Jigawa
It has been suggested to merge this page with Jihar Jigawa.








Jigawa: Jaha ce dake Arewa maso Yammacin Tarayyar Najeriya. An kafa jahar Jigawa ne a ranar ashirin da bakwai 27 ga watan Agustan shekarar alif.dubu daya da dari Tara da Cassa,in da daya 1991[1] daga jihar Kano a lokacin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Babban birnin jihar shi ne Dutse.[2] Jigawa ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijar da jihar Yobe a arewa maso gabas, Bauchi a kudu maso gabas da kudu, Kano a kudu maso yamma da kuma Katsina a arewa maso yamma.
Tattalin Arziki:
[gyara sashe | gyara masomin]Tattalin Arzikin jahar Jigawa yana da alaƙa da ayyukan bangaranci na yau da kullum tare da aikin noma a matsayin babban aikin tattalin arziki. Fiye da kashi 80% na al'ummar jihar sun tsunduma cikin noma da kuma kiwon dabbobi. Ana gudanar da ciniki da kasuwanci na kanana da matsakaita, musamman a harkar noma, da kiwo da sauran kayayyakin masarufi. Jigawa ta shahara a fannin Noma da kiwo, Manyan amfanin gona na jihar sun haɗa da gyada, dawa, gero, shinkafa, Ridi, da kuma Zobo (yakuwa).a fannin kiwo kuma, Kiwon shanu, awaki, da tumaki ya yaɗu sosai a jihar.
Fadin Kasa da yawan Jama'a:
[gyara sashe | gyara masomin]Jahar Jigawa Tana da fadin kasa kimanin muraba'in kilomita dubu ashirin da uku, da ɗari da hamsin da hudu (23,154) da yawan jama’a kimanin miliyan biyu da dubu dari takwas da ashirin da tara da dari tara da ashirin da tara (kidayar yawan jama'a shekara ta 1991). Babban birnin jahar shine Birnin Dutse.

Jahar Jigawa tana da iyaka da jahohi hudu dake Najeriya, su ne: jahar Bauchi, jahar Kano, jahar Katsina,da kuma jahar Yobe. [3] [4].
Harsuna:
[gyara sashe | gyara masomin]
Jigawa wani sassa ne na kasar , a Arewa maso yammacin najeriya .Hausa hausawa sune mafi rinjaye a jihar Jigawa sannan akwai Fulani [5]da Mangawa da Badawa da Ngizimawa wadanda yarukan kanuri ne. Mafiyawancin su suna a kananan hukumomin Birniwa, Guri da Kiri kasamma.

