Jump to content

Ahmad Gumi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ahmad Gumi
Rayuwa
Haihuwa Kaduna, 1959 (64/65 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Mutanen Fulani
Ƴan uwa
Mahaifi Abubakar Gumi
Karatu
Harsuna Turanci
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a mufti (en) Fassara da Malamin addini
Imani
Addini Mabiya Sunnah

Ahmad Abubakar Gumi ko Ahmad Gumi, ko mufti, ɗa ne ga daya daga cikin shahararrun malaman Sunna a Arewacin Najeriya marigayi Shaykh Abubakar Mahmud Gumi.[1]

Farkon rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ahmad Abubakar Gumi a shekara ta alif dari tara da hamsin da tara 1959. Ya kasance ɗa ne ga malam Abubakar Mahmud Gumi[2] kuma shi ne babban ɗan sa wanda mahaifiyarsa ita ce Amina Abubakar Gumi kuma uwargida ce a cikin mata uku da malamin ya aura.

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Ahmad Abubakar Gumi yafara makarantar sa ta farko a cikin garin Kano, inda daga bisani ya dawo jihar Kaduna ya halarci Kwalejin [[Kwalejin Tunawa da Sardauna]] (Sardauna Memorial College (SMC)) don gudanar da karatun babbar sakandire, sannan bayan ya kammala karatun sa, ya samu shiga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya don yin karatun Likitanci, bayan kammala karatun sa ya sa ya shiga Kwalejin Tsaron Najeriya, inda ya fito a matsayin Sojan Najeriya. Gumi ya yi murabus daga aikin soja a matsayin Kaftin kuma ya koma Saudi Arebiya don ci gaba da karatunsa a fannin addinin Musulunci a Jami’ar Ummul al-Qura inda ya yi karatun Fiƙihu da Tafsiri inda yakai ga samun matakin karatu na digirin digirgir wato digiri mataki na uku (Ph.D) daga Jami'ar Ummul Qura dake Birnin Makkah a ƙasar Saudiya.[3]

Ahmad Gumi ya kasance mai son ganin ƴan siyasa sun bi dokokin ƙasa wurin aiwatar da haƙƙoƙin da aka ɗauka masu na jama'a, abinda ya jawo wasu suke ganin malamin bai dace yana sanya kansa cikin batutuwan siyasa ba. A shekarun 2012 zuwa 2014 yayi suna wurin nuna matsalolin gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan. Kuma haka a baya bayan nan ana jinsa yana yawan janyo hankali game da mulkin shugaba Muhammadu Buhari bisa ga salon Mulkin sa da yadda bai kula da harkokin tsaron ƙasa.[4]

Gwamnatin kasar Saudiyya ta taɓa kama shi a shekarar 2013 bisa zargin alaƙa da Umar Faruq Abdulmutallab wanda ya yi nufin tayar da ban a wani jirgin Amurka. Amma daga baya aka sallame shi bayan jami'ai sun wanke shi.

Aikin soja[gyara sashe | gyara masomin]

Ya yi aiki a Kwalejin Tsaro ta Najeriya a matsayin jami'in soja, kuma ya yi ritaya a matsayin kyaftin.

Tuhuma[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar juma'ar 25 ga watan Juni, na shekarar 2021. Hukumar Department Of Security Service ( DSS) suka gayyace shi domin tuhumar sa da sukeyi akan alaqar sa da yan ta'adda da fulanin daji masu garkuwa da mutane. Inda yake samun su domin samun sulhu.[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.bbc.com/hausa/labarai-44699864
  2. "Log In - Oxford Islamic Studies Online". www.oxfordislamicstudies.com. Archived from the original on 2021-09-27. Retrieved 2020-05-26.
  3. "Kaduna Blast, I list targeted Terrorists". Daily Post. Retrieved 9 November 2021.
  4. "Ahmad Gumi". Archived from the original on 27 September 2021. Retrieved 9 November 2021.
  5. https://guardian.ng/opinion/be-careful-what-you-do-with-sheikh-gumi/