Jump to content

Madinah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Madina)
Madinah
المدينة المنورة (ar)


Wuri
Map
 24°28′N 39°37′E / 24.47°N 39.61°E / 24.47; 39.61
Ƴantacciyar ƙasaSaudi Arebiya
Province of Saudi Arabia (en) FassaraMedina Province (en) Fassara
Babban birnin
Khulafa'hur-Rashidun (632–656)
first Islamic state (en) Fassara (622–632)
Medina Province (en) Fassara (1932–)
Q97307705 Fassara (1992–)
Yawan mutane
Faɗi 1,411,599 (2022)
• Yawan mutane 2,396.6 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 589 km²
Altitude (en) Fassara 608 m
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 9 century "BCE"
Muhimman sha'ani
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
UTC+03:00 (en) Fassara
Wasu abun

Yanar gizo amana-md.gov.sa
masallacin Annabi
Masallacin Annabi (s.a.w) dak e birnin madinah
madina Hilton

Madinah: Birni ne da ke a yammacin Saudi Arabia Archived 2015-03-16 at the Wayback Machine nahiyar Asiya cikin tsakiyar yankin gabas ta tsakiya Baruch larabawa, shi dai wannan birni ya kafu ne tun dubbanin shekaru a baya tun a zamanin Annabawa. Hakika birnin Madinah garin Musulunci ne shi ne birnin manzon Allah Annabi Muhammad (S.A.W). Kafin zuwan Musulunci ana kiran birnin da suna Yathrib, amma daga baya sai Annabi ya canjawa garin suna zuwa Madinah ko kuma Madinat Al-munawwarah, a cikin birnin akwai babban masallaci wanda shine farkon Masallacin da Annabi Muhammad (S A W) ya gina a Madinah, wannan masallaci shine ake Kira da masallacin Quba.

Faɗin ƙasa

Birnin Madinah yana da fadin kasa kamar haka:

  • Fadin gari

589 km2 (227 sq mi)

  • Fadin babban birni

293 km2 (112 sq mi)

  • Maki mafi daukaka

608 m (1,995 ft)

  • kididdigar yawan mutane a shekarar (2010)

1,180,770

  • Density

2,000/km2 (5,200/sq mi)

Taswirar birnin Madinah
Wannan taswirar Birnin Madinah kenan.

Hakika birnin Madinah yanada matukar tasiri a Musulunci, shi ne garin Annabi Muhammad (S.A.W) bayan hijararsa daga birnin Makkah acikin garin yayi rayuwa har yakoma zuwa ga Allah, sannan kuma acikin birnin aka birne shi, acikin dakin matarsa nana Aisha inda a nanne yarasu, Wanda a yanzu nan ne masallacinsa, Shi yasa duk Alhazan da sukaje Madinah to sai sun kai ziyara kabarinsa (S.A.W) da manyan sahabbansa.


Masallacin Annabi SAW na Madina

[gyara sashe | gyara masomin]

Ziyara zuwa waje na biyu mafi tsarki a Musulunci, wanda ya samu shekara 1440 da suka gabata.

Daga Sagiru Saleh

Babban Masallacin Madina shi ne na biyu a cikin masallatai mafiya daraja, wanda kuma Annabi Muhammad (SAW) ya fara jagorantar Sallah a cikin sa.

[gyara sashe | gyara masomin]

Masallacin Manzon Allah shi ne wurin da aka fara sanya hasken lantarki a fadin yankin Larabawa a 1909, kamar yadda Sultan Ghalib Al Quaiti ya fada a littafinsa, The holy cities, the Pilgrimage and the World of Islam.

[gyara sashe | gyara masomin]

Ana fadada shi ta yadda zai dauki mutum miliyan daya da dubu 800. Inuwar rumfunan alfarma masu sarrafa kansu kuma masu daukar mutum dubu 800 guda 250 da ke masallacin sun kai murabba'in mita dubu 143, kamar yadda shafin hukumar gudanarwar masallacin ya bayyana.

Nan gaba za mu kawo muku bayanai gwargwadon hali a kan tambayoyin da kuka aiko mana na abubuwan da kuke son sani game da Masallacin Manzon Allah SAW da ke Madina.

Hadisai sun nuna cewa Masallacin Manzon Allah SAW shi ne masallaci mafi tsarki da falala da girma a ban kasa, bayan Masallacin Makkah.

Shi ya sa ake wa masallatan biyu lakabi da masallatai biyu tsarkaka masu daukaka, wato Al-haramainush sharifain, da harshen Larabci.

Masallacin Manzon Allah, wanda ke kwaryar birnin Madina a kasar Saudiyya shi ne wuri da aka fara sanya wa hasken lantarki a fadin yankin Labarawa tun a shekarar 1909 miladiyya.

Fitaccen marubucin tarihin Manzon Allah SAW, Safiur-Rahman Mubarakfuriya ya bayyana a littafin Al-rahikul Makhtum cewa masallacin shi ne biyu da aka gina a Madina bayan masallacin Kuba.A wancan lokaci an gina masallacin ne a kusa da gidan Annabi Muhammad (SAW) shekara ta farko bayan hijira daga Makka zuwa Madina (632 miladiyya). Kuma sallah daya a masallacin Manzon Allah SAW ta fi sallah 1,000 da aka yi a wasu masallatai daraja, ban da masallacin Ka'aba. Kabarin Manzon Allah SAW da na manyan sahabbansa biyu, Abubakar da Umar na cikin masallacin a yanzu, sakamakon fadada masallacin da aka yi a tsawon shekaru sama da 1,400, kaburburan na cikin wani daki da aka yi na kusa da mumbarin da ke cikin rauda, wanda a zamanin Annabi dakin matarsa ne Nana Aisha. Sakamakon fadada wannan masallaci a tsawon zamani, yanzu Rauda ta shige cikin wanan masallacin. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa tsakanin gidana da mimbarina akwai dausayi daga cikin dausayin Aljanna. Wannan wuri shi ne Rauda.

Girman Masallacin Madina

Saboda girman Masallacin Madinah ya kan dauke duk miliyoyin mahajjata da masu umrah da ke ziyartarsa a kowace shekara. Kuma shi ne wurin da mahajjata da masu umrah suka fi ziyarta a fadin Madina. A nan suke yin sallah, su shiga Rauda in hali ya samu, su ziyarci Annabi SAW da sahabbansa a makwancinsu da kuma makabartar Baki'a. Har yanzu ana ci gaba da fadada shi ta yadda zai iya daukar masallata kusan miliyan biyu a lokaci guda, saboda yadda yawan masu ziyartarsa ke karuwa a lokacin Hajji. Girman masallacin a yau ya kai ninki 100 na yadda aka fara gina shi. Kuma ya kusa mamaye fadin asalin garin Madina a zamanin Manzon Allah SAW..Sannan masallacin a bude yake a koyaushe domin masu ibada. Baya ga manyan hasumiyoyi 10 masu tsawon mita 103 kowannensu, masallacin na da kubbobi (tulluwa) 170 da suka hada da masu ruwan azurfa da farare da wasu 27 na zamani masu sarrafa kansu. Akwai kuma wata koriyar kubba babba a daidai saman inda kabarin Manzon Allah yake, ita ake wa kirari da Koriyar Kubba ta Dan Abdullahi. A gefen koriyar kubbar akwai wata kubba mai ruwan azurfa.

Hotuna daga birnin Madina

[gyara sashe | gyara masomin]