Kano (birni)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Kano
KanofromDalaHill.jpg
birni
ƙasaNijeriya Gyara
babban birninjihar Kano Gyara
located in the administrative territorial entityjihar Kano Gyara
coordinate location12°0′0″N 8°31′0″E, 12°0′0″N 8°31′0″E Gyara
located in time zoneUTC+01:00 Gyara

Kano na daya daga cikin manyan birane a kasar Hausa. Kano itace cibiyar kasuwanci ta najeria gaba daya, jihar Kano tana da kananan hukumomi guda arba'in da hudu. Kano garine da yake da masarauta mai dunbun tarihi, Masarauta ce mai kwarjini a cikin kasashen Hausa da kewaye. Haka kuma Kano gari ne babba wanda mazauna cikin sa suna magana da harshen Hausa. kano shine gari mafi yawan jama'a a nijiriya gaba daya.

Cikin birnin kano akwai kofofi kamar haka Kofar Gadon Kaya, Kofar Famfo, Kofar Na'isa, Kofar nasarawa, Sabuwar Kofa, Kofar Mazugal, Kofar Dawanau, Kofar Dan Agundi, Kofar Dukawoya, Kofar Ruwa, Kofar Kansakali, Kofar Mata.

Yawan mutanen da suke garin Kano ya haura kimanin mutane miliyan goma (10,000,000) a kidayar da aka yi a shekara ta alif dubu biyu da shida (2006). Kano tana da matukar tasiri a yawan mutane a Najeriya, saboda ita ce ta fi kowace jiha yawan mutane a Najeriya. Idan ka zo Kano za ka samu mutane daga ko'ina a fadin duniya, tun daga na kudancin Najeriya, zuwa kasashen dake makwabtaka da Najeriya, haka kuma za ka tarar da mutanen Sin, wato (china), da kuma na kasashen Larabawa har da turawan yammacin duniya. Mutanan kano sun sha hara wajin addini sosai.

Kano ta yi suna wajen kasuwancin da ta bunkasa a kai, har ya zamana ana cewa da ita Cibiyar Kasuwanci, haka kuma tarihin Kano ya nuna daman can Kano tana da suna wurin cinikayya tsakaninta da mutanen gabas ta tsakiya.

Tarihin Kano[gyara sashe | Gyara masomin]

Anan za'a sa takaitaccen tarihin Kano

Mutanen Farko[gyara sashe | Gyara masomin]

Kano Jalla babbar Hausa ta dabo tumbin giwa ko da me ka zo amfika wannan shine kirarin da akewa wanna katafaren gari. Idan ana zancen suwane sukafara zama a kano to tarihi zai iya cewa kamar yanda Allah subhanahu wata'ala yayi mutane a sauran sassan Duniya hakama ya ajiye bayin sa a garin Kano.

sai dai kabilu da dama sun zo kasar kano kamar su Madatai da Dala. zuwan wadannan kabilu yakara habaka garin Kano kabilar Madatai ta riga Kabilar Dala zuwa Kano da suka zo wannan gari mai Albarka sun sami wasu kabilu masu yawa a Kano Amma ana ce da su Kabilun Kwararrafa.

Sarakunan Kano[gyara sashe | Gyara masomin]

Bayani game da Sarakunan da suka mulki Kano, izuwa wannan lokacin

Kano a matsayin Jiha[gyara sashe | Gyara masomin]

Tarihin Kano tun da ta zama Jiha a Kasar Najeria, cigaban da ta samu, da kuma matsalolin da take fuskanta