Birnin Kudu
Birnin Kudu | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jihar Jigawa | |||
Tsarin Siyasa | ||||
Majalisar zartarwa | supervisory councillors of Birnin Kudu local government (en) | |||
Gangar majalisa | Birnin Kudu legislative council (en) | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Lambar aika saƙo | 721101 | |||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Birnin Kudu gari ne kuma karamar hukuma ce a kudancin jihar Jigawa ta Najeriya, mai tazarar kilomita 120 kudu maso gabas da Kano. A shekarar 2006 garin Birnin Kudu yana da yawan jama'a 419,800 kuma ita ce karamar hukuma mafi yawan al'umma a jihar.[1]
Birnin Kudu tsohon birni ne mai cike da tarihi da ya yi suna da duwatsu da zane-zane da aka samu a wasu daga cikinsu tun shekaru aru-aru kafin a yi wa Arewacin Najeriya mulkin mallaka da kafa Hukumar ‘Yan Kasa (NA). Birnin ya kasance hedikwatar NA a lokacin mulkin Ingila kuma ya kasance babban birnin karamar hukumar Birnin Kudu.
Bayan haka garin birnin kudu Wanda lokacin da ana hade da jihar kano local government ce wacce tahada dayawa acikinta tundaga wudil kwanar simaila takai dutse kiyawa buji dakuma gwaram.[2]
Kuma ayanzu haka garin birnin kudu wanda adasunan garin shine BODAN yana daga cikin garinda matasa maza da mata suka rungumi kasuwanci da sana'o'in hannu
Birnin Kudu ita ce karamar hukumar da ta fi yawan al'umma a jihar Jigawa bisa ga kidayar jama'a a shekarar 2006, duk da cewa birnin yana tafiyar hawainiya wajen samar da ababen more rayuwa. Haka kuma gari ne da karamar hukumar Gwaram da Buji suka rabu a shekarar 1996.
Gida ne daya daga cikin tsofaffin makarantu a Arewacin Najeriya, Kwalejin Gwamnati ta Birnin Kudu, daga nan ne aka samu Shugabannin Arewa da ‘yan kasuwa da dama da suka hada da Alhaji Aliko dangote (mai kudi a Afirka).
A siyasar baya-bayan nan Birnin Kudu ya samar da gwamnoni biyu na jihar Jigawa (Alh Ali Sa'adu, gwamnan farar hula na farko) da kuma Alh Sule lamido, wanda ya yi gwamnan jihar jigawa daga ranar 29 ga watan Mayu 2007 zuwa 29 ga watan Mayu 2015.
Birnin Kudu yana da unguwannin siyasa guda 11, wato Kantoga, Kangire, Kwangwara, Kiyako, Sundumina, Surko, Lafiya, Unguwar 'ya, Yalwan dama, Birnin Kudu, da Wurno.
halin yanzu Siraj Muhammad Kantoga memba ne mai wakiltar Birnin Kudu a majalisar dokokin jihar Jigawa, 2015 zuwa yau.
BIRNINKUDU ROCK ARTS AND PINTING An gano zanen dutsen Birnin Kudu a shekarar 1950-1955 a Birnin Kudu. Yana da sananne kamar samun tarin tsoffin gongiyoyi na dutse waɗanda aka yi amfani da su azaman kayan kida da ƙararrawa na faɗakarwa
Hotunan dutsen Birnin Kudu na ɗaya daga cikin tabbatattun daɗaɗɗen wayewar ɗan adam a yankin Saharar Afirka. Ana kyautata zaton cewa wadannan zane-zane sun wuce shekaru dubu biyu da suka wuce, wadanda ke cikin shimfidar lu'u-lu'u na Arewacin Najeriya.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "The World Gazetteer". Stefan Helders. Retrieved 2007-03-27.[dead link]
- ↑ tarihin garin birnin kudu