Misra, ko Masar tana kudu maso, gabashin Afrika, kuma tana kudu maso yammacin Asiya [1] daya daga cikin muhimman siffofin da take takama da su shi ne na kasancewa ta a kan mararraba, ta kusa da nahiyar Turai. Sannan kuma tana matsayin kasar da ta kasance mashiga tsakanin Afirka da nahiyar Asiya. Har ila yau kuma, ita ce kuma ta hada hanyar safara ta cikin ruwa, tsakanin tekun Mediterrenean da tekun Indiya ta hanyar Bahar Maliya.
Dalar Giza da ke birnin Al-kahirar Kasar. Misra ko kasar Masar dai ta kasance kasa mafi yawan al'umma a cikin dukkanin kasashen Larabawa, kuma babban birninta wato birnin Al'kahira shi ne birni mafi girma a nahiyar Afirka tun karnoni da dama da suka gabata. Sannan kuma har ila yau, ga ta a karshen kogin nilu, wanda shi ne kogi mafi girma a duniya. Saboda haka, idan aka yi la'akari da wadannan dalilai na tarihi, to za a iya fahimtar dalilin da ya sa matsayin kasar Misra yake da ƴar rikitarwa.
Su ma kansu Misirawan a tsakanin su, sukan kasance cikin rudani a game da batun nahiyar da ya kamata su yi tutiya da ita a matsayin nahiyarsu. Ga su dai a cikin kwazazzabon nilu, da mediterenean, da Sahara, har ila yau kuma ga su cikin duniyar Musulmai, dukkan wadannan siffofi, siffofi ne da kuma ba kasafai ya kamata a ce wata kasa guda daya ta hada su ba. To, sai dai duk da haka za a iya cewa, mafi yawan fadin kasar yana bangaren nahiyar Afirka ne. To, amma fa duk da haka ana kallon garuruwan da suke lardin Sinai na kasar Misiran a matsayin bangaren nahiyar Asiya, kasancewar su, suna yankin gabashin kasar ne.
Kogin Nilu wanda shi ne kogi mafi girma a duniya. A zamanin da can, dangantakar Misra da kasashen da ke Afirka na da matukar karfi. To amma tun lokacin da Siriyawa da ke karkashin daular Rumawa suka mamaye Misira, a karni na bakwai kafin zuwan Annabi Isa Alaihissalam, sai Misira ta fuskanta zuwa ga Yankin Gabas ta Tsakiya, ta fuskar harkokin al'adunta, da na addininta da na siyasarta da kuma na tattalin arzikinta. Kuma mafiya yawan Misirawa suna danganta kansu ne da Larabawa kuma ƴan Yankin Gabas ta Tsakiya. Har ila yau, kuma wasu da yawa daga cikinsu, kusan ace wadanda suke su ne 'yan asalin kasar ta Misira, waɗanda kuma aka fi sani da Nubiyawa, suna danganta kansu ne da Afirka. Hasali ma suna ikirarin su jinin Afirka ne.
Babu shakka dai idan aka bi salsala ta tarihi, shekaru kimanin 200 da suka gabata, Misra tana da alaka mai karfi da kasashe irin su Sudan da Habasha da Libya da ma wasu kasashe da dama na nahiyar ta Afirka. Kuma ba tare da wani kokwanto ba, Misra za ta cigaba da cin tudu biyu, a matsayinta na ruwa-biyu, wato ga ta dai 'yar Afirka, kuma 'yar yankin Gabas ta Tsakiya, yana daga cikin tarihin Misira kasancewarta
gari na farko a tarihi da sheɗan da kansa ya bayyana ga azzalumin sarki Fir' auna a lokacin da Fir'auna ya ce shi Ubangiji ne.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Kasar na da matukar tarihin gaske a yankin Afirka da duniya gabaki daya
-
Gidan tarihi da ke Cairo babban birnin kasar
-
Wani tsohon hoto
Al'adu
[gyara sashe | gyara masomin]Abinci
[gyara sashe | gyara masomin]-
Hatsi daga kasar Misra
Tufafi
[gyara sashe | gyara masomin]Yarika
[gyara sashe | gyara masomin]Mulki
[gyara sashe | gyara masomin]
Kasan misra tana da karfin mulki.
-
Jana'izar Hosni Mubarak
-
Hosni tare da Obama
-
Hosni Mubarak
-
Taro a kasar Misra
Sufuri
[gyara sashe | gyara masomin]Arziki
[gyara sashe | gyara masomin]Noma
[gyara sashe | gyara masomin]Kasar Misra na da dabino da furanni daban-daban.
-
Dabino
-
Fure
-
Farin Fure
-
Fure mai launika iri iri
Kiwon lafiya
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai asibitoci da'ake kula da marasa lafiya
-
Wasu mata sun saka takunkumin hanci Don samun kariya ga cutar "Covid 19"
Wasanni
[gyara sashe | gyara masomin]Addini
[gyara sashe | gyara masomin]Musulunci
[gyara sashe | gyara masomin]-
Masallaci a Misra
-
Haraba
Kiristanci
[gyara sashe | gyara masomin]Tsaro
[gyara sashe | gyara masomin]Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]-
Sabon babban birnin gudanarwa
-
Coat of Arms
-
Tutar kasar
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]
Ƙasashen Afirka |
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe |