Jump to content

Hafsat Ganduje

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Hafsat Ganduje
Rayuwa
Haihuwa jihar Kano, 28 Disamba 1960 (64 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Abokiyar zama Abdullahi Umar Ganduje
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a Malami
Hajia hafsat ganduje
Hajia hafsah da mijin ta ganduje

Hajiya Hafsat Abdullahi Ganduje (wadda aka fi sani da Gwaggo) 'yar Najeriya ce, farfesa, Masaniyar Harkar Siyasa a Najeriya kuma matar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ce, sannan kuma memba ce a jam'iyyar All Progressive Congress.[1]

Tarihin Rayuwa da Karatu

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Hafsat Ganduje a jihar Kano.Ta halarci makarantar firamare ta Malam Madori, da makarantar firamare ta kwana a jihar Kano, da Kwalejin Mata ta garin Kano. Hafsat Ganduje ta samu digiri na farko na fannin Kimiyyan Ilimi, acikin shekara ta dubu daya da Dari Tara da tamanin da daya (1981), ta zama Jagoran Ilimin halin dan Adam, a shekara ta alif dari tara da chasain da biyu (1992), ta zama Jagora na Kasuwanci, a shekara ta dubu biyu da hudu (2004), ta zama Doctor na fannin Falsafa a cikin Gudanarwa da Tsare-tsare, a shekara ta dubu biyu da Sha biyar(2015) duk daga Jami'ar Bayero, Kano.[2]

Ganduje ta fara aiki ne a matsayin malama a aji sannan bayan ta zama shugabar makaranta, daga baya ta zama malama a Kwalejin Ilimi ta Jami'ar Bayero, Kano, Najeriya. Jami'ar Maryniam Abacha ta Nijar ce ta daga darajar ta zuwa matsayin Farfesa a shekara ta (2019).

Ita abokiyar zama memba ce a Cibiyar Gudanarwa ta kasar Nijeriya kuma ta samu lambobin yabo da yawa.

Aure da Iyali

[gyara sashe | gyara masomin]

Hafsat, ta auri Alhaji Abdullahi Umar Ganduje wanda a yanzu haka shi ne gwamnan Jihar Kano, sannan Allah ya albarkace su da ‘ya’ya.

Duk da cewa Hafsat ba ta da ofis din amatsayin matar gwamna da ake kira ‘First Lady’, amma ta himmatu a dashin kanta wajen fito da shirye-shirye da tsare-tsaren da suke samar wa mata ayyukan dogaro da kai, gangamin samar da tallafin kayan karatu, kekunan dinki, tallafin kudaee domin mata su fara gudanar da ‘yan kananan sana’o’in dogaro da kai agarin Kano, dubban daruruwan mata ne suka amfana da kokarinta da azamarta wacce suke kiran hakan a matsayin jinkai a gare su.[3]

An yi ta yada jita-jitan cewa Hafsat tana kaka-gida cikin sha’anin mulkin mijinta wanda ake cewa tana bayyana ra’ayinta ko lamunce ma wadanda take son a basu kwangila ko naɗin mukamai, amma jami’an gwamnatin jihar sun sha karta wannan batun da cewa ba ta katsalandan wa gwamnan a sha’anin tafiyar da mulkin jihar Kano.

 

  1. https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/484916-after-shunning-efcc-invitation-gandujes-wife-attends-sons-graduation-in-london.html?tztc=1
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-07. Retrieved 2023-07-07.
  3. https://www.rfi.fr/ha/najeriya/20211005-jami-an-efcc-sun-kame-matar-gwamnan-kano-hafsat-ganduje