Abubakar Gumi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Simpleicons Interface user-outline.svg Abubakar Gumi
Abubakar Mahmoud Gumi.jpg
Rayuwa
Haihuwa Gumi, 5 Nuwamba, 1922
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Mutuwa Landan, 11 Satumba 1992
Yanayin mutuwa  (Sankaran Bargo (Leukemia))
Ƴan uwa
Yara
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a qadi (en) Fassara
Kyaututtuka
Imani
Addini Mabiya Sunnah
Wannan masallaci shi ne shugaba gurin gina shi amma har ya rasu bai yi wa'azi a ciki ba,a akaramin masallaci ya ke karatu da wa'azi

Sheikh Abubakar Mahmud Gumi (An haife shi a ranar 5 ga watan Nuwamba a shekara ta 1922 ya kuma rasu a ranar 11 ga watan Satumba shekara ta 1992, a Landan)[1][2] Shahararren Malamin Addinin musulunci ne kuma Alkalin Alkalai (Grand kadi) na arewacin Najeriya. Shi ne uba, jigo kuma tushen Izala da Salafanci a Najeriya.[3]

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Ya yi karatu da rubuce-rubuce a kan addinin musulunci sosai, ya fassara Qur'ani zuwa harshen Hausa, kuma shine mutum na farko daya rubuta tarjama wato fassarar dai-daikun ayoyin dake Alkur'ani.[4] Hakan ne ya sa ya samu nasarar samun kyautan Sarki Faisal(King Faisal Award) daga kasar ta Saudiya. Malamin dai ya kasance babban aboki kuma mai ba wa Firimiya Ahmadu Bello sardaunan Sakkwato shawara. Shi ne mahaifin Dakta Shaykh Ahmad Gumi.

Shahara[gyara sashe | gyara masomin]

Gumi ya shahara tun lokacin mulkin mallakar turawa a matsayin mai fada a ji, yana sukar salon Mulkin Turawa cewa ya karya lagon sarakunan Musulmi kuma hakan yana kara karfafa al'adun Turai a kasashen musulunci. A farkon shekara ta 1960s an samu barkewar rikici tsakanin shi da malaman sufaye wanda daga baya rikicin ya koma muhawara a gidajen rediyo da talabijin a shekarun 1970 zuwa shekara ta 1980.[5] Ya riƙa amfani da ranakun Juma'a a matsayin lokutan yada akidunsa a babban masallacin juma'a na Kaduna mai suna Masallacin Sultan Bello.

Dangi[gyara sashe | gyara masomin]

Ba a san takamaiman yawan ƴaƴansa ba, amma mafi shahara a cikinsu shi ne Dr. Ahmad Gumi Wanda shi ne ya gaji Mahaifinsa a matsayin mai gabatar da wa'azi a masallacin na Sultan Bello. Dr Ahmad Gumi kwararren likita daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Kuma tsohon jami'in sojin Najeriya ne, ya bar aikin soja inda ya tafi zuwa Saudiyya domin karanta ilimin fikihu, a jami'ar Ummul Quraa da ke birnin Makka inda ya samu shaidar digirin digir-gir.[6]

Sheikh Abubakar Gumi a shekarar 1970

Duba nan[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. The Independent: "Obituary: Sheikh Abubakar Mahmud Gumi" by Karl Maier 16 September 1992
  2. John O. Hunwick; Rex Séan O'Fahey (1994). Arabic Literature of Africa: The writings of central Sudanic Africa Vol.2. Volume 13. BRILL. p. 551. ISBN 90-04-10494-1.
  3. Hunwick, John O.; O'Fahey, Rex Séan (1994). Arabic Literature of Africa: The writings of central Sudanic Africa Vol.2. Volume 13. BRILL. ISBN 978-90-04-10494-5.
  4. John N. Paden, Muslim Civic Cultures and Conflict Resolution: the challenge of democratic federalism in Nigeria, Brookings Institution Press, 2005. p 60. ISBN 0-8157-6817-6
  5. The Independent: "Obituary: Sheikh Abubakar Mahmud Gumi" by Karl Maier 16 September 1992
  6. John Owen Hunwick. Religion and National Integration in Africa: Islam, Christianity and Politics in the Sudan, Northwestern University Press, 1992. p 551. ISBN 0-8101-1037-7