.
Masarautun:
[gyara sashe | gyara masomin]Tsarin masarautar gargajiya a Jihar ya kasu zuwa masarautun guda biyar kowacce tana da basaraken gargajiya mai suna sarki (sarki) da yake gudanarwa tare da Hakimai da dagatai da masu unguwanni suna taimaka musu. Sarakuna da Hakimai, ba kamar sauran masu rike da madafun iko ba, ba sa gudanar da harkokin siyasa, sai dai a matsayin masu kula da al’adu da masu ba gwamnati shawara kan harkokin gargajiya da na addini. Duk sarakunan masu rike da mukamai ne ajin farko.
- MASARAUTAR HADEJIA[7]
- MASARAUTAR GUMEL.
- MASARAUTAR DUTSE.
- MASARAUTAR RIGIM.
- MASARAUTAR KAZAURE.
GWAMNONI
[gyara sashe | gyara masomin]https://en.m.wikipedia.org/wiki/List_of_governors_of_Jigawa_State.
SHUWAGA BANNIN KANANUN HUKUMOMIN JIHAR JIGAWA:
[gyara sashe | gyara masomin]Wannan jerin sunayen dake gasa, shine jerin sunayena Shuwaga bannin kananun Hukumomi guda ashirin da bakwai (27) dake a Jihar Jigawa a wannan shekara ta alif dubu biyu da ashirin da hudu miladiyya (2024.)
- Hon. Baffa Shine, Shugaban karamar Hukumar Auyo.
- Hon. Lawan Ismail Shugaban karamar Hukumar Babura.
- Hon. Umar Baffa Shugaban karamar Hukumar Birni wa.
- Hon. Magani Yusif Gigo Shugaban karamar Hukumar Birnin Kudu.
- Hon. Abdullahi Sule YariShugan karamar Hukumar Buji.
- Hon. Bala Usman Shamo Shugaban karamar Hukumar Duste.
- Hon. Sani Muktar Madaka Shugaban karamar Hukumar Garawa.
- Hon. Alh. Mudassir Musa Shugaban karamar Hukumar Garki.
- Hon. Ahmad Rufai Gomel Shugaban karamar Hukumar Gumel.
- Hon. Musa shuaibu Guri Shugaban kagaramar Hukumar Guri.
- Hon.Zahradden Abubakar Shugaban karamar Hukumar Gwaram
- Hon. Saleh Ahmad Zauma Shugaban karamar Hukumar Gwiwa.
- Hon. Abdullahi Bala Umar (TO)Shugaban karamar Hukumar Hadejia.
- Hon. Adu Mai unguwa Aujara Shugaban karamar Hukumar Jahun.
- Hon. Muhammad Saminu Yahaya Shugaban karamar Hukumar Kafin Hausa.
- Hon. Alh, Idris Mati Haruna Shuganban karamar Hukumar Kaugama.
- Hon. Arc Muhammad Muktar (mni) Shugaban karamar Hukumar Kazaure
- Hon. Alhaji Isah Matara Shugaban karamar Hukumar Kiri kasamma.
- Hon. Nasiru Ahmad Kiyawa Shugaban karamar Hukumar Kiyawa
- Hon. Alh, Uzairu Na Dabo Shugaban karamar Hukumar Mai gatari.
- Hon. Alhj, Usain Umar Shugaban karamar Hukumar Malam Madori.
- Hon. Adamu Sarki Miga Shugaban karamar Hukumar Miga.
- Hon. Alh, Shehu Suke Ido Shugaban karamar Hukumar Ringim
- Hon. Alh, Tukur Muhammad Ali Shugan karamar Hukumar Roni
- Hon. Saleh Ahmad Dan zumo Shugaban karamar Hukumar Sule Tankarkar.
- Hon. Baffa Yahaya Taura Shugaban karamar Hukumar Taura.
- Hon. Alh, Mubarak Ahmad Shugaban karamar Hukumar yan kwashi.[8]
Kananan Hukumomin jihar Jigawa:
[gyara sashe | gyara masomin]Jihar Jigawa tana da kananan Hukumomi guda ashirin da bakwai (27). Kananan Hukumomin kuwa su ne:
- Auyo.
- Babura.
- Biriniwa.
- Birnin Kudu
- Buji.
- Dutse.
- Gagarawa.
- Garki.
- Gumel.[9]
- Guri.
- Gwaram.
- Gwiwa.
- Hadejia.
- Jahun.
- Kafin Hausa.
- Kaugama.
- Kazaure.
- Kiri Kasamma.
- Kiyawa.
- Maigatari.
- Malam Madori.
- Miga.
- Ringim.
- Roni.
- Sule Tankarkar.
- Taura.
- Yankwashi
- Mai gatari
-
Masarautar Gumel
-
Masarautar Dutse
-
Masarautar Ringim
-
Masarautar Hadejia
-
Masarautar Kazaure
Ma'adanai:
[gyara sashe | gyara masomin]Ma'adanai da ake samu sun hada da;
- Laka:
Bibiliyo;
[gyara sashe | gyara masomin]- Bello, Ahmadu, Sir, a shekara ta 1910-1966. (1999). Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardauna of Sokoto : his thoughts and vision in his own words : selected speeches and letters of the great leader. Nchi, Suleiman Ismaila, Mohammed, Samai̕la Abdullahi. Makurdi: Oracle. ISBN 978-34637-2-1. OCLC 44137937.
Manazarta:
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Jigawa State - Wikipedia
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://gazettengr.com/nuc-accredits-10-programmes-at-federal-university-dutse/&ved=2ahUKEwiyr4ajwPCGAxW8QUEAHSHFC9kQxfQBKAB6BAgIEAI&usg=AOvVaw0P98KYz8m_E8H_1DZLQ5IO
- ↑ https://www.britannica.com/place/Jigawa
- ↑ https://www.familysearch.org/wiki/en/Jigawa_State,_Nigeria_Genealogy
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://guardian.ng/the-gulf-between-fulani-rulers-and-herders/&ved=2ahUKEwiQz-X5wPCGAxXBQkEAHULqNw8QxfQBKAB6BAgNEAI&usg=AOvVaw3_dt1-fWHaREhMjJURdWVA
- ↑ "Nigeria". Ethnologue (22 ed.). Retrieved 2020-01-10.
- ↑ https://hausa.leadership.ng/tarihin-hadejia-da-sarakunanta-6/
- ↑ https://www.jigawastate.gov.ng/2chairmen
- ↑ https://en.wikipedia.org/wiki/Gumel
| Jihohin Najeriya |
| Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |
/gallery>
Bibiliyo
[gyara sashe | gyara masomin]- Bello, Ahmadu, Sir, a shekara ta alif dabu daya da dari Tara da goma 1910-1966. (1999). Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardauna of Sokoto : his thoughts and vision in his own words : selected speeches and letters of the great leader. Nchi, Suleiman Ismaila, Mohammed, Samai̕la Abdullahi. Makurdi: Oracle. ISBN 978-34637-2-1. OCLC 44137937.