Muhammadu Buhari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Simpleicons Interface user-outline.svg Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari, President of the Federal Republic of Nigeria.jpg
Minister of Petroleum Resources (en) Fassara

11 Nuwamba, 2015 -
Diezani Alison-Madueke
15. shugaban ƙasar Najeriya

29 Mayu 2015 -
Goodluck Jonathan
7. shugaban ƙasar Najeriya

31 Disamba 1983 - 27 ga Augusta, 1985
Shehu Shagari - Ibrahim Babangida
Gwamnan Jihar Borno

ga Yuli, 1975 - ga Maris, 1976
Musa Usman - Mustapha Amin (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Daura, 17 Disamba 1942 (80 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Fillanci
Ƴan uwa
Abokiyar zama Aisha Buhari
Yara
Karatu
Makaranta United States Army War College (en) Fassara
Defence Services Staff College (en) Fassara
military education and training (en) Fassara
Mons Officer Cadet School (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Fillanci
Sana'a
Sana'a soja, ɗan siyasa, Malami, hafsa da international forum participant (en) Fassara
Kyaututtuka
Aikin soja
Fannin soja Sojojin Ƙasa na Najeriya
Digiri Manjo Janar
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress
Congress for Progressive Change (en) Fassara
thisisbuhari.com
Hoton Shugaba Buhari a shekara ta 2015.

Muhammadu Buhari G.C.F.R (An haife shi a ranar 17 ga watan Disambar shekara ta 1942), kuma ya kasance tsohon soja ne mai ritaya, kuma ɗan siyasa, ana masa lakabi da Baba Buhari. Ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya ne a zaɓen shekarar 2015 a karo na farko, lokacin da yake ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga cikin jam'iyyar siyasar Najeriya wato APC (ALL PROGRESSIVE CONGRESS) ya kada tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan. Buhari ya sake samun nasarar zama shugaban ƙasar Najeriya a karo na biyu a shekara ta 2019 yayin da ya kayar da ɗan takarar Jam'iyyar hamayya wato Alhaji Atiku Abubakar. Muhammad Buhari ya taɓa shugabancin PTF watau (Asusu na musamman don tattara Kudin Man Fetur Wanda aka fi sani da (Petroleum Special Trust Fund (PTF) wanda tsohon Shugaban mulkin soji wato Janar Sani Abacha ya bashi matsayin, kuma ya taɓa riƙe Ministan man-fetur a lokacin mulkin soji na Janar Sani Abacha.[1][2][3]

Farkon rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Muhammadu buhari

An haifi Muhammad Buhari a ranar 17 ga watan Disambar shekara ta alif, 1942 a garin Daura da ke cikin jihar Katsina, a arewacin tarayyar Najeriya. Sunan mahaifinshi Harɗo Adamu mahaifiyarshi kuma Hajiya Zulaihatu Musa.[4] Mahaifinshi shi ne shugaban ƙauyen Dumurkol, ya haifi yara ashirin da mata daban-daban, Muhammadu Buhari shi ne yaro na ƙarshe a gurin Hajiya Zulaihatu Harɗo, wadda cikakkiyar bahaushiya ce 'yar kabilar Haɓe na Hausawa. Kuma shi ne yaro na ƙarshe a gun babanshi da mamarshi wato Auta. Babanshi da kakanshi cikakkun Fulani ne.[4]  Muhammadu Buhari ya rasa mahaifansa a lokacin yana da shekara goma (10), abinda kawai zai iya tinawa kawai shi dai mahaifinsa dogo ne kuma mai tsayin halitta.Mahaifiyarsa Hajiya Zulaihatu ita ce ta raine shi har ya girma ya yi makaranta.(p2 Ana kiran Muhammadu Buhari da “Leko” kamar Gambo kenan da Hausa saboda an haifeshi ne bayan mahaifiyarsa ta haifi 'yan biyu kuma dukansu sun rasu, sai aka haifeshi.[5] Sunan Muhammadu Buhari ya samo asali ne daga sunan shahararren masanin ilmin Hadisi wato Muhammad Al-Bukhari wannan ne ya sa duk mai suna Buhari, to cikakken sunan shi ne Muhammadu Buhari. Wannan ya saɓawa tunanin mafiya yawan jama'a cewa Muhammad dan Buhari ne. Shi ya sa a tarihin Shugaba Muhammadu Buhari, ba a jin sunan Mahaifinsa.[1]

