Jump to content

Rumawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Daular Rumawa wadda a turance ake kira da “Rome” wani ci gaba ne da ya fara bayan wasu kauyuka na kabilun Latin da suka kafu a bakin kogin Tiber (Tiber river ) daga bisani suka hade guri guda inda suka zama birnin Rum a wajejen shekara ta 700 bayan annabi isa al-Masihu. Wanda wannan ne kuma ya kafa tushen kasantuwar Daular Rum.

Masana tarihi sun tabbatar da cewa Daular Rumawa ce mafi girma da kasaita a tsakanin sauran Dauloli da aka samu a zamanin baya. Saboda a lokacin kasaitar ta, Daular Rum ta mallaki babban fadin kasa wanda ya hada da kusan gaba dayan nahiyar Turai (Europe ), yammacin nahiyar Asia, da kuma daukacin arewacin Africa. Haka kuma, tarihi ya nuna cewa Daular Rumawa ta bar wasu muhimman abubuwa wanda duniyar yanzu take cin gajiyar su.

Ababen da Rumawa Suka Bari[gyara sashe | gyara masomin]

Manya manyan abubuwa wanda daular Rumawa suka bari wadanda baza adaina amfani dasu ba sune kamar haka

  1. tsarin mulkin na wakilci
  2. haruffan turanci
  3. dakarun yaƙi

samar da tsarin dimokaradiyya na wakilci wato “representative democracy”. Wannan shine tsarin mulki Wanda mutane ke tura wakilansu domin zartar da wasu abubuwa wadanda suka shafe su.

Amma Babban abin da aka sanin Daular Rumawa da shahara da shi, shine karfin mayaka da dogewa da izzar yaki. Domin kuwa mayakan Rumawa sun kasance marasa tsoro wanda suka sami kwarewar yaki da kuma kayan yaki masu kyau. Wannan dalili ne ya sa Rumawa ta mamaye yankunan duniya da yawa, sannan kuma ta zama mafi iko a zamanin ta.

Sannan haruffan turanci da ake amfani da su yanzu, sun samo asali ne daga zamanin Daular Rumawa.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]