Borno

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Jihar Borno
Sunan barkwancin jiha: Gidan zaman lafiya.
Wuri
Wurin Jihar Borno cikin Nijeriya.
Ƙidaya
Harsuna Kanuri, Margi, Bura, Shuwa Arab, Fulani, Hausa
Gwamna Babagana Umara Zulum
Jam'iyyar Shiyasa All Progressive Congress (APC)
An kirkiro ta 1976
Baban birnin jiha Maiduguri
Iyaka 57,799km²
Yawan Alumma
2006 (ƙidayar yawan jama'a)

5,925,668
ISO 3166-2 NG-BO

Jihar Borno jiha ce a ƙasar Najeriya. Tana da yawan fili kimanin kilomita murabba’i 57,799 da yawan jama’a miliyan biyar da dubu dari tara da ashirin da biyar da dari shida da sittin da takwas (ƙidayar yawan jama'a shekara 2006). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Maiduguri. Babagana Umara Zulum shi ne gwamnan jihar tun zabensa da akayi a shekara ta 2019 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Usman Mamman Durkwa. Dattijan jihar su ne: Yusuf Buratai, Baba Garba, Ali Madu Sheriff, Muhammad Indimi, Abba Kyari da Mohammed Ali Ndume.

Jihar Borno tana da iyaka da misalin jihhohi uku ne: Jihar Adamawa, Jihar Gombe kuma da Jihar Yobe, sannan ta hadu da kasashe uku wadanda suka hada da Jamhoriyar Nijar, Kamaru da Chadi. [1] [2]

Kananan Hukumomin Borno[gyara sashe | Gyara masomin]

Jihar Borno nada kananan hukumomi guda 27. Sune:[3]

 1. Abadam
 2. Askira/Uba
 3. Baga
 4. Bama
 5. Bayo
 6. Biu
 7. Chibok
 8. Damboa
 9. Dikwa
 10. Gubio
 11. Guzamala
 12. Gwoza
 13. Hawul
 14. Jere
 15. Kaga
 16. Kala/Balge
 17. Kwaya kusar
 18. Konduga
 19. Kukawa
 20. Mafa
 21. Magumeri
 22. Maiduguri
 23. Marte
 24. Mobbar
 25. Monguno
 26. Nganzai
 27. Shani

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

 1. https://www.britannica.com/place/Bornu-historical-kingdom-and-emirate-Nigeria
 2. https://www.hurstpublishers.com/book/history-borno/
 3. Nigeria (2000). Nigeria: a people united, a future assured. 2, State Surveys (Millennium ed.). Abuja, Nigeria: Federal Ministry of Information. p. 106. ISBN 9780104089. 


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara