Abdullahi Umar Ganduje

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Abdullahi Umar Ganduje
gwamnan jihar Kano

Mayu 2015 -
Rabiu Kwankwaso
Rayuwa
Cikakken suna Abdullahi Umar Ganduje
Haihuwa Dawakin Tofa, 25 Disamba 1949 (72 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Yan'uwa
Abokiyar zama Hafsat Ganduje
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Jami'ar Ibadan
Jami'ar Bayero
Government College, Birnin Kudu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa National Party of Nigeria (en) Fassara

[[File:GG Family.jpg| An haifi Abdullahi Umar a kauyen Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa, jihar Kano a cikin kasar Najeriya a shekarar 1949. Ya fara karatun Qur'ani da Islamiyya a kauyensa inda ya samu ilimin addini. Daga nan kuma ya shiga makarantar firamare ta Dawakin Tofa daga shekarar 1956 zuwa shekarar 1963. Ganduje ya fara makarantar sakandaren Birnin Kudu daga shekarar 1964, kuma ya kammala ta a shekarar 1968. Bayan nan Ganduje ya shiga makarantar horar da malamai da ke Kano, tsakanin shekara ta 1969 zuwa shekarar 1972 inda ya shiga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jahar Kaduna Ya kammala karatun jami'a a fannin ilimi cikin shekarar ta 1975. A shekarar 1979 ne kuma ya kammala digirinsa na biyu daga Jami'ar Bayero dake Kano. Sannan ya kara komawa Jami'ar Ahmadu Bello Zariya daga shekarar 1984 zuwa shekara ta 1985 don karantar ilimin tafiyar da gwamnati. A shekara ta 1993 ne ya samu digirin-digirgir daga Jami'ar Ibadan.


Ganduje ya shiga jam'iyyar NPN a jamhuriyya ta biyu sannan ya zama mataimakin sakatare na jihar Kano daga shekara ta 1979 zuwa shekarar 1980. Ya tsaya takarar wakiltar Kano a zauren majalisar wakilai a shekarar 1979 a jam'iyyar NPN amma bai yi nasara a zaben ba. A shekarar 1998 ya shiga jam'iyyar People Democratic Party (PDP) inda ya nemi jam'iyyar ta tsayar da shi takarar gwamna, amma bai yi nasara ba bayan da PDP ta tsayar da Rabi'u Musa Kwankwaso. An zabi Ganduje a matsayin mataimakin Gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003. Baya ga haka, an nada shi a matsayin kwamishinan kananan hukumomi. Daga shekarar 2003 zuwa 2007, ya rike mukamin mai bai wa ministan tsaro shawara na Najeriya, wato Rabi'u Kwankwaso, An zabi Ganduje a matsayin shugaban kwalejin fasaha a Ado Ekiti a 2008 daga nan kuma aka nada shi a matsayin babban sakataren Hukumar Kula da Tafkin Chadi da ke Ndjamena. Ya kuma kasance daga cikin wadanda suka halarci taron yi wa tsarin siyasa a Najeriya garambawul a 2006. Kwankwaso da Ganduje sun kuma yi rashin nasara a zaben da suka nemi ta-zarce inda Malam Ibrahim Shekarau ya samu nasara.


An sake zabar Kwankwaso da Ganduje ranar 27 ga watan Afrilun 2011 inda aka rantsar da su ranar 29 ga Mayun 2011 domin karasa zangon mulkinsu na biyu.[1][2]

Badakalar cin hanci[gyara sashe | Gyara masomin]

Ganduje na fuskantar tuhuma daga al'umma daban-daban a kan wani bidiyo da wata jaridar yanar gizo, wato 'Daily Nigerian' ta fitar, inda aka ga Gandujen na karbar daloli daga hannun wani ɗan kwangila yana tura su aljihun babban rigarsa, ɗan kwangilan na fadi masa cewar kaga haka yafi rufin asiri. Amma gwamnati ta yi mirsisi ba tare da tace komai ba akan hakan, sai majalisar jahar ta nemi shugaban jaridar Ja.afar Ja.afar da ya gurfana a gabanta dan tabbatar da sahihancin bidiyon daya fitar, daga nan sukai watsi da batun, kuma da akwai wani lauya Mai zaman kansa wato Audu Bulama Bukarti wanda a lokacin da abun ya faru Yana kasar Ingila wanda ya fada cewa ya tambayi mukaddashin hukumar EFCC wato Ibrahim Magu Kuma ya tabbatar mai da wannan bidiyon na gaskiya ne.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. Kolade, Adeyemi (2 December 2014). "Ganduje scales screening in Kano governorship race". The Nation. Retrieved 16 October 2018.
  2. "Archived copy". Archived from the original on 13 April 2015. Retrieved 2015-05-24.CS1 maint: archived copy as title (link).