Sani Yahaya Jingir

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Sani Yahaya Jingir
Rayuwa
Haihuwa Jos
ƙasa Najeriya
ƙungiyar ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Hausa
Larabci
Sana'a

Sani Yahaya Jingir malamin Addinin Islama ne, wanda ke zaune a jihar Filato,[1][2] Kuma Shi ne Shugaban Majalisar Malaman, Jama'atul Izalatil Bid'ah Wa'Ikamatis Sunnah (JIBWIS) a karkashin jihar Jos . A ranar 25 ga watan Mayun shekarar 2015, an zabe shi a matsayin shugaban majalisan ne bayan an yanke shawara a wani taron majalisa a Jos da manyan shuwagabannin ta sukayi, wanda majalisar dattawan Ulama’un ta yi, yayin da Sheikh Alhassan Saed Adam ya zama mataimaki, an yi zaben ne lokacin da majalisar ta rasa shugabanta Sheikh Zakariyya Balarabe Dawud.

Shahararren aikin Musulunci[gyara sashe | Gyara masomin]

Jingir yana yin tafsirin watan Ramadana na shekara shekara ne a cikin garin Jos, Yana daya daga cikin manya manyan malamai a Arewacin Najeriya . Jingir ya yi wa'azin koyarwa kan mahimmancin fa'idar ilimantarwa a tsakanin dukkan mutanen biyu, Jingir ya yi fatali da cewa duk wanda ya hada Ibrahim Inyass tare da Allah a cikin bautansa toshi Kafiri ne, Jingir yana nuna mahimmancin yin azumin sittu shawwal wato azumin da akeyi guda shidda bayan gama azumin watan Ramadana, Jingir ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta yi aiki tare da Saudi Arabiya kan abin da ya faru a Saudi Arabiya a lokacin aikin Hajji a ranar 24 ga watan Satumbar shekara ta 2015, ta dauki kwararan matakai don hana aukuwar irin wannan taron hadari a gaba. rushewar Jingir yayi ta wa'azi tukuru a kan Boko Haram sabo kafir cewan su saboda sunayni Jihadi ba bisa ka'idar da Musulunci da Shari'ah ba, Jingir a lokacin wani bikin bude masallacin Juma'ah [Mosque] a saman Dutsen Zinariya a arewacin Jos, Ya gargadi masu satar mutane a duk fadin kasar da su nemi gafarar Allah, su tuba, haka ma zai shirya addu’o’i na musamman da azumin har Allah Ya shafe su, wasu mutane sun gaza wajan yunƙurin kashe shi bayan an biya shi Naira dubu 500

Zargi[gyara sashe | Gyara masomin]

Gwamnatin jihar Filato ta kama Jingir bayan ya karya doka ta hanyar yin sallar juma'a a ranar 27 ga watan Maris 2020, Lokacin da aka ayyana dokar hana fita da kuma dokar kulle masallatai da choci-choci na dukkan Kiristoci da Musulmin Najeriya ba su da sallar idi don guje wa yaduwar cutar corona, Jingir ya ce; An aiwatar da Coronavirus don dakatar da Musulmi daga Salah ne, Har ila yau a ranar Jumma'a ne a gidansa a Jos Jingir ya ce: "Coronavirus baƙar fata ce kuma farfagandar da ake nufi don yaƙar Musulunci da kuma aiwatar da yaƙin tattalin arziki tsakanin China da Amurka. " Ya kuma kira hankalin gwamnatin tarayya da na jihohi da kada su hana yin sallolin farilla a masallatai fa, Jingir ya kuma ce " Ina kiran masarautar Saudi Arabiya data bude manyan masallatan Makka da Madina domin musulmai su iya tsayar da salla." Jingir ya kuma bayyana ƙarin dalilai da kuma ra’ayinsa game da abin pendamic. Bayan haka Jingir ya yi wani korafi cewa zai bi dukkan dokoki da kuma aiwatarwa da gwamnatin Najeriya ta bayar don magance cutar ta coronavirus saboda ya fahimci cewa Cutar ta ainihi ce ba kamar yadda yake tsammani ba.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. https://blueprint.ng/sheikh-jingir-now-plateau-ulamau-council-boss/
  2. https://www.nigerianbulletin.com/tags/sheik-sani-yahaya-jingir/