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Muhammadu Buhari 2015.jpg

Muhammadu Buhari ya halarci Katsina Model School a shekarar 1953.[5] A shekarata alif 1955, kuma an mayar da makarantar Kankiya, lokacin Muhammadu Buhari yana shekarar karshe.[6] Daga nan sai ya tafi Provincial Secondary School a shekarata alif 1956, ya shiga gidan soja ne a shekarata 1962.[7]. Kuma Buhari ya zauna tare da danshi mai suna Dauda Daura, a lokacin dan nashi yana karantarwa a Mai Aduwa Primary School. Banda karatun addinin da ya yi a gida Buhari ya shiga makarantar firamare ta Daura ta Mai’aduwa, sannan ya je Katsina Model School a shekaran 1953, sai kuma Katsina Provincial Secondary School (wadda ake kira Government College Katsina a yanzu) daga shekarar 1956 har zuwa shekarar 1961.[1]

Aikin soja[gyara sashe | gyara masomin]

Muhammadu Buhari a lokacin yakin neman zabe.

Daga nan ne ya shiga makarantar sojoji ta Nigerian Military Training College wadda akafi saninta da NMS Zaria da ke kaduna, inda ya fara aikin soja. Buhari ya ci gaba da karatu a ciki da wajen kasar, a makarantu wadanda suka hada da,: Defence Services Staff College, Wellington, India, a shekara ta 1973. Sa'annan kuma Army Mechanical Transport School borden a birnin Borden, na kasar Birtaniya. Karatunsa na karshe shi ne na The United States Army War College (USAWC) a Carlisle, na jihar Pennsylvania, a kasar Amurka inda ya sami digiri na biyu ko kuma Masters Degree a ilmin sanin dabarun yaki ko Strategic Studies.[1][8]

Kafin ya zama shugaban kasa a karon farko a shekarar 1983, Buhari ya riƙe wasu manya manyan muƙaman gwamnati waɗanda suka haɗa da gwamnan jihar Arewa maso gabas, da Ministan man fetur da albarkatun kasa a lokachin mulkin soji.[1]

A shekarar 1983 Buhari da abokansa cikin rundunar sojojin kasar nan suka yi juyin mulki wa zababben gwamnatin Shehu Shagari bayan zargin ta da lalata tattalin arzikin kasar sanadiyyar cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikatan gwamnati da 'yan siyasa.[1]

A cikin gwamnatin da ya jagoranta harna tsawon watanni 20, muhimman lamura daya aiwatar a bangaren tattalin arziki shi ne chanza launin kudaden kasar, don raya bankunan da kuma lalata shirin attajiran kasar wadanda suka bobboye kudade a wurare daban-daban. Har ila yau, Buhari ya ki amincewa da bukatar Bankin lamuni ta duniya IMF na ya rage darajar Naira da kashi 60%, a maimakon haka ya takaita shigar da kayayyaki daga kasashen waje wadanda zasu cutar da tattalin arzikin kasar da sauransu.[1]

A kokarin gyara halayen yan Najeriya kuma, Buhari ya jefa yan siyasa da dama cikin gidan kaso tare da tuhumar su a kan sata da cin hanci da rashawa, sannan ya gabatar da shirin yaki da rashin da’a da nufin kyautata halayen yan Najeriya. Sai dai kamar yadda aka zata ya sha suka daga bangaren kungiyoyi da kasashen duniya kan take hakkin bil’adama musamman ma yan jaridu.[1]

Bayan an masa juyin mulki a shekarar 1985 Buhari, gwamnatin Babangida ta tsareshi na wasu shekaru.[1]

