Annabawa a Musulunci
Annabawa a Musulunci | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | manzo |
Bangare na | Al Kur'ani |
Annabawan Musulunci (Harshen larabci|الأنبياء في الإسلام) sun hada da "manzanni" (rasul, dayawa. rusul), wadanda sukazo da Wahayi ta hannun Mala'ika (Lrbc:|ملائكة, malāʾikah);[1][2] Da "Annabawa" (nabī, dywa. anbiyāʼ), wadanda sukazo da shari'o'i da Musulmi suka yarda daga Allah ne zuwa ga dukkan halittu,wanda kuma Annabawan nan ba'a aiko suba sai da harshen da al'umman dake tare dasu zasu fahimta.[1][3] Sani da yarda da Annabawa a musulunci na daga cikin Rukunnan Imani Shida,[4] kuma da ambato na musamman a Qur'an.[5]
Musulmai sun yarda da cewa, Annabi na farko kuma shine mutum na farko da aka fara halitta shine Adam (ادم), wanda Allah Madaukakin Sarki ya halitta (الله). Mafi yawan wahayoyi daga cikin 48 na Annabawa a Yahudanci da Annabawa a Kiristanci anfadesu a Qurani saidai da dan banbanci kadan, misali, the Jewish Ilyas ana kiransa da (Elisha) da yahudanci, (Job) shine Ayyub, Isah kuma Isa, da sauransu. At Torah da akaba Annabi Musa ana kiranta daTorah da musulunci kuma Taurat, (Psalms) da akaba Annabi Dawuda) itace Zabura sukuma suke kira da (Zabur), sai littafin annabi Isah itace Injila (The Gospel).[1]
Wanda ya banbanta a addinin musulunci shine Annabi Muhammad ibn ʿAbdullāh(محمد), wanda musulmai suka yarda da shine "Cikamakon Annabawa" (Khatam an-Nabiyyin, wato. Annabin karshe); kuma Quran ne aka saukar Masa amma ba bashi ya rubuta ta ba,[6] Musulmai sun yarda da cewar itace littafin karshe kuma ita Allah madaukaki ke tsare ta, daga samun wani canji, ragi, kari ko kutse acikin ta,[7] destined to remain in its true form until the Last Day.[8] Musulmai sun tabbatar da Annabi Muhammad shine manzo kuma annabin karshe, dukda cewar ko bayan Annabawa za'a cigaba da samun salihsan bayi wato Waliyyai[9] (Amma wasu daga cikin mazhabobi(makarantu) mabiya sunnah sun Kore batun ansan wahayi na Waliyyai[10]).
A Imanin musulmai, duk wani Annabi a musulunci yana kira ne akan Abubuwan dasune ginshikin addinin musulunci, kamar Kadaita Allah, bautan Allah shi kadai, kinyin bautar wani abu koma bayansa da aikata sabo, da kuma imani Ranar Kiyama ko Ranar Sakamako da rayuwa bayan mutuwa. Duk kowannensu sunzo suyi kira zuwa addinin Allah a mabanbantan lokuta a tarihi, wasunsu sun sanarda zuwan Annabi kuma Manzon karshe daga Allah, Wanda za'a samasa suna "Ahmad and Muhammad".
Wadannan bayanan ansamesu acikin surorin Alqur'ani, Qur'an, 61:6 sanda Allah ya umurce Isah daya tunatar da mutanen ya'yan banu Isra'ila amma sai suka tuhume shi akan manzancinsa:
وَإِذْ قَالَ عِيسَى ٱبْنُ مَرْيَمَ يَـٰبَنِى إِسْرَٰعِيلَ إِنِّى رَسُولُ ٱللهِ إِلَيْكُم مُّصَدِقًا لِّمَا بَيْنَ يَدَىَّ مِنَ ٱلتَّوْرىٰةِ وَمُبَشِّرًا بِرَسُولٍ يَأْتِى مِن بَعْدِى ٱسْمُهُ أَحْمَدُ فَلَمَّا جَآءَهُم بِٱلْبَيِّنَـٰتِ قَالُواْ هَـٰذَا سِحْرٌ مُّبينٌ
wa-idh qāla ‘Īsā ’b·nu Maryama: "yā Banī Israā‘īla innī Rasūlu ’llāhi ilay-kum muṣaddiqal li-mā bayna yadayya mina ’t-Tawraāti wa-mubash·shiram bi-Rasūlin ya’tī mim ba‘dī ’s·mu-huū Aḥmadu, fa-lammā jaā’a-hum bi’l-bayyināti, qālū "hādhā siḥrum mubīn!"
And remember, Jesus, the son of Mary, said: "O Children of Israel! I am the messenger of Allah (sent) to you, confirming the Law [[Taurat]] (which came) before me, and giving Glad Tidings of a Messenger to come after me, whose name shall be Ahmad." But when he came to them with Clear Signs, they said, "this is evident sorcery!" Quran, sura 61 (As-Saf).
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 cite book|last1=Campo|first1=Juan Eduardo|title=Encyclopedia of Islam|date=2009|publisher=Infobase Publishing|isbn=9780816054541|pages=559–560|url=https://books.google.com/books?id=OZbyz_Hr-eIC&pg=PA559&dq=prophethood+in+islam+encyclopedia&hl=en&sa=X&ei=pTKIVduAEobuoAS0-Yi4Ag&ved=0CB0Q6AEwAA#v=onepage&q=prophethood%20in%20islam%20encyclopedia&f=false%7Caccessdate=22 June 2015
- ↑ Shaatri, A.I. (2007). Nayl al Rajaa' bisharh' Safinat an'najaa'.Dar Al Minhaj.
- ↑ Cite quran|30|47|s=ns
- ↑ Cite web|url=http://www.bbc.co.uk/religion/religions/islam/beliefs/beliefs.shtml%7Ctitle=BBC - Religions - Islam: Basic articles of faith|last=|first=|date=|website=|language=en-GB|archive-url=https://web.archive.org/web/20180813005904/http://www.bbc.co.uk/religion/religions/islam/beliefs/beliefs.shtml%7Carchive-date=13 August 2018|dead-url=no|access-date=2018-10-05
- ↑ quran-usc|2|285|s=ns
- ↑ cite book|last=Denffer|first=Ahmad von|title=Ulum al-Qur'an : an introduction to the sciences of the Qur an|year=1985|publisher=Islamic Foundation|isbn=0860371328|pages=37|edition=Repr.
- ↑ Understanding the Qurán - Page xii, Ahmad Hussein Sakr - 2000
- ↑ Cite quran|15|9|s=ns
- ↑ Neal Robinson Christ in Islam and Christianity SUNY Press 1990 ISBN|978-0-791-40558-1 page 58
- ↑ Radtke, B., Lory, P., Zarcone, Th., DeWeese, D., Gaborieau, M., F. M. Denny, Françoise Aubin, J. O. Hunwick and N. Mchugh, "Walī", in: Encyclopaedia of Islam, Second Edition, Edited by: P. Bearman, Th. Bianquis, C. E. Bosworth, E. van Donzel, W. P. Heinrichs.