Alqur'ani mai girma
Al-Qur'ani (Larabci: القرآن al-Qur'an) ko kuma Alkur'ani mai girma kamar yadda musulmi suka fada, littafi ne mai tsarki wanda Allah ya saukar da ayoyinsa ga annabin musulunci Muhammad (SAW). ta hannun mala'ika Jibrilu. A cikin akidar Musulunci, Kur'ani shi ne mafi muhimmanci kuma mafi girman mu'ujizar Muhammadu, yana tabbatar da cewa Muhammadu Annabi ne na gaskiya.
Shari'ar Musulunci, wacce kuma ake kira sharia, ta dogara ne akan Kur'ani (Madogararsa na Farko), tare da hadisai da ake ganin maganar Muhammadu ne. Musulmai suna karanta ayoyin kur'ani daban-daban a cikin addu'o'insu.
Lafiyayyan hankali da tsaftataccen tunani na dan Adam da ayyuka na yau da kullum sun tabbatar da cewa kur'ani ya bada cikakkiyar kulawa da kariya ta fuskar haƙƙin ɗan adam na duniya, da 'yancin ɗan adam.[1]
Hotuna[gyara sashe | gyara masomin]
Mushafin al-qurani tun karni na 7 shekara dari bayan wafatin Annabi Muhammad SAW a Birmingham kasar Ingila
Rubutun qurani a warsh da turanci
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
- Quran Word by Word // QuranAcademy.org
- Translation of the Meanings of the Quran into Hausa