Sai kuma bayan darewar marigayi Sani Abacha kan kujerar shugabancin kasar ya kafa hukumar PTF wacce ta gudanar da ayyukansa da karin kudaden man fetur da aka yi a shekarar 1994. Inda ya mikawa Buhari shugabancin hukumar.[1] PTF ta yi rawar gani a kyautata rayuwar yan Najeriya, PTF ta kyautata bangarori da dama a Najeriya wadanda suka hada da makarantu, kiwon lafiya, hanyoyi da sauransu. Wanda yan Najeriya basu manta da it aba.[1]

Rayuwar Muhammadu Buhari[gyara sashe | gyara masomin]

shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da yake zantawa da Sakataren Kasashen Waje na Amurka John Kerry a yayin wani taro da kasar Burtaniya ta shirya a Lancaster don yaki da cin hanci da rashawa

Buhari ne na 23 a cikin yayan mahaifinsa malam Adamu, sannan ya tashi a hannun mahaifiyarsa mai suna Zulaihatu bayan rasuwar mahaifinsa yana dan shekaru 4 a duniya.

Banda karatun addini a gida Buhari ya shiga makarantar firamare ta Daura da Mai’adua, sannan ya je Katsina model school a shekara ta alif 1953, sai kuma Katsina Provincial Secondary School (wanda ake kira Government College Katsina a yanzu) daga shekara ta alif 1956 zuwa shekarar alif 1961..

Aikin soja[gyara sashe | gyara masomin]

Daga nan ne ya shiga makarantar soje ta Nigerian Military Training College da ke kaduna , inda ya fara aikin soja. Buhari ya ci gaba da karsatu a ciki da wajen kasar, a makarantu wadanda suka hada da,: Defence Services Staff College, Wellington, India, a shekara 1973. Sannan Army Mechanical Transport School a birnin Borden, na kasar Britania .Karatunsa na karshe shi ne na The United States Army War College (USAWC) a Carlisle, na jihar Pennsylvania, a kasar Amurka inda ya sami digiri na biyu ko kuma Masters Degree a ilmin sanin dabarbarun yaki ko Strategic Studies.

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Kafin ya zama shugaban kasa a karon farko a shekarar 1983, Buhari ya rike wasu manya manyan mukaman gwamnati wadanda suka hada da gwamnan jihar Arewa maso gabas, da ministan man fetur da albarkatun kasa.

A shekarar ta alif 1983 Buhari da abokansa cikin rundunar sojojin kasar suka yi juyin mulki wa zabebben gwamnatin shehu shagari bayan zargin ta da lalata tattalin arzikin kasar sanadiyyar cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikatan gwamnati da yan siyasa.

A cikin gwamnatin da ya jagoranta na watannin 20, muhimman al’amuran daya aiwatar a bangaren tattalin arziki shi ne ya chanza launin kudaden kasar, don raya bankunan da kuma lalata shirin attajiran kasar wadanda suka bobboye kudade a wurere daban daban. Har’ila yau Buhari ya ki amincewa da bukatar Bankin lamuni ta duniya IMF na ya rage darajar Naira da kashi 60%, a maimakon haka ya takaita shigar da kayayyaki daga kasashen waje wadanda zasu cutar da tattalin arzikin kasar da sauransu.

A kokarin gyara halayen yan Nigeria kuma, Buhari ya jefa yan siyasa da dama cikin gidan kaso tare da tuhumar su da laifin sata da cin hanci da rashawa, sannan ya gabatar da shirin yaki da rashin da’a da nufin kyautata halayen yan Nigeria. Sai dai kamar yadda ake zata ya sha suka daga banagren kungiyoyi da kasashen duniya kan take hakkin bil’adama musamman yan jaridu.

Bayan an masa juyin mulki a shekarar ta alif 1985 Buhari, gwamnatin Baban gida ta tsareshi na wasu shekaru.

