Tarihi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Wikidata.svgtarihi
set (en) Fassara
Nikolaos Gyzis - Historia.jpg
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na research object (en) Fassara da chain of events (en) Fassara
Karatun ta study of history (en) Fassara
Stack Exchange site (en) Fassara https://history.stackexchange.com
Classification of Instructional Programs code (en) Fassara 54, 54.01, 54.0101 da 54.0199
Facet of (en) Fassara past (en) Fassara

Tarihi Shine tushe ko asalin abu, Sannan tarihi wani muhimmin abu ne, domin al'ummar da basu zo duniya ba sukan san abinda ya faru idan sunzo duniyar kafin zuwan su, ta hanyar neman sanin dukkan wani abu da ya gabace su. hausawa kan ce Kunne ya girmi kaka. ma`ana, Wato yaro da aka haifa kwanannan zai iya sanin abin da kakansa ma bai sani ba ko kuma ba a haifeshi shi ba sanda abun ya faru. Idan muka duba wannan karin magana za mu ga cewa tabbas tarihi ya na da amfani tunda zai ba ka damar sanin wani abin da ya faru shekara da shekaru. bugu da kari dalilin tarihi ne kaɗai ake sani abubuwan da suke a da chan baya.

Abin lura[gyara sashe | Gyara masomin]

Dukkan wata al'umma da ba ta damu da tarihi ba, to ba shakka ta na cikin matsala saboda ba za su san su, suwaye ba.

Hanyoyin sanin tarihi[gyara sashe | Gyara masomin]

Ana sanin tarihi ta hanyoyi da dama kamar;

  1. Rubutu
  2. Furta sa baki
  3. Amfani da kayan zamami. da sauransu.

A cikin waɗannan hanyoyi ingantacciya kuma tabbatacciya ita ce hanyar rubutawa, larabawa su na cewa ما كتب قررا وما حفظ فررا Wato rubutacce tabbatacce ne haddatacce kam ƴatacce ne. Idan ba a rubuta abu ba to tabbas wata rana ana iya neman sa a rasa.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]