Sunna

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Sunna
سنن الدارقطني.jpg
Asali
Mawallafi Muhammad
Characteristics
Harshe Larabci
Masallacin Harami dake Makka waje na daya mafi tsarki a wajen Musulmi Mabiyin Sunnar Annabi Muhammad (S.A.W.)

Sunna Shine bangare mafi girma daga cikin bangarorin addinin Musulunci. Asalin sunan yazone daga kalmar Sunnah, wato koyi da yin dukkan abun da Annabi Muhammad (S.A.W.) Ya aikata, ko Yayi umarni da a aikata ko kuma aka aikata shi a gabansa amma bai yi hani ba. Bambanci tsakanin Akidun Sunnah da kuma na Shi'a Ya samo asaline tun daga takaddama akan wanda ya cancanci ya jagoranci al'umar Musulmai bayan wafatin Annabi (S.A.W.) wato Khalifanci.A bangaren fahimtar mabiya Sunnah sunce,tunda yake Annabi (v) bai yi nuni ba da wani cewa shi za'abi to sai suka yanke hukuncin a baiwa surukin sa wato Sayyadina Abubakar ya zamo Khalfa na farko.

Amma a bangaren Mabiya Shi'a kuwa sai sukace ai a ranar Ghadir Khumm Annabi (v) ya sanar da cewa ba wanda zai gaje shi sai dan'uwan sa kuma sirikin sa wato Sayyadina Aliyu sun ce sabo da shi jinin sane kuma surukin sa wato mijin yarsa Sayyida Fatima Bint Nabiy.

Tun daga nanne rikicin bangaren Sunnah da Shi'a ya samo asali.

A shekarar 2009 Musulmai mabiya Sunnah sunkai 87% zuwa 90%. Haka zalika Mabiya Bangaren Sunnah sune bangare a Addini wanda sukafi ko wanne yawa a duniya bayan Katolika a Kiristanci.Sanannu ne a sunan da sukayi fice a shi wato Ahlul Sunnah Wal Jama'a wato (al'uma mabiya sunnah).

Akidun mabiya Sunnah[gyara sashe | Gyara masomin]

Ga jerin akidojin Sunnah kamar Ha:

Shika-shikan Musulunci a wajen mabiya Sunnah[gyara sashe | Gyara masomin]

Shika-shikan Musulunci a wajen mabiya sunnah guda biyar ne sune.

Imani da Allah da Annabi Muhammada (S.A.W.)[gyara sashe | Gyara masomin]

Wato mutum ya furta kalmar SHahada kamar haka LA ILAHA ILALLAH MUHAMMAD RASULULLAH ma'ana mutum ya hakikance a ransa cewa BABU WANI ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH SANNAN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W.) BAWAN ALLAH NE KUMA MANZON ALLAH NE .

Tsai Da Sallah[gyara sashe | Gyara masomin]

Yin salloli guda biyar a kowacce rana.

Da Azumi Watan Ramadan[gyara sashe | Gyara masomin]

Sai yin azumin watan Ramadana wato wata na tara a kalandar Musulunci.

Da Bada Zakka[gyara sashe | Gyara masomin]

Shine mutum ya cire wani adadi da shari'a ta fada na dukiyar sa ya bayar dashi ga mabukata Zakka saboda Allah.

Da ziyartar Dakin Allah Ga Wanda Allah Yabawa Ikon Zuwa (Hajji)[gyara sashe | Gyara masomin]

Idan Musulmi ya kasance yana da dukiyar da takai zai iya biyan ta wajen zuwa Saudiyya kuma yana da karfin lafiya to Hajji ya hau kan sa.

Shika-shikan imani a wajen mabiya Sunnah[gyara sashe | Gyara masomin]

Shika-shikan Imani a makidar mabiya sunnah guda shida ne, gasu kamar haka.

 • Imani da Allah
 • Imani da Mala'iku
 • Imani da Litattafai Saukakku
 • Imani da Manzannin Allah
 • Imani da Ranar Kiyama
 • Imani da Kaddara

Matsayin Hadisai a wajen mabiya Sunnah[gyara sashe | Gyara masomin]

Sanannun litattafan Hadisannan guda shida wato Kutub al-Sittah sune litattan hadisan da mabiya sunnah suka yi imani da gaskiyar hadisan dake cikin su Ga jerin su:

 • Sahih al-Bukhari o na Muhammad al-Bukhari
 • Sahih Muslim na Mislim ibn al-Hajjaj
 • Sunan al-Sughra na Al-Nasa'i
 • Sunan Abu Dawud na Abu Dawood
 • Jami' at-Tirmidhi na Al-Tirmidhi
 • Sunan Ibn Majah na Ibn Majah

Amma ba iyakar wadannan kadai bane litattafan da mabiya sunnah suka amince da gaskiyar hadisan dake cikin su ba, akwai dansu litattafan da dama wadanda suka hada da:

 • Musannaf na Abd al-Razzaq o na ‘Abd ar-Razzaq as-San‘ani
 • Musnad na Ahmad ibn Hanbal
 • Mustadrak na Al Haakim
 • Muwatta na Imam Malik
 • Sahih Ibn Hibbaan
 • Sahih Ibn Khuzaymah of Ibn Khuzaymah
 • Sunan al-Darimi na Al-Darimi

Iyalan gidan Annabi (S.A.W.) a mahangar Sunnah[gyara sashe | Gyara masomin]

Su ne DUKKAN DANGIN Manzon Allah (SAW) wadanda sadaka ta haramta garesu, da kuma MATANSA da ZURIYYARSA. Allah ya yarda da su gaba daya. Sabanin Akidun Shi'a ko Rafidanci Wadanda suke cewa Iyakacin Nana Fatima da Imamuna Aliyu da suran zurriyar su, sune kadai Iyalan gidan Manzon Allah (S.A.W.). Wannan gurguwar fahimta ce a mahangar Mabiya Sunnah.

Ahlus Sunnah sun yi ITTIFAQI akan WAJABCIN Son Ahlul Baiti, da kuma HARAMCIN Cutar dasu, ko Munana musu, da magana ko aiki.

Sahabbai a mahangar mabiya Sunnah[gyara sashe | Gyara masomin]

Rashidun Caliph Abu Bakr as-Șiddīq (Abdullah ibn Abi Quhafa) - أبو بكر الصديق عبد الله بن عثمان التيمي القرشي أول الخلفاء الراشدين.svg

Sahabbai Sune dukan mutanen da suka ga Annabi (S.A.W.) sanna Kuma suka bayar da gaskiya da shi. Wadannan mutane suna da matsayi mai girma tare da samun girmamawa daga wajen mabiya akidar sunnah.

Mabiya Sunnah suna yin cikakkiyar soyayya da biyayya ga sahabbai ne sakamakon wadansu ayiyin Alkur'ani inda Allah da kansa yake yabon su, kamar haka:

Kuma magabatan farko na Muhajirai da Ansarai da waxanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda da su kuma sun yarda da shi,kuma ya yi musu tattalin gidajen aljanna, qoramu suna gudana a qarqashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada. Wancan ne rabo mai girma.

- Suratut Taubah: 100

A wannan aya mutane sun kasu kashi uku. Muhajirai da Ansarai da wadanda suka bi su da kyautatawa ba da zagi ba.

Sai kuma aya ta gaba:

Muhammad manzon Allah ne. Kuma wadanda da ke tare da shimasu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, ka na ganinsu suna masu ruku’i masu sujada, suna neman falala daga Ubangijinsu, da yardarsa. Alamarsu tana a cikin fuskokinsu, daga kufan sujuda. Wannan ita ce siffarsu a cikin Attaura. Kuma siffarsu a cikin Linjila ita ce, kamar tsiron shuka wanda ya fitar da reshensa, sa’an nan ya qarfafa shi, ya yi kauri, sa’an nan ya daidaita a kan qafafunsa, yana bayar da sha’awa ga masu shukar, domin (Allah) ya fusatar da kafirai game da su. Kuma Allah ya yi alqawali ga waxanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan qwarai daga cikinsu da gafara da lada mai girma

- Suratul Fathi, Aya ta 29

Sahabbai goma wadanda akayi masu albishir da shiga Aljannah tun suna duniya. Manzon Allah (S.A.W.) yana da Sahabbai 120,4000. Duk da cewa dukkan wadannan Sahabbai 'yan Aljanna ne to amma akwai wadanda akayi musu bishara da Aljanna tun suna da rai.

Akwai guda goma wannan Manzon Allah (S.A.W.) ya fada a hadisi cewa an yi musu bishara da gidan Aljanna, wato ASHARATUL MUBASHSHIRUN. Wannan Sahabbai sune:

 1. Abubakar Saddik (R.T.A.)
 2. Umar Bin Khaddab (R.T.A.)
 3. Usman Bin Affan (R.T.A.)
 4. Aliyu Bin Abi Dalib (R.T.A.)
 5. Dhalha Ibn Ubaidullah (R.T.A.)
 6. Zubair Ibnul Awwam (R.T.A.)
 7. Abdurrahman Bin Auf (R.T.A.)
 8. Sa'ad Bin Wakkas (R.T.A.)
 9. Sa'id Bin Zaid Bin Amr (R.T.A.)
 10. Abu Ubaidah Bin Jarrah (R.T.A.)

Allah Madaukin Sarki ya bamu albarkacin wadandan bayi nasa.