Bayan Mutuwar Abacha a shekararta alif 1998 da kuma dawowar Dimokaradiyya a shekarar 1999, Buhari ya shiga harkokin siyasa da kuma neman takarar shugabancin kasar a shekaru 2003, 2007, 2011, amma ba tare da samun nasara ba, sai a karo na 4 wato a wannan shekara ta 2015.[9]

Idan muka dubi halin da kasar take ciki a lokacinda Buhari ya sake dawowa a matsayin shugaban kasa a karo na biyu, zamu ga cewa matsalolin da kasar take fama da su sun ninninka wanda ya tarar a shekara ta 1983. Sai dai ayi masa fatan alheri a cikin gagarumin aikin da ke gabansa.[1]

Shugaban PTF[gyara sashe | gyara masomin]

Sai kuma bayan darewar marigayi Sani Abacha kan kujerar shugabancin kasar ya kafa hukumar PTF wacce ta gudanar da ayyukanta da karin kudaden man fetur da aka yi a shekarar 1994. Inda ya mikawa Buhari shugabancin hukumar.

PTF ta yi rawar gani a kyautata rayuwar yan Nigeria, PTF ta kyautata bangarori da dama a Nigeria wadanda suka hada da makarantu, kiwon lafiya, hanyoyi da sauransu. Wanda yan Nigeria basu manta da it aba.

lokacin da Muhammad buhari yayi nasarar zabe a shekara 2015

Bayan Mutuwar Abacha a shekara ta 1998 da kuma dawowar Dimokaradiyya a shekarar 1999, Buhari ya shiga harkokin siyasa da kuma neman takarar shugabancin kasar a shekaru 2003, 2007, 2011, amma ba tare da samun nasara ba, sai a karo na 4 wato a cikin shekara ta 2015.

Mutum Mutumin Shugabar Kasar Najeriya Kenan. Muhammad Buhari.

Idan muka dubi halin da kasar take ciki a lokacin da Buhari ya sake dawowa a matsayin shugaban kasa a karo na biyu, zamu ga cewa matsalolin da kasar take fama da su sun ninninka wanda ya tarar a a shekara ta 1983. Sai dai ayi masa fatan alheri a cikin gagarumin aikin da ke gabansa.

Iyali da dangi[gyara sashe | gyara masomin]

Buhari ne ɗa na 23 a cikin 'ya'yan mahaifinsa malam Adamu, sa'annan ya tashi a hannun mahaifiyarsa mai suna Zulaihatu bayan rasuwar mahaifinsa yana ɗan shekaru 4 a duniya.[1]

Dangi[gyara sashe | gyara masomin]

Iyali[gyara sashe | gyara masomin]
matan Muhammadu buri na biyu ke nanShugaba Muhammadu Buhari ya auri mata biyu a rayuwarsa. Akwai Safinatu Yusuf wacce ita ce matarsa ta farko da ya aura (daga 1971 zuwa 1988) kuma ta rasu ta bar manyan 'ya'ya kafin ya auri Aisha Halilu a shekarar 1989

'Ya`ya

Muhammad Buhari yana da 'ya'ya guda goma Wanda suka haɗa da:

 • Zulaihat (marigayiya)
 • Fatima
 • Musa (marigayi)
 • Hadiza
 • Safinatu
 • Aisha
 • Halima
 • Yusuf
 • Zarah
 • Amina

Bibiliyo[gyara sashe | gyara masomin]

 • Atim, Tyodzua. (1998) Muhammadu Buhari: The Making of a Legend. ISBN: 778-31385-1-0

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. 1.00 1.01 1.02 1.03 1.04 1.05 1.06 1.07 1.08 1.09 1.10 1.11 1.12 https://www.britannica.com/biography/Muhammadu-Buhari
 2. https://www.globalsecurity.org/military/world/nigeria/muhammadu-buhari.htm
 3. https://www.aljazeera.com/tag/muhammadu-buhari/
 4. 4.0 4.1 Tim, Tyodzua. (1998) Muhammadu Buhari: The Making Of a Legend.p. 1. ISBN 778-31385-1-0
 5. 5.0 5.1 Tim, Tyodzua. (1998) Muhammadu Buhari: The Making Of a Legend.p.5. ISBN 778-31385-1-0
 6. Tim, Tyodzua. (1998) Muhammadu Buhari: The Making Of a Legend.p. 6. ISBN 778-31385-1-0
 7. Tim, Tyodzua. (1998) Muhammadu Buhari: The Making Of a Legend.p.7. ISBN 778-31385-1-0
 8. https://ke.opera.news/ke/en//393cb33173db32ebb97138b1f7ab9236
 9. Shugaban kasa