Izala

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Group half.svgIzala
Bayanai
Iri Tsarin Siyasa
Ƙasa Najeriya
Mulki
Hedkwata Jos
Tarihi
Ƙirƙira 1978

Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa'Ikamatus Sunnah (JIBWIS). Ƙungiyar Addinin musulunci ce, mabiya Sunnahr manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Ƙungiya ce da aka kafa ta da manufar yaqi da bidi'o'i, wato ƙirqire-ƙirqire a cikin addini da kuma tabbatar da biyayya ga Annabi Muhammadu (Aminci Allah ya tabbata agare shi) shi kaɗai, tare da abubuwan da ya zo da su daga Allah Maɗaukakin Sarki, ba tare da daɗi ko ragi ba.

Kamar yadda ƙungiyoyi masu kawo sauyi da gwagwarmaya a duniya suka sha wuya da suka daga hannun jama'a a karon fari, ita ma ƙungiyar Izala ta sha fama da irin wadannan matsaloli, amma daga baya ta yi nasara wajen kafa tsayayyen tsarin bin hanyar addinin Islama, ta yadda har wasu ƙungiyoyin da su ka fi ta daɗewa su ka dawo suna koyi da ita.

Daga cikin muhimman manufofin wannan qungiya sun hadar da:

1) Kaɗaita Allah da bauta ba tare da haɗa Shi da wani (shirka) ba. Sannan a tabbatar biyayya ga Annabi Muhammadu (S.A.W) ba tare da jayayya ko kawo maganganun wasu mutane ba.

2) Tabbatar da bin ɗabi'un (sunnar) Manzon Allah (S.A.W) ba tare da ƙirƙire-ƙirƙire ba.

3) Watsi da dukkanin al'adun da suka saɓa ma addinin Islama.

4) Soyayyar Annabi (S.A.W) da iyalan shi da sahaban shi /abokan shi da kuma surukan shi ba tare da sukar ko ɗaya daga cikin su ba.

5) Tabbatar da neman ilimin addini da na boko a ko'ina a faɗin duniya tare da bin dokokin addini.

6) Tabbatar da mutuncin waliyyan Allah na gaskiya da salihan bayi da duk sauran mutanen kirki.

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.