Sani Abacha

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Muhammad Sani Abacha tsohon janar din soja kuma ɗan siyasa a Nijeriya. An haife shi a shekara ta 1943 a garin Kano, Arewacin Najeriya (a yau jihar Kano); ya mutu a shekara ta 1998. Sani Abacha shugaban kasar Nijeriya ne daga Nuwamba shekarar 1993 zuwa watan Yuni shekara ta 1998 (bayan Ernest Shonekan - kafin Abdulsalami Abubakar).